Tauraron mawakin, Najeriya, Asake a yayin da ya je Aikin Umrah an ganshi yana ta kokarin taba ka'aba amma bai yi nasara ba.
Bidiyon lamarin ya dauki hankula sosai inda akai ta yadashi a gurare da bayyana mabanbanta ra'ayoyi.
https://twitter.com/i/status/2032638933318697082
Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa, Gwamnatin jihar ta mayar da malamin Makaranta, Abduljalal Usman bakin aikinsa bayan da suka ta yi yawa a kafafen sadarwa.
Da farko dai an dakatar da Abduljalal Usman ne na tsawon watanni 3 babu Albashi bayan da ya fito yayi korafin cewa bai gode da tallafin abinci sa'i daya na Shinkafa da Masara ba da aka bashi.
Bidiyon nasa ya watsu a kafafen sada zumunta sosai.
Hakan yasa aka dakatar dashi.
Saidai bayan hakan an yi Allah wadai da lamarin, abinda yasa aka mayar dashi bakin aikinsa kenan inda hukumar tace za'a ci gaba da bincike kan abinda ya aikata.
Shahararren dan kasuwa na jihar kaduna, Mahdi Shehu ya aikawa Abduljalal Usman tallafin Naira 120,000 sannan ya ce masa idan dai wannan lamari yasa aka koreshi daga aiki, yayi masa alkawar...
Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Saudiyya ta gayyaci tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad zuwa sakawa dakin Ka'aba Turare.
Malam Bashir Ahmad da kansa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta inda ya bayyana cewa wannan ba karamin karramawa bace a gareshi.
https://twitter.com/i/status/2032832756166635587
Tsohon Ministan sadarwa, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ya taya Malam Bashir Murna inda yace yana fatan Allah ya karbi wannan abu a matsayin Ibada ya bashi lada.
https://twitter.com/i/status/2032915410522136738
Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa, an dakatar da wani malamin makaranta a jihar saboda ya fito ya soki rabon shinkafa da masa Sa'i guda da aka bashi.
Malamin a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta an ganshi yana fadar cewa shi bai gode ba a matsayinsa na malamin makaranta da aka bashi wannan a matsayin tallafi.
https://www.tiktok.com/@jalalkmb/video/7616007512118152468?_r=1&_t=ZS-94gC28EsZ7Y
Sahara Reporters ta wallafa cewa, an dakatar da malamin saboda wannan Bidiyon.
A wata takardar dakatarwar da Sahara Reporters ta wallafa, anga cewa an dakatar da malmin me suna Abduljalal Usman na tsawon watanni 3 ba tare da Albashi ba.
Takardar dai ta zargeshi da sakaci da aiki.
Amma a zahirin gaskiya da yawa sun ce saboda wancan Bidiyon ne da yayi.
Wannan wani farar fata ne da ya tashi yana kuka saboda an sace masa kayansa a kasar Saudiyya inda yaje aikin umrah.
An ga Bidiyonsa na yawo a kafafen sada zumunta inda mutane da dama ke ta Alhinin faruwar lamarin.
https://www.tiktok.com/@muhammadsunnahaljosawy/video/7616851832333274375?_r=1&_t=ZS-94g9vci3oAq
Wannan matashin dake ikirarin Malunta ya bayyana cewa, yana neman tallafin Raguna 100 dan yayi wani aiki wanda duk Tshàgyèràn Dhàjì na Najeriya sai sun rigamu gidan gaskiya.
Ya yi ikirarin cewa tuni aka fara tura masa tallafi dan gudanar da wannan aiki har daga kasashen waje.
https://www.tiktok.com/@sahiburruhani/video/7616834522247695636?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7616834522247695636&source=h5_m×tamp=1773480184&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7606977366144993025&a...
Wannan wani dan Tiktok ne da ya bayyana cewa insha Allahu, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai rigamu gidan gaskiya bayan Sallah.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sadarwa inda aka ganshi rike da Qur'ani.
https://www.tiktok.com/@yakson.geeyy3/video/7613407863028960520?_r=1&_t=ZS-94g5rWGAIPx
A wani Bidiyo da ya watsu sosai, an ga Tauraron mawakin Najeriya, Asake tare da Dansandan kasar Saudiyya sun samu rashin Jituwa.
Dansandan dai na baiwa Asake Kariyane yayin da yake aikin Hajji.
Saidai an ga masoya Asake na ta daukar hoto dashi.
Dansandan yayi kokarin hana Asake daukar hoto da masoyan nashi inda ya turashi gaba yace muce, amma Asake shima sai ya ture dansandan.
Lamarin ya dauki hankula sosai inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.
https://www.tiktok.com/@gossiploadedtv/video/7616968075199532308?_r=1&_t=ZS-94fs7JeFXnt
An hangi mawakin Najeriya, Asake a cikin wata motar Alfarma a kasar Saudiyya inda yake Aikin Umrah
Da yawa sun bayyana cewa a ko ina babba, babba ne.
https://www.tiktok.com/@asakelife/video/7616753614941375775?_r=1&_t=ZS-94eztVLFEq9