Kalli Hotuna: Gagga-gaggan ƴan Bìndìgà 5 da rundunarsu a yankin Jibia sun tuba sun aje makami sun ayyana ba za su kara kai hari ba
Gagga-gaggan ƴan bindiga 5 da rundunarsu a yankin Jibia sun tuba sun aje makami sun ayyana ba za su kara kai hari ba
Sun kuma mika bindigar AK49 har guda biyu don tabbatar da tubansu
An kai ƙarshen zaman tattaunawa tareda da tubabbun yan dindiga a karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina.
A ranar Juma'a 28/2/2025, ne aka kai ƙarshen zaman tattaunawa da yan dindigar da suka shirya karɓar zaman lafiya a karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
Anyi zaman a karkashin jagorancin Chairman na karamar hukumar Jibia da Jibiya Peoples Froum da (NCSOSACK) da rundunar sojin Nigeriya ta jihar Katsina, daga cikin tubabbun yan dindigar da a kayi zaman tattaunawar dasu akwai.1- Audu Lanƙai2- Kantoma3- Ori4- Tukur Dan Najeriya5- Bammi.
A yayin zaman an tattauna batutuwa da da dama da kuma shimf...








