Rahotanni sun bayyana cewa, an garzaya da Tauraron fina-finan Indiya, Prem Chopra zuwa Asibiti.
Babu dai cikakken bayani kan irin rashin lafiyar dake damunshi.
Hakanan abokin aikinsa, Dram shima yana can kwance a Asibiti inda tuni har an fara yada rade-radin cewa ya mutu amma iyalansa sun musanta hakan.
A jiyane, Hutudole ya kawo muku rahoton cewa, an garzaya da tsohon Tauraron fina-finan Indiya, Dram zuwa Asibiti.
A yau da safe kuma an tashi da rade-radin cewa ya rugamu gidan gaskiya.
Saidai da Iyalansa sun musanta lamarin.
Sun ce har yanzu yana karbar magani a Asibiti.
Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya bayyana cewa a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Tinubu da wasu 'yan Najeriya sun taba kai kara zuwa kasar Amirka cewa ana yiwa Kiristoci Khisan Kyiyashi
Yace amma yanzu da yake ba sune suka kai karar ba suna karyatawa.
https://twitter.com/channelstv/status/1987959434296127732?t=w3fNTVRr9QH7YA8R493yNA&s=19
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a TVC News.
Ya kara da cewa, Amurka na da 'yancin Shigowa Najeriya dan kawowa Kiristoci dauki.
INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN:
Sokoto mun yi rashi…
Matar marigayi tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari Hajiya Sutura Shehu Shagari ta rasu.
Ubangiji Allah ya jikanta da rahama.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aika da wakilai daga Najeriya zuwa kasar Ingila inda suka kaiwa Sanata Ike Ekweremadu dake tsare a gidan yari ziyara.
Wakilan da Shugaba Tinubu ya aika sune Yusuf Maitama Tuggar da Lateef Olasunkanmi Fagbemi da sauransu.
Jakadan Najeriya a Landan, Mohammed Maidugu ne ya karbi tawagar ta Gwamnati.
https://twitter.com/julezolayinka/status/1987900261369610538?t=QSWjrnK69H95bJyJ3BjepA&s=19
Bature me sharhi akan Al'amuran yau da kullun, George Galloway ya bayyana cewa arzikin da Allah yawa Najeriya ya kamata ace kowane dan kasar Miloniya ne.
Ya bayyana hakane a wani jawabi da yayi.
Inda yace Amma Azzaluman shuwagabanni da aka rika aamu a kasarne suka rika dakushe 'yan kasar da hanasu ci gaban da ya kamata.
https://www.tiktok.com/@georgegallowayofficial/video/7570694498234289430?_t=ZS-91HuozcSN5V&_r=1
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC na neman tsohon karamin Ministan man fetur kuma tsohon Gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva ruwa a jallo.
EFCC a wata sanarwa data fitar tace tana neman Sylva ne bayan umarnin wata kotu a Legas ranar 6 ga watan Nuwamba inda ake zarginshi da yin canjin Dala $14,859,257 ba bisa ka'idaba.
EFCC tace duk wanda ya ganshi ya gaggauta sanar da ofishinta mafi kusa ko kuma ofishin 'yansanda.
Timipre dai ne ake zargin ya dauki nauyin yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Jhuyin mulki wanda aka dake a kwanannan.
Rahotanni sun bayyana cewa, An kwantar da tauraron Fina-finan Indiya, Dram a Asibiti.
Rahoton yace, Dram ya karbi maganine.
Saidai wasu bayanai sun rika cewa yana can kwance magashiyan bashi da lafiya.
Amma daya daga cikin 'ya'yansa, Sonny Deol yace ba gaskiya bane mahaifinsu ya je a duba lafiyarsa ne.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero ya yi kira da a janyo jami'o'in Najeriya masu zaman kansu su shiga cikin ƙungiyar ASUU.
Ajaero ya buƙaci ƙungiyar ASUU ta fara tattaunawa da shugabannin jami'o'in na Najeriya domin fahimtar da su buƙatar shiga ƙungiyar domin a gudu tare a tsira tare, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ajaero ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a lokacin da yake jawabi a lokacin da aka tattaunawa da shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna a shirin Toyin Falola.
Shugaban na NLC ya ce "dole a daina cin zarafi tare da yi wa mambobin ASUU," in ji shi, sannan ya bayyana mamakinsa kan yadda gwamnatin ta gaza wajen tabbatar da alƙawarin da ta sa hannu tun a shekarar 2009.
Ya ce asali an ƙirƙiri ASUU ne domin raba kan NLC, sanan a ...
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa, Abin takaici ne matuka yanda wai idan aka kama 'yan tà'àddà dake Khashewa da Gharkuwa da mutane da yiwa mata fyade ace wai suna da wani hakki na bil'adama da za'a kare musu.
Sanata Ndume yace ai kawai irin wadannan Khashyesu kawai ya kamata a yi.
Yace su ina hakkin mutanen da suke lalatawa rayuwa?
Sanata Ndume ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labarai wadda ta watsu sosai a kafafen sada zumunta.
https://twitter.com/TheBeninBlogger/status/1987744772480479397?t=okCmVbbFFDvvJDAX1_fP7Q&s=19