Tuesday, December 16
Shadow
Wanda suka yi Gàrkùwà da janar Tsiga a Katsina sun nemi a biya kudin fansa Naira Miliyan dari biyu da hamsin(250m)

Wanda suka yi Gàrkùwà da janar Tsiga a Katsina sun nemi a biya kudin fansa Naira Miliyan dari biyu da hamsin(250m)

Duk Labarai
' Yan Bindigar da suka yi garkuwa da tsohon janar din soja kuma tsohon shugaban hukumar bautar kasa(NYSC) Janar Maharazu Tsiga rtd sun nemi a biya Naira Miliyan 250M a matsayin kudin fansarsa. Wata majiya dake kusa da iyalan janar dinne suka bayyana hakan inda suka ce masu garkuwa da mutanen sun kira iyalan janar din suka sanar da hakan. An yi garkuwa da janar tsiga ne tare da wasu mutane 9. Lamarin ya faru ranar Laraba da dare inda 'yan Bindiga su kusan 100 suka zagaye gidansa suka tsafi dashi. Dan majalisar tarayya dake wakiltar Bakori da Danja ya tabbatar da faruwar lamarin saidai zuwa yanzu hukumomin soji dana 'yansanda basu bayar da ba'a si ba kan lamarin.
An gurfanar da tsohon Minista kuma tsohon dan takarar shugaban kasa Kabiru Turaki a kotu bisa zargin yin lalata da wata mata har ta kai ga ya dirka mata ciki

An gurfanar da tsohon Minista kuma tsohon dan takarar shugaban kasa Kabiru Turaki a kotu bisa zargin yin lalata da wata mata har ta kai ga ya dirka mata ciki

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, an gurfanar da tsohon Ministan ayyukan na musamman Kabiru Turaki (SAN) a kotun magistre dake Abuja bisa zargin yin lalata da wata mata. Saidai Turaki ya musanta zargin da ake masa bayan da aka karanto masa zarge-zargen a gaban me shari'a, Abubakar Jega. An zargi ministan da cewa a tsakanin watan Disamba na shekarar 2014 zuwa watan August na shekarar 2016 ya kai wata me suna  Ms. Hadiza Musa wani otal me suna Hans Palace inda yayi lalata da ita. Ya kuma sake yin lalata da matar a otal din Ideal Home Holiday dake Asokoro tsakanin watan August 2016 zuwa watan November 2021. Daga baya ma sai ya kama mata gida dake da adireshin at No. 12 Clement Akpagbo Close, Gauzape inda ya ci gaba da lalata da ita da sunan cewa ya aureta. A ...
Maganar canja tsarin karatun Najeriya daga JSS da SSS zuwa shekaru 12 ba gaskiya bane>>Inji Gwamnatin Tarayya

Maganar canja tsarin karatun Najeriya daga JSS da SSS zuwa shekaru 12 ba gaskiya bane>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Ma'aikatar ilimi ta tarayya, ta bayyana cewa, Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya bada shawarar canja tsarin karatun Najeriya daga JSS da SSS zuwa shekaru 12 ne amma bai ce an canja ba. Sanarwar tace maganar canja tsarin kai tsaye ba gaskiya bane. Me magana da yawun ma'aikatar Ilimin, Folasade Boriowo ta bayyana cewa, kwamitin Ilimi na kasa zai duba wannan shawara kamin sanin matakin da ya kamata a dauka na gaba. Ministan ya bayar da wannan shawara ne a Abuja ranar 6 ga watan Fabrairu a wajan wani taro kan Ilimi da aka yi a Abuja.
DA DUMI DUMINSA: fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al’ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu

DA DUMI DUMINSA: fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al’ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu

Duk Labarai
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Sama da mutanen Arewa kimanin Miliyan 60 Suka Nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin ya cigaba da mulki 2027, al'ummar Arewa sama da Miliyan 60 Sun Bayyana Goyan bayan Su ga Tinubu. Fadar shugaban ƙasa tace Sama da Mutanen Arewa Miliyan 60 Sun nuna goyon Bayan Su ga Shugaban Kasa Bola Tinubu, da Wasu da Kungiyoyi ga tuntuba ta matasan Arewa ta wakilta, sun bayyana Goyon bayansu ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Sun jaddada cewa "goyon bayansu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Sanata Akpabio suna mai cewa "shugabannin biyu daga Kudu sun goyi bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban ƙasa da Shugaban majalisar Dattawa, kuma hakan ya dace a gare mu. don rama wannan gudummawar da suka ba...
Ministar da Tinubu ya sauke ta koma yin Fim

Ministar da Tinubu ya sauke ta koma yin Fim

Duk Labarai
Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta dawo masana’antar Nollywood tare da sabon fim dinta mai suna “Hatred”. Fim ɗin, wanda ita ce ta shirya, ya kasance alamar dawowarta a hukumance cikin masana'antar bayan tsawon lokacin da ta yi a harkar siyasa. An naɗa Kennedy-Ohanenye a matsayin ministan Shugaba Bola Tinubu a ranar 21 ga Agusta, 2023, amma aka tsige ta daga mukaminta a ranar 23 ga Oktoba, 2024, tare da wasu ministoci hudu. VANGUARD ta rawaito tun bayan barin ta ofis, matar mai shekaru 51 ta koma mayar da hankali kan harkar shirya fina-finai da fasaha.
Da Duminsa: Kamfanin Wutar Lantarki sun janye yajin aikin da suke a Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi

Da Duminsa: Kamfanin Wutar Lantarki sun janye yajin aikin da suke a Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanin wutar lantarkin dake kula da wutar lantarki ta Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sokoto dake yajin aiki sun janye yajin aikin nasu da ya kwashe kwanaki biyar suna yi. Ma'aikatan kamfanin wutar sun janye yajin aikinne bayan da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya shiga tsakani. Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda ya tabbatar da cewa, an janye yajin aikin.
Komai ya tafi daidai a Gwamnatina>>Tsohon Shugaban kasa Buhari ya bugi kirji

Komai ya tafi daidai a Gwamnatina>>Tsohon Shugaban kasa Buhari ya bugi kirji

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya bayyana cewa a zamanin mulkinsa abubuwa sun tafi yanda ya kamata. Ya bayyana hakane a gawarsa da wasu 'yan jarida da suka kai masa ziyara a Daura. Yace abubuwan ci gaba da ya kawo a zamanin mulkinsa za'a dade ana amfana dasu a Najeriya. Shugaban ya bayyana cewa, a shekarar 2015 da ya karbi mulki, ya gaji matsaloli da yawa daga gwamnatin Jam'iyyar APC wanda suka hada dana rashin tsaro, matsalar tattalin arziki da sauransu.
Amurkawa na zuwa Asibitocin Najeriya neman magani>>Inji Gwammatin Tarayya

Amurkawa na zuwa Asibitocin Najeriya neman magani>>Inji Gwammatin Tarayya

Duk Labarai
Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, an samu ci gaba sosai a Najeriya musamman ta fannin lafiya inda yace 'yan kasar Amurka na zuwa Najeriya neman magani. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da wata kungiyar Likitocin da suka kai masa ziyara a Abuja fadar shugaban kasa. Yace kwanannan wasu marasa lafiya daga kasar Amurka su 13 suka zo Asibitin Zenith Medical and Kidney Centre aka musu dashen koda kuma an samu nasarar yin aikin. Yace kuma sun samu aikin a farashi me sauki kasa da yanda ake yinsa a kasar ta Amurka. Mataimakin shugaban kasar ya kuma jinjinawa shugaban Asibitin me suna Dr. Olalekan Olatise inda yace gwarzo ne wajan kula da lafiya. Saidai ya koka game da yanda 'yan Najeriya da yawa ke fama wajan aikin Koda saboda tsadarsa inda yace wasu na dog...
Yajin aiki akan kara kudin kiran waya ba gudu ba gudu ba ja da baya>>TUC

Yajin aiki akan kara kudin kiran waya ba gudu ba gudu ba ja da baya>>TUC

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta TUC ta jadada cewa, babu gudu ba ja da baya akan maganar yajin aikin da take shirin yi dan nuna rashin jin dadin karin kudin kiran waya dana data. Shugaban kungiyar, Festus Osifo ne ya bayyana haka a ganawar da aka yi dashi a ChannelsTV. Yace abinda ya kawo tsadar kudin gudanarwa na kamfanonin sadarwar, farashin canjin kudin Naira da dala ne wanda kuma gwamnati zata iya yin maganinsu. Yace gwamnati ce ke da alhakin magance matsalar ta kamfanonin sadarwar ba wai su rika fanshewa akan talakawa ba.
Kalli Bidiyo: ‘Yan Uwan me yada badala a Tiktok, Yahya Amerika sun taru sun masa dukan kawo wuka saboda zubar musu da mutunci da yake inda yace ya tuba ba zai kara ba

Kalli Bidiyo: ‘Yan Uwan me yada badala a Tiktok, Yahya Amerika sun taru sun masa dukan kawo wuka saboda zubar musu da mutunci da yake inda yace ya tuba ba zai kara ba

Duk Labarai
ABIN KOYI: 'Yan Uwan Wani Mai Yada Baďàla A Țiķțok me suna Yahya Amerika Sun Taŕu Sùm Yi Mašà Ďuķan Țšiýa Saboda Yadda Yake Źùbaŕwa Da Dañginsu Mùtùnci Bayan ya daku, mutumin ya ce daga yau ya tuba ba zai sake ba, kuma zai goge shafin nasa na țiķtoķ. https://www.tiktok.com/@babyn.babybackup4/video/7468258337616907526?_t=ZM-8ti5YVGGBwk&_r=1 Hutudole ya fahimci cewa, yakan rika bayyanawa a shafinsa cewa duk macen da take son a yi lalata da ita, ta mai magana. Fatan mu shine Allah yasa da gasken ya daina.