Sunday, May 3
Shadow
Ƴansandan sun hana hawan sallah a Kano

Ƴansandan sun hana hawan sallah a Kano

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan jihar Kano tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro a jihar sun ɗauki matakin haramta bukukuwan hawan salla a Kano. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya ce hukumomin tsaron sun ɗauki matakin ne sakamakon dalilai na tsaro. Matakin na zuwa ne bayan da wata takarda da aka yi amanna daga fadar Sarki Muhammadu Sanusi II ta fito, ta yi kira da hakimai da su shiga birnin Kano domin gudanar da bukukuwan hawan Sallah. Ko a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah ma hukumomin tsaron jihar sun haramta hawan sallah, saboda bayanan sirrin da suka ce sun samu na wasu ''ɓata-gari'' da ke son amfani da bukukuwan hawan sallar wajen tayar da zauen tsaye a jihar. ''Kan haka ne hukumomin tsaron suka sake ɗaukar matakan haramta...
Gwamna Abba Kabir Ya Bada Gudummuwar Naira Miliyan Biyar Ga Farfesan Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Da Ake Nema Wa Taimako Rashin Lafiya

Gwamna Abba Kabir Ya Bada Gudummuwar Naira Miliyan Biyar Ga Farfesan Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Da Ake Nema Wa Taimako Rashin Lafiya

Duk Labarai
Gwamna Abba Kabir Ya Bada Gudummuwar Naira Miliyan Biyar Ga Farfesan Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Da Ake Nema Wa Taimako Rashin Lafiya Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf Ya Baiwa Farfesa Abubakar Roko Na Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Dake Sokoto Gudummuwar Naira Miliyan Biyar Dake Fama Da Jinya, Domin Zuwa Neman Lafiya A Kasashen Waje. Allah Ya Ba Shi Lafiya Ya Kuma Saka Wa Gwamna Abba Kabir Yusuf Da Alheri! Daga Jamilu Dabawa
Ya kamata Najeriya ta gina katanga a kan iyakokinta>>Inji Shugaban Sojojin Najeriya, Christopher Musa

Ya kamata Najeriya ta gina katanga a kan iyakokinta>>Inji Shugaban Sojojin Najeriya, Christopher Musa

Duk Labarai
Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya nuna buƙatar gina katanga a ilahirin iyakokin ƙasar da maƙwaftanta domin kare kwararar masu ɗauke da makami zuwa cikinta. Yanzu haka dakarun sojin Najeriya na fafutikar ganin sun yaƙi matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, musamman rikicin Boko Haram da ƙasar ta kwashe shekara 16 tana fama da shi a arewa maso gabas. Mayaƙan ƙungiyar - wadda ta samo asali daga kungiyar IS reshen yammacin Afirka - sun kashe jami'an tsaro da dubban fararen hula, yayin da rikicin ya tagayyara miliyoyi. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Janar Christopher Musa a wani taron tsaro da ke gudana a Abuja yau Talata a Abuja na cewa "kula da kan iyakoki abu ne mai muhimmanci," inda ya bayar da misali da iyakar ƙasar Pakistan mai katangar da ke ...
Da gangan wasu mugayen ‘yan Najeriya ke kara farashin kaya dan kawai su bata min suna>>Gwamnatin Tinubu

Da gangan wasu mugayen ‘yan Najeriya ke kara farashin kaya dan kawai su bata min suna>>Gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa da gangan wasu 'yan Najeriyar ke karawa kayan da suke sayarwa farashi dan kawai su batawa gwamnatinsa suna. Hadimin shugaban kasar me bashi shawara akan tattalin arziki, Tope Fasua ne ya bayyana hakan. Yace banda alkaluma tattalin arziki, akwai sauran abubuwan da ke sanya farashin kayan masarufi su tashi a Najeriya, hadda muguntar wasu 'yan kasar. Ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook yayin da yake martani ga wani rahoto dake cewa wani gidan mai yana biyan ma'aikatansa Naira Dubu 10.
Ba kamar yanda ake cewa mun Kàshè ‘yan sa kai da yawa ba a Zamfara, Guda biyu ne kawai suka mùtù bayan jirgin saman mu yayi kuskuren jefa musu Bàm da tunanin cewa ‘yan Bìndìgà ne>>Hukumar Sojojin Najeriya

Ba kamar yanda ake cewa mun Kàshè ‘yan sa kai da yawa ba a Zamfara, Guda biyu ne kawai suka mùtù bayan jirgin saman mu yayi kuskuren jefa musu Bàm da tunanin cewa ‘yan Bìndìgà ne>>Hukumar Sojojin Najeriya

Duk Labarai
Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai hare-hare ta sama a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar, tana mai cewa dakarun sa-kai biyu sun rasu yayin da take harar 'yanfashin daji. A jiya Litinin ne mazauna ƙaramar hukumar Maru suka shaida wa BBC Hausa cewa jirgin yaƙin sojin ya kashe 'yan sa-kai, yayin da ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mayaƙa 20 aka kashe a lokacin da suke bin sawun 'yanbindigar da suka kai musu hari da sace wasu mutane. Kakakin rundunar Ehimen Ejodame ya ce hare-haren da suka kai bayan samun bayanan sirri sun yi sanadiyyar kashe 'yanbindigar 20. "A martanin da muka mayar cikin gaggawa ranar 31 ga watan Mayu, dakarunmu sun kashe sama da 'yanta'adda 20 tare da lalata babura fiye da 21," a cewarsa yayin wani taron manema labarai&...
Kalli Hotuna: An kàshè sojojin Isra’ila uku a Gàzà

Kalli Hotuna: An kàshè sojojin Isra’ila uku a Gàzà

Duk Labarai
Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da sunayen dakarunta uku da ta ce an kashe a arewacin Zirin Gaza ranar Litinin. Mutanen uku da ke da shekaru 20 da ɗoriya sun fito daga bataliya ɗaya - an ce biyu daga ciki likitoci ne, na ukun kuma kwamanda, a cewar wata sanarwa da rundunar sojin ta IDF ta fitar. Jaridar Times of Israel ta bayar da rahoton cewa an kashe su ne sakamakon wani bam da ya tashi da su lokacin da suke tsaka da fafatawa da mayaƙan ƙungiyar Hamas a yankin Jabalia.
Sanata Kalu ya fasakwai inda ya Bayyana masu daukar nauyin Ayyukan tà’àddàncì a Najeriya

Sanata Kalu ya fasakwai inda ya Bayyana masu daukar nauyin Ayyukan tà’àddàncì a Najeriya

Duk Labarai
Sanata Orji Uzor Kalu dake wakiltar mazabar Abia North a majalisar Dattijai ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa ne da manyan ma'aikatan Gwamnati da 'yan Kasuwa ke daukar nauyin ayyuka Kungiyar Bòkò Hàràm. Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV. Yace kuma masu yin hakan suna yi ne dan kawai su hana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu iya gudanar da Gwamnatinsa yanda ya kamata. Yace amma ba ta haka bane ake karbar mulki, yace yawanci suna yi ne dan su kwace mulki daga hannun Tinubu ba kudi bane a gabansu.
Gwamnatin Tarayya zata biya bashin Naira Tiriliyan 2 na kudin wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya zata biya bashin Naira Tiriliyan 2 na kudin wutar lantarki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta fara amincewa da batun biyan bashin Naira Tiriliyan 2 na wutar lantarki da akw binta. Hakan kokarine na samar da ingantacciyar wutar Lantarki a Najeriya. Na kusa da me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar makamashi, Eriye Onagoruwa ce ta bayyana hakan a wajan wani taron masu ruwa da tsaki na harkar wutar da aka gudanar. Tace gwanatin na duba muhimmancin hakan wajan samar da wutr Lantarki me karfi. Inda tace gwamnatin na kokarin ganin ta samar da wata hanya ta bashi dan biyan wannan bashi musaman lura da karancin kudin da gwamnatin ke fama dashi.
Kalli Bidiyon: Mutum daya ya rasu, 69 sun jikkata yayin girgizar kasa a Turkiyya

Kalli Bidiyon: Mutum daya ya rasu, 69 sun jikkata yayin girgizar kasa a Turkiyya

Duk Labarai
Girgizar kasa ta faru a kasar Turkiyya inda mutane 69 suka jikkata. Yawanci wadanda suka jikkatar sun diro ne daga benaye saboda fargabar kada gidan da suke ciki ya rushene. Saidai mutum daya ya mutu. Karfin girgizar kasar ya kai maki 6.2 kamar yanda masana suka sanar. https://twitter.com/geotechwar/status/1929690994091741373?t=qa7qPmG2xXaNo2yyCcmrog&s=19 Kasar Turkiyya dai na daga cikin kasashe masu yawan fuskantar Ambaliyar ruwa.