Thursday, December 18
Shadow
Shugaba Tinubu zai halarci taron ci gaban Kasashe a Abu Dhabi

Shugaba Tinubu zai halarci taron ci gaban Kasashe a Abu Dhabi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai halarci taro kan ci gaban kasashe a Abu Dhabi. Taron zai wakanane ranar 12 zuwa 18 ga watan Janairu inda shi kuma shugaba Tinubu zai bar Najeriya ranar Asabar, 11 ga watan Janairun, kamar yanda me magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya sanar. Onanuga yace Shugaban kasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci shugaba Tinubu zuwa taron.
An hana bude wajan Sayarda Pizza a kasar Ingila saboda tana sa yara kibar data wuce kima

An hana bude wajan Sayarda Pizza a kasar Ingila saboda tana sa yara kibar data wuce kima

Duk Labarai
Garin Bacup dake karkashin Lancs a kasar Ingila ya hana wani kamfanin yin Pizza, me suna Woody’s Pizza ya bude reshe saboda a cewar mahukuntan garin yaran garin kib ta musu yawa. Woody’s Pizza sun so bude reshene a wani tsohon shagon barasa da aka kulle kuma sun ce suna aka sukari da gishiri kadan a Pizza dinsu sannan zasu rika sayen kayan yin Pizza din daga kasuwar garin. Saidai mahukuntan garin sun ce basu yadda ba. Ko da a shekarar 2023 ma, mahukuntan garin Bacup sun taba hana bude wajan cin abinci saboda irin wannan dalili.
Najeriya ta hada kai da kasar China dan horas da sojiji da kera makamai

Najeriya ta hada kai da kasar China dan horas da sojiji da kera makamai

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da kara karfafa hulda tsakaninta da kasar China dan horas da sijoji da kuma kera makamai. Tace hakan hanyace da zata taimakawa kasar wajan yaki da ta'ddanci da sauran matsalolin tsaro. Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa, ranar Alhamis bayan gawar da shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi da ministan harkokin waje na kasar China, Wang Yi. Yusuf yace irin wannan hadaka da kasar China zata taimakawa Najeriya dama makwabtanta wajan samar da tsaro.
Wani ya taimaka ya fito, Saboda na sha maganin mata gashi kuma G-Fresh Al-Amin yace ya fasa Aurena, ina cikin Matsala>>Inji Alpha Charles

Wani ya taimaka ya fito, Saboda na sha maganin mata gashi kuma G-Fresh Al-Amin yace ya fasa Aurena, ina cikin Matsala>>Inji Alpha Charles

G-Fresh Al'amin
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"transform":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Shahararriyar 'yar Tiktok, Alpha Charles wadda labarai suka watsu sosai cewa, Abokin burminta, watau G-Fresh Al-Amin zai aureta ta fito tace ya fasa. Ta bayyana hakane a wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta. Charles tace ita yanzu abin tausai ce saboda ta sha maganin mata gashi ango G-Fresh Al-Amin yace ya fasa, dan hakane ta yi kiran cewa, idan akwai wanda ya shirya ya fito su yi aure. Saidai ta bayar da sharadi wanda za'a iya ji a bidiyon kamar ...
El-Rufai ne ya sani, Inji tsohon Kwamishina a Gwamnatin Jihr Kaduna Bashir Sa’idu da aka kama sa satar kudi

El-Rufai ne ya sani, Inji tsohon Kwamishina a Gwamnatin Jihr Kaduna Bashir Sa’idu da aka kama sa satar kudi

Duk Labarai
Tsohon Kwamishina a jihar Kaduna lokacin mulkin tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, watau Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu da yanzu haka yake tsare bisa zargin satar kudaden gwamnati, yace Gwamna El-Rufai ne ya sashi duk abinda yayi. Ya bayyana hakane a cikin jawabin da ya baiwa 'yansanda bayan kamashi, kamar yanda wani dansanda da baiso a bayyana sunansa ya gayawa manema labarai kamar yanda jaridar TheNation ta ruwaito. Ana zargin Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu da sayar da daloli mallakin jihar ta Kaduna akan farashin da bai kamata ba. Kotu tace ya aikata laifinne a shekarar 2022.
Kuma Dai: Kwanaki kadan bayan da EFCC ta kori jami’anta daga aiki saboda cin hanci da rashawa, Dala $400,000 da Gwalagwalai na miliyoyin Naira sun bace a ofishin EFCC din

Kuma Dai: Kwanaki kadan bayan da EFCC ta kori jami’anta daga aiki saboda cin hanci da rashawa, Dala $400,000 da Gwalagwalai na miliyoyin Naira sun bace a ofishin EFCC din

Duk Labarai
Rahotanni daga ofishin hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC sun bayyana cewa an nemi tsabar kudi har dala $350,000 zuwa dala $400,000 ba'a gani ba. Hakanan akwai wasu gwalagwalai na miliyoyin Naira da suma auka bace tare da kudin. Lamarin ya farune a ofishin hukumar dake jihar Legas, kamar yanda kafar PRNigeria ta ruwaito. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da EFCC ta kori ma'aikata 27 saboda samunsu da rashawa da cin hanci da zamba cikin aminci. Wannan lamari yasa 'yan Najeriya na diga ayar tambaya akan hukumar ta EFCC da aka sani da yaki da rashawa da cin hanci amma da alamu me dokar bacci na neman bugewa da yin gyangyadi. Majiyar tamu tace ta yi kokarin jin ta bakin kakakin EFCC kan wannan sabon lamari amma abu ya faskara.
‘Yan Najeriya sun bayyana cewa man fetur din matatar man Dangote na dadewa kamin ya kare

‘Yan Najeriya sun bayyana cewa man fetur din matatar man Dangote na dadewa kamin ya kare

Duk Labarai
'Yan Najeriya da yawa ne suka bayyana jin dadinsu da amfani da man fetur din matatar man fetur ta Dangote. Da yawa da jaridar Punchng ta yi hira dasu sun ce sun ji dadin amfani da man fetur din na matatar man fetur ta Dangote saboda yana dadewa bai kone ba a mota idan aka kwatantashi da wanda suke amfani dashi a baya. Matatar man fetur ta Dangote ta bayyana cewa, ta yi hadaka da gidajen sayar da man fetur na MRS dan ta rika sayarwa 'yan Najeriya man fetur din da Rahusa. Wasu daga cikin wadanda aka yi hira dasu sun ce gwamnati ta yaudaresu kan matatar man fetur din Dangote inda suka ce man da ake shigowa dashi bashi da inganci.
Kotu ta bayar da belin Mahadi Shehu kan Milyan uku

Kotu ta bayar da belin Mahadi Shehu kan Milyan uku

Duk Labarai
Wata babbar kotun jihar Kaduna ta bayar da belin mai fafutuka Mahdi Shehu kan kudi Naira miliyan uku da kuma mutane biyu da za su tsaya masa a kan wannan kudi. Kotun ta ce wadanda za su tsaya wa dole ne su zama sanannun malamai a Nageriya. Sannan ta kwace fasfonsa kuma tace dolene sai ya rika zuwa wajan jami'an tsaro duk wata ana ganinsa, kuma duk idan ya zama dole sai yayi tafiya, ya sanar da kotun. Kotun tace ta amince ta bayar da belinsa ne saboda a yanzu ba'a tabbatar da laifin daya aikata ba.