Monday, December 15
Shadow
Ban santa ba, Har Gaban Allah tazo ta yi karya, Fasto ya nesanta kansa da matar data ce addu’arsa tasa ta yi kudi amma daga baya aka ganta tana saida lemu

Ban santa ba, Har Gaban Allah tazo ta yi karya, Fasto ya nesanta kansa da matar data ce addu’arsa tasa ta yi kudi amma daga baya aka ganta tana saida lemu

Duk Labarai
A jiyane dai muka ga wata mata data fito take ikirarin fasto Ebuka Obi na cocin Zion Prayer Movement Outreach ya mata addu'a inda daga Dubu dari uku da take dashi har ta sayi gidan Naira Miliyan 500. Saidai daga baya an ga matar na sayar da lemu wanda lamarin ya baiwa mutane mamaki akai ta yada hotunan ta i da aka rika zargin faston da hada baki da ita dan ya nuna addu'ar sa na aiki. Saidai da yake martani game da lamarin, Fasto Ebuka Obi yace bai san matar ba kuma babu wani a cocinsa da ya santa inda yace har gaban Allah ta zo ta yi karya. Yace dama a baya ya fada cewa, sunansa zai ta yawo a kafafen yada labarai nan ba da dadewa ba akan labarin karya.
An kubutar da daya daga cikin daliban da aka yi gàrkùwà dasu a jami’ar FUDMA jihar Katsina

An kubutar da daya daga cikin daliban da aka yi gàrkùwà dasu a jami’ar FUDMA jihar Katsina

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, jami'an tsaro sun kubutar da daya daga cikin dalibai 4 da aka yi garkuwa dasu daga jami'ar FUDMA dake Dutsimma jihar Katsina. Hakanan rahoton yace ana kan kokarin kubutar da sauran dalibai 3 din da suka rage a hannun masu garkuwa da mutanen. Dalibin da aka kubutar shine Fahad Muhammad me shekaru 20 dake tsangayar kimiyyar Kwamfuta aji daya. Kuma an kubutar dashine ranar lahadi bayan bin sahun 'yan Bindigar. Sauran daliban da suka rage sune Adewale Bolaji Ajayi, 23, Emmanuel Michael, 24, da Favour Michael, 22. Dukansu daliban suna ajinsu na farko ne a jami'ar.
Kalli bidiyo inda Shiekh Adam Muhammad Dokoro yace Idan akwai wanda ya taba yin Zina ya tashi tsaye a wajen wa’azinsa

Kalli bidiyo inda Shiekh Adam Muhammad Dokoro yace Idan akwai wanda ya taba yin Zina ya tashi tsaye a wajen wa’azinsa

Duk Labarai
Babban malamin Islama, Shiekh Adam Muhammad Dokoro ya nemi idan akwai wanda ya taba yin zina ya mike tsaye. Sai dai babu wanda aka samu ya mike. https://www.tiktok.com/@mhaliru92/video/7477552048578284806?_t=ZM-8uNPYcIktPh&_r=1 Dan haka yace idan mutum yana yi ya daina ya tuba dan idan bai daina ba sai ya mike a gaban Allah. Kalli Bidiyon anan
Ana shirin sasanta Kwankwaso da Ganduje da Shekarau 

Ana shirin sasanta Kwankwaso da Ganduje da Shekarau 

Duk Labarai
Tsohon ɗan takarar kujerar sanatan Kano ta Tsakiya, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun sulhunta tsakanin jagororin siyasar jihar: Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Shekarau. Zaura ya ce haɗin kan manyan jagororin zai taimaka wajen gyara siyasar jihar, tare da samar da cigaba ta yadda jihar za ta yi gogayya da jihar Legas da wasu jihohin da suka ci gaba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Zaura ya ce, "irin adawar siyasa da ake yi a Kano ba ta da amfani. A shirye nake in shige gaba wajen samar da maslaha tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Shekarau. Ya kamata mu fifita ci gaban Kano sama da son ranmu. Da zarar an samu wannan nasarar, Legas da sauran jihohi sai sun yi koyi da Kano wajen siyasa ta hank...
Ƙungiyar dattawan arewa ta buƙaci a yi bincike kan rikicin Natasha da Akpabio

Ƙungiyar dattawan arewa ta buƙaci a yi bincike kan rikicin Natasha da Akpabio

Duk Labarai
Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, wato Arewa Consultative Forum ko kuma ACF a taƙaice ta nuna damuwarta kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi wanda kakakin ƙungiyar, Muhammad-Baba ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce akwai buƙatar a gudanar da bincike mai kyau domin tantance sahihancin zargin, kamar yadda tashar Channels a shafinta na intanet. "A yanzu dai yadda abubuwa suke shi ne zargin nan zai iya ɓata sunan Najeriya a idon duniya," in ji ƙungiyar, wadda ta nuna damuwa kan yadda a cewarta har zuwa yanzu, sanatocin arewa ne kaɗai suka fuskanci takunkumi kamar dakatarwa a majalisar ta 10. "Wannan ya sa ACF ke fargabar ko dai abin ɓoye ne ya fara fitowa fili na...
Mun kusa fara biyan alawus ɗin naira 77,000 – NYSC

Mun kusa fara biyan alawus ɗin naira 77,000 – NYSC

Duk Labarai
Hukumar NYSC ta ce ta kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus ɗin naira 77,000. Hukumar ta bayyana haka ne a matsayin martani kan rashin fara biyan sabon alawus ɗin bayan an sanar da ƙari daga naira 33,000 da ake biya biyo bayan ƙara mafi ƙanƙantar albashi. A watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin fara biyan sabon alawus ɗin, amma har yanzu ba a fara biya ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga masu bautar ƙasar. A watan Janairu, darakta-janar na NYSC, Birgediya-janar Yushau Ahmed ya sanar da cewa daga watan Fabrairu za a fara biyan sabon alawus ɗin, amma kuma ba a biya ba a watan na Fabrairu da ya gabata. Daraktan riƙo na hulɗa da jama'a na hukumar, Caroline Embu, ta ce suna jiran kuɗi ne da umarni kafin fara biyan sa...
Darajar wasu kuɗaɗen kirifto ta tashi bayan sanarwar Donald Trump

Darajar wasu kuɗaɗen kirifto ta tashi bayan sanarwar Donald Trump

Duk Labarai
Darajar wasu kuɗaɗen kirifto sun tashi bayan shugaba Donald Trump ya sanar da cewa za a kafa wani rumbun adana kuɗaɗen kirifto na ƙasar Amurka. Ya ambaci kuɗin kirifto na Bitcoin da Ethereum da XRP, da ADA SOL a cikin wani jawabi da ya yi a kafofin sadarwa, inda ya ƙara da cewa Amurka ce za ta zama babbar cibiyar hada-hadar kirifto ta duniya. Jim kaɗan da yin jawabin ne darajar kuɗaɗen da ya ambata suka tashi, inda Bitcoin da Etherium suka ƙara daraja da kusan kashi 10 kafin suka ja baya, sannan sauran kuɗaɗen ma suka tashi. A baya dai Trump da matarsa Melania sun fitar da kuɗinsu na kirifto na matakin meme.
Hukumar EFCC tace itace ta kai samame Otal a Jihar Naija ba ‘yan Bìndìgà ba

Hukumar EFCC tace itace ta kai samame Otal a Jihar Naija ba ‘yan Bìndìgà ba

Duk Labarai
A jiyane dai muka samu rahoton cewa, 'yan Bindiga cikin shiga irin ta EFCC sun kai samame wani otal dake Chanchanga inda suka sace mutane 10. Saidai a yau, hukumar EFCC ta fito inda ta bayyana cewa, itace ta kai wannan samame ba 'yan Bindiga ba. Hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa, ta samu bayanai akan wasu 'yan damfarar yanar gizo ne dake zaune a otal din inda wakilanta na jihar Kaduna suka kai samame kan otal din me suna WhiteHill Hotel dake Chanchaga a jihar ta Naija. Sanarwar tace an kama mutane 11 daga otal din sannan hukumar tace ta gudanar da aikinta cikin kwarewa da bin doka dan haka bata san daga inda maganar 'yan Bindiga ta samo asali ba. Hakanan kuma sanarwar tace an kwace motoci 2 da wayoyin hannu 13. Sanarwar tace za'a gurfanar da wadanda ake zargin...