Monday, December 15
Shadow
Matasan Inyamurai sun baiwa Fulani Makiyaya awanni 48 su fice musu daga jihar Enugu

Matasan Inyamurai sun baiwa Fulani Makiyaya awanni 48 su fice musu daga jihar Enugu

Duk Labarai
Wata Kungiyar matasan Inyamurai me suna COSEYL ta baiwa Fulani makiyaya awanni 48 su fice daga jihar Enugu. A sanarwar da kungiyar ta fitar ta bakin shugabanta, Goodluck Ibem ta zargi makiyayan da yiwa mata fyade da kisa a wasu yankunan jihar. Ya bayyana cewa ayyukan na Fulani makiyayan shedanci ne da mugunta inda yace suna Allah wadai da hakan. Yace fulanin 'yan ta'adda ne ba makiyaya ba yayi zargin cewa sunawa matansu fyade kuma su rika saka musu sanda a al'aurarsu. Ya kara da cewa sun yi iya hakurin da zasu iyayi amma an kaisu bango.
Kotu taki amincewa da hana masu rike da mukaman siyasa  zuwa kasashen waje neman magani

Kotu taki amincewa da hana masu rike da mukaman siyasa zuwa kasashen waje neman magani

Duk Labarai
Kotun daukaka kara dake Abuja ta yi dokar cewa bai kamata a hana masu rike da mukaman siyasa zuwa kasashen waje neman lafiya ba. Kotun da Alkalai 3 suka jagoranci yin shari'ar sunce hana 'yan siyasar zuwa kasar waje neman magani kamar take hakkinsu ne a matsayin 'yan Adam. Babban lauya me rajin kare hakkin bil'adama, Femi Falana ne ya shigar da wannan kara akan Gwamnatin tarayya.
Tonon Silili, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya haura shekaru 90 ba 88 kamar yanda yake ikirari>>Inji Tsohon Gwamnan Ogun, Amosun

Tonon Silili, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya haura shekaru 90 ba 88 kamar yanda yake ikirari>>Inji Tsohon Gwamnan Ogun, Amosun

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya bayyana cewa, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fi shekaru 88 kamar yanda yake ikirari. Yace shekarun tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo sun kai tsakanin 93 ko 94. Ya bayyana hakane yayin da ake bikin cikar tsohon shugaban kasar shekaru 88. Saidai tsohon shugaban kasar yace ba gaskiya bane, shekarunsa 88 kamar yanda suke a hukumance.
Ƴànbìndìgà sun kashe ƴan sa-kai biyu a jihar Jigawa

Ƴànbìndìgà sun kashe ƴan sa-kai biyu a jihar Jigawa

Duk Labarai
Ƴanbindiga sun kashe mutum uku, ciki har da jami'an tsaron Najeriya biyu a wani da suka kai a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar. Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Jigawa ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ƴan bindigar sun kai harin ne a ƙaramar hukumar Ringim a jiya Laraba da marece. Hukumar ta ce ƴan bindigar sun buɗe wa wasu jami’an sa-kai masu yaƙi da masu garkuwa da mutane wuta a ofishinsu.
IMF ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta ɓullo da hanyoyin rage raɗaɗin talauci

IMF ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta ɓullo da hanyoyin rage raɗaɗin talauci

Duk Labarai
Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, ya roƙi gwamnatin Najeriya da ta fito da wasu hanyoyin samar wa al’umma yadda za su rage tasirin raɗaɗin da suke ji sakamakon matakan da ta ɗauka domin inganta tattalin arzki. A cewar IMF duk da matakin da gwamnatin ta ɗauka na cire tallafin man fetur ya zama wajibi, amma kuma ya haifar da wahalhalun rayuwa ga ƴan Najeriya da dama. Bankin lamunin ya ce a yanzu tsananin talauci a ƙasar ya ƙaru ya zuwa kashi 47 a cikin shekarar 2024 da ta gabata.
Sanata Natasha Akpoti taki mikewa tsaye kamar kowane sanata bayan da Sanata Godswill Akpabio ya shiga majalisar

Sanata Natasha Akpoti taki mikewa tsaye kamar kowane sanata bayan da Sanata Godswill Akpabio ya shiga majalisar

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti ta ki mikewa tsaye kamar kowane 'yar majalisa bayan da kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio da take zargin ya nemi yin lalata da ita ya shiga majalisar. A daidai wannan lokacin, bulaliyar majalisar, Sanata Mohammed Monguno ya gargadi sanata Natasha Akpoti da cewa dokar majalisar ce idan kakakin majalisar na shiga kowa sai ya mike. Ya jawo hankalinta da cewa ya kamata ta rika mutunta dokar majalisar ba tare da la'akari da wani abuba.
Najeriya ta ƙara yawan man da take haƙowa – Rahoto

Najeriya ta ƙara yawan man da take haƙowa – Rahoto

Duk Labarai
Najeriya ta ƙara yawan man fetur da take haƙowa zuwa ganga 70,000 a kowace rana fiye da adadin da ƙungiyar OPEC ta sanya mata, kamar yadda nazarin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna. A cewar nazarin, man da ƙasashe mambobin ƙungiyar OPEC - ta masu arzikin man fetur - su ka fitar a watan Fabrairu ya ƙaru, inda Iran ke kan gaba, duk da ƙoƙarin da Amurka ke yi na daƙile fitar da man. Najeriya ta ƙara adadin man da take fitarwa da ya zarce adadin da ƙungiyar ta ware mata. Ƙungiyar ta OPEC ta haƙo gangan miliyan 26 da 74,000 a kowace rana a watan da ya gabata, inda aka samu ƙarin ganga 170,000 a kullum idan aka kwantanta da watan Janairu, a cewar nazarin na Reuters. Ƙungiyar OPEC+ - wadda ta haɗa da ƙasashen OPEC da Rasha da sauran ƙawaye - na son rage yawan man da suke h...
Da Duminsa: An dakatar da sanata Natasha Akpoti daga ayyukan majalisa na tsawon watanni 6, an dakatar da Albashinta an kuma janye jami’an tsaron dake bata kariya saboda karya dokar majalisa

Da Duminsa: An dakatar da sanata Natasha Akpoti daga ayyukan majalisa na tsawon watanni 6, an dakatar da Albashinta an kuma janye jami’an tsaron dake bata kariya saboda karya dokar majalisa

Duk Labarai
A zaman majalisar tarayya na yau, Alhamis, majalisar ta dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6. Tun farko dai shugaban kwamitin ladaftarwa na majalisar, Sanata Neda Imasuen ne ya bayar da shawarar dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6 sannan a dakatar da albashinta da kuma janye jami'an tsaron dake bata kariya. Yace ya kamata a dauki wannan mataki ne saboda sanata Sanata Natasha Akpoti ta karya dokokin majalisar sannan an gayyaceta zuwa gaban kwamitin ladaftarwa saidai ta ki amsa gayyatar. A karshe dai majalisar ta amince da dakatar da sanata Sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6 sannan kuma jami'an tsaro sun tasa keyarta zuwa waje. Saidai kamin ta fita tace wannan rashin adalcin ba zai dore ba. kalli Bidiyon anan
Har Majalisa Sanata Natasha Akpoti ta zo mana da Mijinta suka sumbaci juna, su rasa inda zasu je su yi hakan sai a gaban mu, Tana zargin Sanata Godswill Akpabio da nemanta ne kawai dan daukar hankalin mutane>>Inji Majalisar Dattijai

Har Majalisa Sanata Natasha Akpoti ta zo mana da Mijinta suka sumbaci juna, su rasa inda zasu je su yi hakan sai a gaban mu, Tana zargin Sanata Godswill Akpabio da nemanta ne kawai dan daukar hankalin mutane>>Inji Majalisar Dattijai

Duk Labarai
Majalisar dattijai ta bayyana cewa, Sanata Natasha Akpoti ta zargi kakakin majalisar da neman yin lalata da itane kawai dan ta dauki hankulan nmutane. Kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ne ya bayyana haka a hirar da kafar ChannelsTV ta yi dashi. Yace har kofar majalisa Sanata Natasha Akpoti ta je ta yi kiss ita da mijinta. Yace ba yace hakan ya sabawa doka bane amma ai ana barin halas dan kunya dan kuwa hakan ya sabawa al'ada da dabi'ar mutanen kasarnan. _Yace Sanata Natasha Akpoti ta yi zargin Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata ne kawai dan ta dauki hankalin mutane.