Thursday, December 18
Shadow
Mu na fama da matsanancin ƙarancin ma’aikata – NAFDAC

Mu na fama da matsanancin ƙarancin ma’aikata – NAFDAC

Duk Labarai
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, NAFDAC, ta koka kan matsanancin ƙarancin ma'aikata. Da ta ke ganawa da manema labarai a Legas a jiya Alhamis, shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ta baiyana cewa a yanzu haka hukumar na da ma'aikata dubu 2 kacal a fadin ƙasar, inda ta ce hakan adadi ne mai matuƙar kankanta duba da irin aikin hukumar. Ta yi kira da a ninka adadin ma'aikatan hukumar sau biyu ko sau uku, inda ta ce aikin da su ke yi na kare lafiyar al'ummar ƙasa baki daya na buƙatar wadatuwar ma'aikata don a samu sakamako mai kyau.
Ɗan bayan Liverpool Kuma dan ƙasar Netherlands, Virgil Van Dijk ya rattaba hannu a tsawaita kwantaragi na shekaru 2 a ƙungiyar

Ɗan bayan Liverpool Kuma dan ƙasar Netherlands, Virgil Van Dijk ya rattaba hannu a tsawaita kwantaragi na shekaru 2 a ƙungiyar

Duk Labarai
Ɗan bayan Liverpool Kuma dan ƙasar Netherlands, Virgil Van Dijk ya rattaba hannu a tsawaita kwantaragi na shekaru 2 a ƙungiyar. Hakan na zuwa ne yayin da rahotanni daga Transfer News Live ke nuni da cewa Luiz Diaz ya ƙi karɓar tayin tsawaita kwantaragi daga Liverpool, inda shi hankalin sa ya yi kan Barcelona.
Nan da watan Disamba farashin kayan masarufi zai sauka>>Inji Masana

Nan da watan Disamba farashin kayan masarufi zai sauka>>Inji Masana

Duk Labarai
Masana tattalin Arziki sun bayyana cewa, nan da watan Disamba na shekarar 2025 farashin kayan masarufi zai sauka da kaso 27.1. latest NESG-Stanbic IBTC Business Confidence Monitor ne suka fitar da wadannan bayanai inda suka ce wannan zai baiwa 'yan kasuwa dama sauran jama'a kwarin gwiwa kan matsin tattalin arzikin da aka samu kai a ciki. Hauhawar farashin kayayyaki da tashin farashin man fetur da karyewar darajar Naira ne kan gaba cikin abubuwan dake damun 'yan Najeriya.
Shugaba Tinubu zai halarci taron ci gaban Kasashe a Abu Dhabi

Shugaba Tinubu zai halarci taron ci gaban Kasashe a Abu Dhabi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai halarci taro kan ci gaban kasashe a Abu Dhabi. Taron zai wakanane ranar 12 zuwa 18 ga watan Janairu inda shi kuma shugaba Tinubu zai bar Najeriya ranar Asabar, 11 ga watan Janairun, kamar yanda me magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya sanar. Onanuga yace Shugaban kasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci shugaba Tinubu zuwa taron.
An hana bude wajan Sayarda Pizza a kasar Ingila saboda tana sa yara kibar data wuce kima

An hana bude wajan Sayarda Pizza a kasar Ingila saboda tana sa yara kibar data wuce kima

Duk Labarai
Garin Bacup dake karkashin Lancs a kasar Ingila ya hana wani kamfanin yin Pizza, me suna Woody’s Pizza ya bude reshe saboda a cewar mahukuntan garin yaran garin kib ta musu yawa. Woody’s Pizza sun so bude reshene a wani tsohon shagon barasa da aka kulle kuma sun ce suna aka sukari da gishiri kadan a Pizza dinsu sannan zasu rika sayen kayan yin Pizza din daga kasuwar garin. Saidai mahukuntan garin sun ce basu yadda ba. Ko da a shekarar 2023 ma, mahukuntan garin Bacup sun taba hana bude wajan cin abinci saboda irin wannan dalili.
Najeriya ta hada kai da kasar China dan horas da sojiji da kera makamai

Najeriya ta hada kai da kasar China dan horas da sojiji da kera makamai

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da kara karfafa hulda tsakaninta da kasar China dan horas da sijoji da kuma kera makamai. Tace hakan hanyace da zata taimakawa kasar wajan yaki da ta'ddanci da sauran matsalolin tsaro. Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa, ranar Alhamis bayan gawar da shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi da ministan harkokin waje na kasar China, Wang Yi. Yusuf yace irin wannan hadaka da kasar China zata taimakawa Najeriya dama makwabtanta wajan samar da tsaro.
Wani ya taimaka ya fito, Saboda na sha maganin mata gashi kuma G-Fresh Al-Amin yace ya fasa Aurena, ina cikin Matsala>>Inji Alpha Charles

Wani ya taimaka ya fito, Saboda na sha maganin mata gashi kuma G-Fresh Al-Amin yace ya fasa Aurena, ina cikin Matsala>>Inji Alpha Charles

G-Fresh Al'amin
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Shahararriyar 'yar Tiktok, Alpha Charles wadda labarai suka watsu sosai cewa, Abokin burminta, watau G-Fresh Al-Amin zai aureta ta fito tace ya fasa. Ta bayyana hakane a wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta. Charles tace ita yanzu abin tausai ce saboda ta sha maganin mata gashi ango G-Fresh Al-Amin yace ya fasa, dan hakane ta yi kiran cewa, idan akwai wanda ya shirya ya fito su yi aure. Saidai ta bayar da sharadi wanda za'a iya ji a bidiyon kamar ...