Thursday, January 15
Shadow
Kalli Bidiyo: Ni nasan Mu Kirista ne za’a bari da wahalar biyan Harajin da shugaba Tinubu zai saka, amma Musulmai ba zasu biya harajin ba>>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Kalli Bidiyo: Ni nasan Mu Kirista ne za’a bari da wahalar biyan Harajin da shugaba Tinubu zai saka, amma Musulmai ba zasu biya harajin ba>>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Duk Labarai
Malamin Kirista, Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa, Musulmai ba zasu biya kudin Harajin da shugaba Tinubu zai saka ba. Yace su Kirista ne kadai za'a bari da biyan Harajin. Ya bayyana cewa ko gwal da sauran ma'adanan kasa da ake hakowa a Arewa Gwamnati bata amfana dashi amma Man Fetur da ake hakowa a kudu, kowa na amfana dashi. https://www.tiktok.com/@luckyudu/video/7585176684165418247?_t=ZS-92Lg7c70IHh&_r=1
Kalli Bidiyon:Kai da ka kasa hana Matarka yin bikin Birthday shine kake tunanin zaka hani yin da’awa? Dr. Hussain ya gayawa Baffa Hotoro

Kalli Bidiyon:Kai da ka kasa hana Matarka yin bikin Birthday shine kake tunanin zaka hani yin da’awa? Dr. Hussain ya gayawa Baffa Hotoro

Duk Labarai
Dr. Hussain ya mayarwa da Baffa Hotoro raddi kan sukar da Baffa Hotoron yayi game da kalaman Dr. Hussain na cewa yana rokon Allah kada ya kai matsayin da sai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ceceshi ranar tashin qiyama kamin ya shiga Aljannah. Dr. Hussain a wani Bidiyo daya yadu sosai a kafafen sada zumunta yayi ta Zhaghin Baffa Hotoro inda yace shi da ya kasa hana matarsa yin bikin Birthday shine yake tunanin zai hanashi yin da'awa? Baffa Hotoro dai ya baiwa Dr. Hussain shawarar ya koma makaranta inda yace kalaman na Dr. Hussain jahilci ne. https://www.tiktok.com/@sanda08924/video/7585347083704503608?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7585347083704503608&source=h5_m&timestamp=1766136235&...
Kungiyar ‘yan Kasuwar man fetur IPMAN ta ce membobinta su fara sayen man fetur daga matatar man fetur ta Dangote

Kungiyar ‘yan Kasuwar man fetur IPMAN ta ce membobinta su fara sayen man fetur daga matatar man fetur ta Dangote

Duk Labarai
Kungiyar 'yan kasuwar Man fetur ta IPMAN ta baiwa membobinta shawarar su fara sayen man fetur daga matatar man Dangote. Shugaban kungiyar, Abubakar Maigandi Shettima ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace saye a wajan matatar man Dangote yafi musu sauki fiye da shigo da man daga kasashen waje. Yace kuma suma suna kokarin su gina tasu matatar man fetur din. Hakan na zuwane bayan da Dangote ya karya farashin man fetur din zuwa Naira 740 akan kowace lita kamar yanda wasu gidajen man fetur na MRS ke sayarwa.
Hana ‘yan Najeriya shiga Amurka: Sai da Muka Gargadi Masu zuwa wajan Amurka su bata sunan Najeriya da cewa, idan Amurka ta tashi daukar mataki haddasu abin zai shafa>>Inji Bulama Bukarti

Hana ‘yan Najeriya shiga Amurka: Sai da Muka Gargadi Masu zuwa wajan Amurka su bata sunan Najeriya da cewa, idan Amurka ta tashi daukar mataki haddasu abin zai shafa>>Inji Bulama Bukarti

Duk Labarai
Shahararren Lauya kuma dan fafutuka Bulama Bukarti ya bayyana cewa, sai da suka gargadi 'yan Najeriya masu zuwa kasar Amurka su bata sunan Najeriya cewa idan fa Amurkar zata dauki mataki haddasu zai shafa. Hakan na zuwane bayan da Amurka ta kakabawa 'yan Najeriyar doka me tsauri kan shiga kasarta. Wasu Kiristoci dai sun je kasar Amurka inda suka kai mata koken cewa Musulmai na musu Qìsàn Gilla, abinda yasa Amurkar ta sha alwashin daukar mataki akan Najeriya. https://twitter.com/bulamabukarti/status/2001726456746201452?t=u4xk0l9bcRsWlcWbEHbBKg&s=19
Kalli Bidiyon yanda ake ta tururuwar zuwa ganin katafaren gidan da Aminu Saira ya gina

Kalli Bidiyon yanda ake ta tururuwar zuwa ganin katafaren gidan da Aminu Saira ya gina

Duk Labarai
Da yawa na ta tururuwar zuwa ganin gidan da Malam Aminu Saira ya gina. Gidan malam Aminu Saira ya dauki hankula sosai musamman a kafafen sada zumunta inda akai ta cece-kuce akai. An ga yanda aka shirya wata Qarya-Qaryar Liyafa dan murnar gina gidan. Naziru Sarkin Waka dan uwa ga Aminu Saira na daga cikin wanda suka je ganin Gidan. https://www.tiktok.com/@mailafiyasairamovies/video/7584537575541476616?_t=ZS-92LTOoNdNk9&_r=1
Kalli Bidiyon: Idan na hadu da Naziru Sarkin Waka, za tsaya ne inga zai kirani da sarkin Wakar kasar Hausa ko kuwa? Inji Rarara

Kalli Bidiyon: Idan na hadu da Naziru Sarkin Waka, za tsaya ne inga zai kirani da sarkin Wakar kasar Hausa ko kuwa? Inji Rarara

Duk Labarai
Tauraron Mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa idan ya hadu da Naziru Sarkin Waka, zai tsaya ne ya ga zai kirashi da Sarkin Wakar Kasar Hausa ko kuwa? Rarara dai an bashi sarautar Sarkin Wakar Qasar Hausa a Masarautar Daura wanda lamarin ya dauki hankula Saidai a wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Hikima, Rarara yace, a baya idan yaga Naziru Sarkin Waka yana kiranshi da Sarki. Yace amma yanzu idan suka hadu zai tsaya ne ya ga shin Nazirun zai kirashi da sunan Sarkin Wakar Qasar Hausa? https://www.tiktok.com/@hikima_radioandtv/video/7585264612770155797?_t=ZS-92LRx7wCnVg&_r=1
Kalli Bidiyon: Nasan da yawanku kun yadda da cewa ‘yan siyasa makaryatane, Mayaudara, Amma ni ba haka nake ba>>Inji Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare

Kalli Bidiyon: Nasan da yawanku kun yadda da cewa ‘yan siyasa makaryatane, Mayaudara, Amma ni ba haka nake ba>>Inji Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare

Duk Labarai
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare yace bai taba yin rantsuwa da Qur'ani ba sai da ya zama Gwamna. Yace dan haka yasa irin nauyin dake kansa. Yace mutane da yawa sun yi imanin cewa, 'yan Siyasa Mayaudara ne Maqaryata. Yace amma shi ba haka yake ba. https://twitter.com/AM_Saleeeem/status/2001755817855312171?t=pe_6M-aaghuYxjKdf11qKw&s=19
Kalli Bidiyon: Yarinya na gabanka ma ya ka kare da tarbiyyarta ballantana ka turaka karatu wani gari? Inji Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah

Kalli Bidiyon: Yarinya na gabanka ma ya ka kare da tarbiyyarta ballantana ka turaka karatu wani gari? Inji Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah

Duk Labarai
Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah ya jawo hankalin iyaye kan daina kai 'ya'ya makaranta wani Gari. Yace yarinya na gabanka ma ya ka kare da tarbiyyarta ballantana kuma ka turata Karatu wani gari. Ya bayyana cewa, yace gara ta zauna a gida idan miji yazo shikenan idan ma bai zo ba ta ci gaba da zuwa Islamiya. https://www.tiktok.com/@abdurrahmanumarr/video/7585311876637084949?_t=ZS-92LO0pIRTqD&_r=1