Saturday, December 6
Shadow
Kalli Bidiyon, Yanda hankula suka tashi bayan sojoji sun hana Wike Shiga wani Fili a Abuja

Kalli Bidiyon, Yanda hankula suka tashi bayan sojoji sun hana Wike Shiga wani Fili a Abuja

Duk Labarai
Hankula sun tashi akaita musayar yawu bayan da sojoji suka hana Ministan Abuja, Nyesom Wike shiga wani fili da ake rikici akansa. Sojojin sunce shugabansu, Shugaban Sojojin Ruwa watau Vice Admiral Zubairu Gambo ne ya basu umarni. Saidai Shugaban tsaro na kasa ya shiga lamarin aka sasanta kamin abun ya kazance. https://twitter.com/emmaikumeh/status/1988232078660350319?t=aMVL1A0a5ASt688z4sH_Jg&s=19
Kalli Sabon Bidiyon Dan majalisa Alhassan Ado Doguwa a Landan yana Kwambo daya dauki hankula inda a wannan karin aka ganshi yana cin abinci a bandaki

Kalli Sabon Bidiyon Dan majalisa Alhassan Ado Doguwa a Landan yana Kwambo daya dauki hankula inda a wannan karin aka ganshi yana cin abinci a bandaki

Duk Labarai
A dasu da safene aka ga Bidiyon Alhassan Ado Doguwa yana kwambo a kan titin Birnin Landan na kasar Ingila. Lamarin ya jawo cece-kuce inda mutane sukai ta mamakin dan majalisar Tarayya guda da nuna irin wannan halayya. Saidai ashe kallo be kare ba, a karo na biyu an ga Doguwa yana daukar hoton a cikin dakin Otal dib da ya sauka inda a wannan karin har abinci yaci a cikin bandaki. https://twitter.com/Asad_Mukty/status/1988160598086164882?t=k_sh_5vZZm33_Yz-mo4w3Q&s=19
Mutuncin Najeriya ya zube a Idon Duniya, A lokacin ina shugaban kasa, Amurka basa yin komai a Afrika ba tare da sun sanar da Najeriya ba>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Mutuncin Najeriya ya zube a Idon Duniya, A lokacin ina shugaban kasa, Amurka basa yin komai a Afrika ba tare da sun sanar da Najeriya ba>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwa kan yanda Darajar Najeriya ta zube a Idon Duniya inda yace a lokacin mulkin sa da Marigayi Janar Murtala, Kasar Amurka basa daukar wani mataki a Afrika ba tare da Sanar da Najeriya ba. Ya bayyana hakane a Abeokuta ranar Litinin yayin ganawa da wasu matasa. Obasanjo yace shi da Murtala sun dawo da Martabar Najeriya . Yace a lokacin da aka baiwa Najeriya 'yancin kai Turawa na ganin itace giwar Africa kuma suna girmama ta amma daga baya wannan girman ya dusashe. Obasanjo yayi kira ga matasa da su tashi tsaye su karbe mulki daga hannun tsaffin dake mulkar Najeriya a yanzu yace amma idan suka bari abubuwa suka ci gaba da faruwa a haka, babu inda kasar zata.
A rika yin aure yanda Addini ya tanada: Tsarabe-Tsaraben da ake kawowa ne yasa aure be dadewa yake mutuwa>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma’u Wakili

A rika yin aure yanda Addini ya tanada: Tsarabe-Tsaraben da ake kawowa ne yasa aure be dadewa yake mutuwa>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma’u Wakili

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma'u Wakili ta bayar da shawarar a rika yin aure kamar yanda addinin Musulunci ya tanada inda tace tsarabe-tsaraben da ake yi na wasu shagulgulan da suka sabawa Addini wani bin su ne ke kawo mutuwar aure da wuri. Ta bayar da shawarar ne a shafinta na sada zumunta inda tace tasan zata sha martani. https://www.tiktok.com/@asmee_wakili/video/7571186756314320136?_t=ZS-91J25LB8g9g&_r=1
Har yanzu ina nan inata kokarin ganawa da Trump tun bayan Bharazanar da yawa Najeriya>>Shugaba Tinubu

Har yanzu ina nan inata kokarin ganawa da Trump tun bayan Bharazanar da yawa Najeriya>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa har yanzu yana kokarin ganawa da shugaban kasar Amirka, Donald Trump. Ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara kan harkar sadarwa, Watau Daniel Bwala a hirar da aka yi dashi a Arise TV. Daniel Bwala yace kwanannan Shugaba Tinubu da Donald Trump zasu gana dan karfafa dangantakar Najeriya da kasar ta Amurka. Ya bayyana cewa ba zai bayyana irin shirin da suke ba amma mutane au fahimci cewa har yanzu suna kokarin ganin an bi hanyar data dace dan ganawa tsakanin shuwagabannin biyu.
Ganin Sheikh Dr. Ahmad Gumi a kasar Turkiyya ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ya tsere ne saboda kharin da Amirka tace zhata Kawo Najeriya

Ganin Sheikh Dr. Ahmad Gumi a kasar Turkiyya ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ya tsere ne saboda kharin da Amirka tace zhata Kawo Najeriya

Duk Labarai
An ga babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi a kasar Turkiyya inda har wakilin kafar yada labarai ta TRTHausa, Bahause ya bayyana cewa sun yi hira da malamin. Saidai da yawa, Musamman ma 'yan kudancin Najeriya na cewa ya tsere ne saboda fargabar harin da kasar Amirka tace zata kawo Najeriya. Saidai babu wasu bayanai dake tabbatar da wannan zargi inda Bahaushe ya mayarwa wani martani bayan ya tambayi yaushe Sheikh Dr. Ahmad Gumi zai dawo Najeriya da cewa, Kwanannan. Yace masa shine ma zai jagorancin Sallar Juma'a me zuwa in Allah ya yarda. https://twitter.com/Bahaushee/status/1987967521253626059?t=GK9SG43O7xARHUmO0-_aoA&s=19
Kalli Bidiyo: Wani Wakilin Kiristoci na zagayawa yanawa shugaba Tinubu Yakin Neman zabe inda yace ko da wa Tinubu zai sake tsayawa takara a 2027 shi zasu zaba saboda abinda ya musu ko Shuwagabannin kasa Kiristoci da suka yi shugabanci a Najeriya basu musu ba

Wani wakilin Kiristoci ya dauki hankula sosai a kafafen sadarwa bayan da aka ganshi yana fadar cewa abinda Tinubu ya musu babu wani shugaba da ya taba musu. Ya na zagayawa ne yana hado kan kiristoci musamman na Arewa ta tsakiya, inda yace shugaba Tinubu ya baiwa shugaban jam'iyyar APC kirista, sannan ya baiwa shugaban hukumar zabe me zaman kanta, INEC kirista wanda yace idan da shugaba Kirista ne ba zai yi hakan ba. https://twitter.com/jrnaib2/status/1987797704064577737?t=GILH8rkJ_GZxOFeSeqpB6g&s=19
Kalli Bidiyon yanda dan majalisar wakilai daga Kano, Alhassan Ado Doguwa ke Kwambo a ziyarar da ya kai Birnin Landan na kasar Ingila

Kalli Bidiyon yanda dan majalisar wakilai daga Kano, Alhassan Ado Doguwa ke Kwambo a ziyarar da ya kai Birnin Landan na kasar Ingila

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai ta tarayya, Alhassan Ado Doguwa daga jihar Kano ya dauki hankula bayan da aka ga wani Bidiyonsa yanata Kwambo a birnin Landan na kasar Ingila. An ga Doguwa yana zagayawa a jikin wani gini me kama da ital inda ake daukarsa Bidiyo. Wasu dai sun rika tambayar cewa, wannan ne karin farko daya je kasar Ingilar? https://twitter.com/Asad_Mukty/status/1987981456916795501?t=r5cfaNLKB90DFxf5cww9GQ&s=19
Gwamnatin tarayya na rokon kasar Ingila ta bada dama a dawo da Sanata Ike Ekweremadu ya ci gaba da zaman gidan yarinsa a Najeriya

Gwamnatin tarayya na rokon kasar Ingila ta bada dama a dawo da Sanata Ike Ekweremadu ya ci gaba da zaman gidan yarinsa a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta fara rokon gwamnatin ingila ta taimaka a dawo da sanata Ike Ekweremadu Najeriya ya ci gaba da zaman gidan yarinsa anan. A jiyane Hutudole ya kawo muku cewa, Shugaba Tinubu ya aike da wata tawaga ta musamman zuwa kasar Ingima dan kaiwa Sanata Ike Ekweremadu ziyara a gidan yarin da yake daure acan. Saidai Sabbin Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa, Gwamnati ta aika wakilanne zuwa Ingila dan su roki hukumomin kasar su bayar da dama a dawo da Sanata Ekweremadu zuwa Najeriya ya ci gaba da zaman gidan yarinsa anan. Rahoton yace Wakilan Gwamnatin Najeriyar na kuma rokon a sassautawa Sanata Ekweremadu hukunci ko kuma a rage yawan shekarun da aka yanka masa na zama a gidan yarin. An yankewa Sanata Ike Ekweremadu hukuncin daurin sh...