Monday, April 6
Shadow
Yaro ya dauki Bìndìgàr mahaifinsu inda ya harbe kanwarsa ta mùtù

Yaro ya dauki Bìndìgàr mahaifinsu inda ya harbe kanwarsa ta mùtù

Duk Labarai
Karamin yaro dan shekaru 16 ya dauki Bindigar mahaifinsa ya harbe kanwarsa ta mutu har lahira a jihar Delta. Kakakin 'yansandan jihar, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace lamarin akwai sosa Zuciya. Ya kara da cewa, mahaifin yace shi mafarauci ne kuma dan nasa yakan rika wasa da Bindigar. Yace zuwa ya zu ba'a kai ga tantance sunayen wadanda lamarin ya faru dasu ba.
Ban ga wani abu da zai iya hana Tinubu zarcewa ba a 2027>>Tanko Yakasai

Ban ga wani abu da zai iya hana Tinubu zarcewa ba a 2027>>Tanko Yakasai

Duk Labarai
Dattijon Jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa a yanzu babu dan siyasar dake da karbuwa kamar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda yace Tinubu bai yi wa Arewa Laifin komai ba. Yace APC ce ke rike da mafi yawan jihohi kuna ko jihohin da jam'iyyar Adawa ke rike dasu duk sun nuna goyon bayan Tinubu dan haka bai ga me kada shi ba. Yace amma watakila abubuwa na iya canjawa inda yace amma maganar gaskiya a yanda ake tafiya bai ga wani abu da zai hana Tinubu zarcewa a shekarar 2027 ba.
An kama dattijo mai shekara 80 da miyagun ƙwàyòyì a Kaduna

An kama dattijo mai shekara 80 da miyagun ƙwàyòyì a Kaduna

Duk Labarai
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami'anta sun kama wani dattijo mai suna Ayuba Ashiru mai shekara 80 da kilo 2.3 na miyagun ƙwayoyi. A wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa Femi Babafemi ya fitar wadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 14 ga Mayun 2025 a yankin Dogarawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna ne bayan samun bayanan sirri a game da harƙallarsa. Sanarwar ta ce an taɓa kama Ashirun bisa fataucin miyagun ƙwayoyi, aka ɗaure na shekara goma tsakanin 2014 zuwa 2024. "Ya ce ya kasance a harƙallar fataucin miyagun ƙwayoyi na tsawon shekara 46," kamar yadda sanarwar ta nuna. Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jami'an hukumar sun kama wata dattijuwa mai suna Uloma Uchechi Su...
Da Duminsa: Jami’an tsaro sun kama Rikakken Dan Bìndìgà da ake nema ruwa a jallo cikin maniyyata yana shirin zuwa aikin Hanjji

Da Duminsa: Jami’an tsaro sun kama Rikakken Dan Bìndìgà da ake nema ruwa a jallo cikin maniyyata yana shirin zuwa aikin Hanjji

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana cewa, jami'an tsaro sun kama rikakken dan Bindiga da ake nema ruwa a Jallo cikin maniyyatan da ake tantance wa. Sunan wanda aka kama din shine Yahaya Zango wanda jami'an tsaro sun jima da saka sunansa cikin wadanda ake nema ruwa a jallo. Ya je wajan tantance Alhazai inda ya bayar da fasfo dinsa nan kuwa jami'an DSS suka yi ram dashi aka wuce ofis dashi, kamar yanda Jaridar daily Trust ta ruwaito.
An min tayin Naira Miliyan 21 da takardar zama dan kasar Rasha, da fili dan in je in yiwa kasar yaki amma na kiya>>Sojan Najeriya

An min tayin Naira Miliyan 21 da takardar zama dan kasar Rasha, da fili dan in je in yiwa kasar yaki amma na kiya>>Sojan Najeriya

Duk Labarai
Wani tsohon sojan Najeriya wanda ya ajiye aikin da karfinsa me suna Abubakar Afan ya bayyana cewa an masa tayin zuwa kasar Rasha dan ya tayasu yaki da Ukraine a bashi Naira Miliyan 21 amma yaki. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a kafar Punchng inda yace dalilinsa na kin zuwa shine yasan addinin musulunci ya hana yin yaki saboda kudi, yace idan ya mutu bai san matsayinsa a wajan Allah ba. Yace sannan akwai abokansa da sukewa Ukraine yaki bai san yanda zai yi ba idan ya je shi kuma yanawa Rasha yaki, shin zai je ya kashe abokan nasa ne? Yace rayuwarsa ta fi kudin muhimmanci inda yace matarsa ma tace masa bata yadda yaje ba tunda dai basu rasa komai ba. Yace a yanzu haka ya samu wani aiki ne a kasar Egypt inda yake can yayin da ya bar matarsa a gida Najeriya.
Sabon Fafaroma, Pope Leo ya jawo cece-kuce bayan da yace ba ruwansa da masu auren jinsi

Sabon Fafaroma, Pope Leo ya jawo cece-kuce bayan da yace ba ruwansa da masu auren jinsi

Duk Labarai
Sabon Paparoma Pope Leo XIV ya bayyana cewa, aure tsakanin mace da namiji ne suka gani a Baibul. Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke yaba masa, wasu kuma na sukarsa. Fafaroma da ya mutu, Pope Francis yayi suna sosai wajan nemawa 'yan Madigo da Luwadi da masu auren jinsi 'yanci. Wannan magana da sabon fafaroman yayi ana ganin ya zo da sabon canji.
Arewa maso yamma ta Tinubu ce a 2027>>Inji APC

Arewa maso yamma ta Tinubu ce a 2027>>Inji APC

Duk Labarai
APC a shiyyar Arewa-maso-yamma ta sanar da goyon bayan ta ga Tinubu a zaɓen 2027. Jam'iyyar APC a shiyyar Arewa-maso-yamma ta kada kuri'ar amincewa da shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takara gabanin zaben shugaban kasa na 2027. An bayar da amincewar ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kaduna a jiya Asabar, inda kuma aka amince da Tinubu a matsayin dan takarar daya tilo. A cikin sanarwar da Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna ya karanta, shiyyar ta jaddada biyayyar ta ga jam’iyyar APC tare da yin alkawarin “cikakken goyon baya ga manufar shugaba Tinubu na samar da wadata, daidaito da kuma sauyi mai dorewa ga daukacin ‘yan Najeriya”. “Muna godewa kuma muna yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa kyakkyawan jagoranci da ya ke yi, da sauye-sauyen da ya yi,...
Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Duk Labarai
Tinubu ya dawo da zaman lafiya a Arewa-maso-Yamma, inji Uba Sani. Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya daidaita harkar tsaro a yankin Arewa maso Yamma tare da farfado da harkokin noma da 'yan ta'adda suka durkusar da su a baya. Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar, Sani ya ce yankin da a da ke zama cibiyar ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga, yanzu yana samun sauyi mai ma’ana. “Tun kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, yankin Arewa maso Yamma ne cibiyar ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan tashin hankali,” in ji shi. “Ba za ka iya yin tafiya daga wuri zuwa wani wuri ba. Manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba. Rayuwa ta kasance...