Monday, April 6
Shadow
Gwamnatin Kaduna ta ƙwace gidajen da El-Rufa’i ya sayar

Gwamnatin Kaduna ta ƙwace gidajen da El-Rufa’i ya sayar

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Uba Sani ya bayar da umarnin ƙwace gidaje da filayen da tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ta Malam Nasiru El-Rufa'i ta sayar a jihar. Gidajen da filayen da aka ƙwacen sun haɗa da waɗanda tsohon gwamnan ya sayar a kwalejin Queen Amina da ke Kaduna da kwalejin Alhuda-huda da kwalejin Government Commercial da ke Zaria. Umarnin na ƙunshe ne a wata sanarwar da aka fitar, a ranar Talata da daddare, mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr AbdulKadir Mu’azu Meyere. Sanarwar ta bayyana cewa an ƙwace gidajen da filayen ne saboda amfanin al'umma. Sai dai an jima ana takun saƙa tsakanin gwamna Uba Sani mai ci yanzu, da kuma wanda ya gada, Malam Nasir El-Rufa'i.
Ya kamata shuwagabannin Najeriya su yi koyi da halin  marigayi Fafaroma na son Talakawa>>Inji Jam’iyyar NNPP

Ya kamata shuwagabannin Najeriya su yi koyi da halin marigayi Fafaroma na son Talakawa>>Inji Jam’iyyar NNPP

Duk Labarai
Wanda ya kirkiro jam'iyyar NNPP, Boniface Aniebonam ya yi kira ga mutanen Najeriya da su yi koyi da halin Marigayi Fafaroma Francis na son Talakawa. Ya bayyana hakane a sakonsa na ta'aziyyar fafaroman inda yace babu ta yanda za'a yi a ci gaba da barin wagegen gibin dake tsakanin Talakawa da masu kudi yana kara karuwa amma ace ana son zaman Lafiya. Yace dolene Gwamnati ta mayar da hankali wajan yaki da Talauci kuma hakan ba aikin gwamnati ne kadai ba hadda masu hannu da shuni.
Ba bÒm bane ya tashi a Kaduna, Bindiga hadin gidace ta tashi ba da shiri ba

Ba bÒm bane ya tashi a Kaduna, Bindiga hadin gidace ta tashi ba da shiri ba

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi karin haske kan rahotannin dake cewa Bam ya fashe a Unguwar Abakpa dake jihar. A jiya ne dai rahotanni suka rika yawo cewa Bam din ya fashe ne inda har ya kashe yara biyu da jikkata wasu mutane 3, Kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Saidai a jawabin da gwamnatin jihar ta fitar ta bakin Kwamishinan tsaron cikin gida, Sir James A. Kanyip, KSM; PhD tace rahoton ba gaskiya bane. Yace abinda ya faru shine, Bindiga hadin gida ce ta tashi ba tare da shiri ba shine abinda ya faru. Yace Tuni jami'an tsaro suka kai dauki wajan da abin ya faru sannan ana kan bincike.
Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja.

Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja.

Duk Labarai
Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja. Gwamnan jihar Neja Manomi Umaru Mohammed Bago ya ayyana sababbin dokoki da zasu fara aiki nan take a faɗin jihar. Gwamnatin jihar ta Neja ta haramta bangar siyasa da duk wani abu mai kama da haka a faɗin jihar. Duk wanda aka same shi da wani makami da ya haɗa da wuka ko sanda a ɗauke shi a matsayin Ɗan fashi da makami, idan kuma yayin gardama da jami'an tsaro aka harbe shi da harsashen bindiga kada abada shi har sai ƴan uwan shi sun biya kuɗin wannan harsashen da akayi asarar shi. Duk wanda aka gani namiji da kitso ko Dada akan shi a kama shi a kuma aske kan. An Haramta amfani da Mashi mai ƙafa Biyu da mai ƙafa Ukku Keke Napepe daga ƙarfe Shidda na Yamma ...
‘Yan Najeriya miliyan 2 ne ke fama da cutar Kanjamau me karya garkuwar jiki: Karanta Jadawalin Jihohin da suka fi yawan masu cutar a Najeriya

‘Yan Najeriya miliyan 2 ne ke fama da cutar Kanjamau me karya garkuwar jiki: Karanta Jadawalin Jihohin da suka fi yawan masu cutar a Najeriya

Duk Labarai
Jihohi 3 ne suka fi yawan masu dauke da cutar Kanjamau me karya garkuwar jiki a Najeriya. Jihohin sune Rivers, Benue, and Akwa Ibom, hakan ya bayyana ne daga hukumar dake kula da cutar ta kasa. Rahoton yace mutane sama da miliyan 2 ne ke fama da cutar a Najeriya. Jihohin dake da yawan mutane masu cutar sune kamar haka: Rivers nada mutane 208,767 Benue na da mutane 202,346 Jihar Akwa Ibom na da mutane 161,597 Jihar Legas na da mutane 108,649 Jihar Anambra na da mutane 100,429 Sai Abuja dake da mutane 83,333 Delta na da mutane (68,170) Imo na da mutane (67,944) Enugu na da mutane (61,028) Edo na da mutane (60,095) Taraba na da mutane (58,460) abia na da mutane (54,655) Kaduna na da mutane (54,458) Kano na da mutane (53,972) Jihar Filato...
Sanata Neda Imasuen na shirin komawa jam’iyyar APC

Sanata Neda Imasuen na shirin komawa jam’iyyar APC

Duk Labarai
Sanata Neda Imasuen daga jihar Edo na shirin komawa jam'iyyar APC daga jam'iyyar Labour Party. Hakan na faruwa ne yayin da ake ganin yana hada alaka me kyau da 'yan APC a jihar ta Edo kamar yanda kafar jaridar Vanguard ta ruwaito. Hakanan Rahoton yace Gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya aike da wakilinsa me bashi shawara a harkar siyasa dan ya kara jawo Neda Imasuen ya shiga jam'iyyar sa.
Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar ‘yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu’a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiyar Rashin Lafiya

Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar ‘yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu’a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiyar Rashin Lafiya

Duk Labarai
Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar 'yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu'a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiya. Allah Ubangiji ya kawo masa ɗauki na gaggawa.