Saturday, December 13
Shadow
YANZU-YANZU :Hussaina matar Seaman Abbas ta ce yanzu basa tare da mijinta Seaman Abbas

YANZU-YANZU :Hussaina matar Seaman Abbas ta ce yanzu basa tare da mijinta Seaman Abbas

Duk Labarai
Ba sakinta ya yi ba amma wulakanci da hantara da cin mutuncin da take zargin yake mata shi da danginsa da yan garinsu abun yayi yawa, kuma duk suna yi mata cin mutuncin ne saboda zargin an bata gudunmawar Naira milyan N20 daga Berekete Family. Tace kuma ba gaskiya bane ba a bata ko sisi ba. Yanzu dai haka bayan sun fatattako ta daga gidan mijin tana cen tana fama da rashin lafiya har ma ta roki a taya ta da addu'a… Abun lura shine Seaman Abbas ya ji sauki, yana cikin hayyacinsa, ya dawo lafiyarsa lau
Kungiyoyin kare hakkin masu amfani da wayoyin hannu sun maka Gwamnati a kotu saboda karin kudin kiran waya da kaso 50

Kungiyoyin kare hakkin masu amfani da wayoyin hannu sun maka Gwamnati a kotu saboda karin kudin kiran waya da kaso 50

Duk Labarai
Kungiyoyin dake fafutuka dan kare hakkin masu amfani da wayar hannu aun mikawa hukumar kula da sadarwa ta kasa NCC korafin rashin amincewarsu kan karin kudin kiran waya da kaso 50 cikin 100. Sun mika korafinne nan ranar Juma'ar data gabata inda suka bukaci a basu amsa nan da ranar Talata ko su shiga kotu. Kamfanonin sadarwa sun nemi a basu damar kara kudin kiran waya da kaso 100 bisa dari watau su nunka amma NCC ta basu damar kara kaso 50 cikin 100. Wannan kari dai shine irinsa na farko a cikin kusan shekaru 10 da suka gabata. Kungiyar NATCOMS na daga cikin kungiyoyin da suka shigar da wannan korafi, kuma shugabanta, Adeolu Ogunbanjo, ya shaidawa jaridar Punchng cewa, tunda har ranar Talata basu ji amsa ba daga NCC, to basu da zabin da ya wuce su shiga kotu. Jaridar ta yi ko...
Ba zan bar Jam’iyyar APC ba>>El-Rufai

Ba zan bar Jam’iyyar APC ba>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ba zai bar Jam'iyyar APC ba. El-Rufai ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da 'yan Jarida ranar Talata a Abuja wajan taron karfafa Dimokradiyya a Najeriya. Yace ba zai bar Jam'iyyar APC ba. An tambayeshi to me yasa yake sukar Jam'iyyar APC din sai yace ai yana so su gyara ne kuma yana tsammanin zasu gyara din. Daga nan ya wuce abinsa.
El-Rufai na son kifar da Gwamnatin mu>>Inji Gwamnatin Tarayya

El-Rufai na son kifar da Gwamnatin mu>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamnatin tarayya ta yi martani akan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda tace a baya yana tare da ita amma yanzu yana son kifar da gwamnatin. Hakan na zuwane bayan da Tsohon Gwamnan yayi tsokaci akan gwamnatin Tinubu inda yace Jam'iyyar APC ta kaucewa tubalin da aka dasata akai na shugabanci me kyau. Me baiwa shugaban kasa shawara na musamman akan sadarwa, Daniel Bwala ya mayar da martanin ta shafinsa na kafar X inda yace da El-Rufai na cikin gwamnatin ...
Jahilaine ke shugabantar Najeriya a yanzu>>Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Jahilaine ke shugabantar Najeriya a yanzu>>Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, Jahilaine ke mulkar Najeriya a yanzu inda yace yawanci wanda basu da isashshen limi ko Wanda basu dashine suke gaba-gaba a Gwamnati. El-Rufai ya bayyana hakane a wajan wani taron karfafa Dimokradiyya da ya faru a babban barnin tarayya, Abuja. El-Rufai ya zargi Jam'iyyar APC da yin halin ko in kula game da yin shugabanci na gari. El-Rufai yace shi bai ganewa kan Jam'iyyar APC ba dan kuwa komai nata ya lalace ba taron Jam'iyyar babu wata harka ta ci gaba.
Najeriya ta lalace, sai an sha wuya kamin ta dawo daidai>>Kashim Shettima

Najeriya ta lalace, sai an sha wuya kamin ta dawo daidai>>Kashim Shettima

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Najeriya ta samu matsalar rashin kula a baya dan haka gyaranta sai an sha wuya. Ya bayyana hakane ta bakin wakilinsa, Hakim Baba Ahmad a yayin da ya wakilceshi zuwa taron karfafa Dimokradiyya a Abuja jiya. Ya kara da cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana sane da irin halin matsin rayuwa da al'ummar Najeriya ke ciki kuma zai dauki matakin gyara a inda ya kamata. Ya kara da cewa, Gwamnatinsu da Bola Ahmad Tinubu ke jagoranta zata ci gaba da yaki da rashawa da cin hanci da tada komadar tattalin arziki da ci gaba da goyon bayan zaben gaskiya.
Hukumar Federal Civil Service Commission ta sanar da daukar sabbin ma’aikata

Hukumar Federal Civil Service Commission ta sanar da daukar sabbin ma’aikata

Duk Labarai
Hukumar Gwamnatin tarayya ta Federal Civil Service Commission ta sanar da daukar sabbin ma'aikata wanda za'a cike guraben ayyuka da yawa. Me magana da yawun hukumar Taiwo Hassan ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin. Hukumar ta bukaci 'yan Najeriya dasu cike bayanansu dan samun gurbin aiki da ake nema. Shafin da za'a bi dan cike bayanai shine: https://recruitment.fedcivilservice.gov.ng Shafin zai kasance a bude har nan da zuwa ranar 10 ga watan Maris. Hakanan hukumar tace masu bukata ta musamman da masu nakasa ma na iya neman wannan aiki.
Na samu karin Lafiya sosai bayan dana sauka daga Mulkin Najeriya>>Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Na samu karin Lafiya sosai bayan dana sauka daga Mulkin Najeriya>>Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya samu karin lafiya sosai bayan da ya sauka daga kan mulkin Najeriya. Shugaban ya bayyana hakane a wajan taron Jam'iyyar APC a jihar Katsina. Yace duk da kokarin da yayi na gyaran kasarnan amma ya fuskanci suka daga mutane da yawa. Yace wadanda basa kusa da Gwamnati basu san yanda ake gudanar da mulki da matsalar mulkin ba. Yace bayan da ya sauka, mutane dake kai masa ziyara sun bayyana cewa, a yanzu yafi lafiya fiye da sanda yake kan mulki. Buhari ya baiwa shuwagabanni shawarar su ji tsoron Allah.
Ni kiristane amma har yanzu ina taba addinin gargajiya da tsafe-tsafe>>Inji tsohon shugaban kasa Obasanjo

Ni kiristane amma har yanzu ina taba addinin gargajiya da tsafe-tsafe>>Inji tsohon shugaban kasa Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, shi kiristane amma har yanzu yana taba addinin gargaji na bautar wani gunki da ake cewa Ifa. Obasanjo yace kamin zuwan addinin kiristanci da Musulunci suna da Ifa kuma duk wnda ya zagi Ifa zai ce shi wawane. Ya bayyana cewa, shi bai wasa da al'ada saboda abincinmu, tufafi da yaren Yarbawa duk suna da muhimmanci a wajansa.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da ‘yan Bìndìgà

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da ‘yan Bìndìgà

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da 'yan Bindiga a jiharsa. Gwamnan ya bayyana hakanne a hirar da BBChausa ta yi dashi. Ya bayyana cewa, yayi sulhu da 'yan Bindigar ne saboda ko da mutum daya aka kashe sai Allah ya tambayeshi. Ya kara da cewa, Basu baiwa 'yan Bindigar ko sisi ba sannan kuma sun saki wadanda suka yi garkuwa dasu. Yace harkar kasuwanci da noma na ci gaba da habaka tun bayan lamarin.