Tuesday, April 7
Shadow
Taliya Ba Za Ta Yi Tasiri Ba A Zaɓen 2027 Saboda Kan Mage Ya Waye, Cewar Sanata Babba Kaita

Taliya Ba Za Ta Yi Tasiri Ba A Zaɓen 2027 Saboda Kan Mage Ya Waye, Cewar Sanata Babba Kaita

Duk Labarai
Taliya Ba Za Ta Yi Tasiri Ba A Zaɓen 2027 Saboda Kan Mage Ya Waye, Cewar Sanata Babba Kaita. Wayewa a siyasa ita ce damawa da kowa ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ko yankin da mutum ya fito ba, don haka ya zama wajibi a dama da dukannin bangarorin ƙasar nan muddin ana yin siyasa ne don cigaban al’umma. Yin wani abu akasin haka kuskure ne babba a siyasance, domin mutane ba su da mantuwa. Komai daren daɗewa za su rama abin da aka yi musu idan lokacin yin ramuwar ya zo. Duk da cewa mutane na cikin yunwa da fatara, a wannan karon Taliyarka ba za ta yi ma amfanin komai ba saboda kan mage ya waye! Daga Jamilu Dabawa
Kalli Bidiyon hudubar da uba yawa diyarsa bayan daurin aure da ta dauki hankula sosai

Kalli Bidiyon hudubar da uba yawa diyarsa bayan daurin aure da ta dauki hankula sosai

Duk Labarai
Wani mahaifi bafulatani ya dauki hankulan mutane sosai musamman a kafafen sadarwa bayan da aka ga irin hudubar da yawa diyarsa da aka daurawa aure. Bidiyon hudubar ya watsu sosai a kafafen sadarwa inda ake ya sanya masa Albarka. Ya gargadi diyarsa kada ta sake ta saurari kowa idan ba mijinta ba. https://www.tiktok.com/@fulani_tutor/video/7232318925684460805?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7232318925684460805&source=h5_m&timestamp=1745185435&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7483198445273974549&am...
Atiku ya nemi Peter Obi ya zama mataimakinsa a 2027 dan su kwace mulki a hannun Tinubu, inda shi kuma yayi Alkawarin yin mulki sau daya ya sauka ya barwa Peter Obin

Atiku ya nemi Peter Obi ya zama mataimakinsa a 2027 dan su kwace mulki a hannun Tinubu, inda shi kuma yayi Alkawarin yin mulki sau daya ya sauka ya barwa Peter Obin

Duk Labarai
Rahotanni daga bangaren Atiku na cewa jiga-jigai sun nemi hada kai da Peter Obi ganin yana da mabiya sosai musamman a kudancin Najeriya. Rahoton yace an nemi goyon bayan Peter Obi dan ya zama mataimakinsa a shekarar 2027 dan su kwace mulki daga hannun shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Rahoton yace bangaren Atiku sun yi Alkawurin yin mulki sau daya inda a shekarar 2031, za'a barwa Peter Obi shi kuma yayi takarar shugaban kasa. Saidai bangaren Peter Obi sun ki amincewa inda suka ce ai kudu bata kammala wa'adinta na zango biyu ba kamar yanda Buhari yayi. Dan haka suka ce idan ba Peter Obi bane zai zama ahugaban kasa ba, to basu yadda ba. Saidai ana ganin har yanzu wannan tattaunawa bata kare ba inda ake tsammanin zata iya cimma gaci.
Kalli Bidiyo: Tinubu dan Kanone>>Inji Ganduje

Kalli Bidiyo: Tinubu dan Kanone>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC, Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dan Kanone kuma sunansa Ashiru. Ya bayyana cewa da aka kaishi Legas ne sai yarbawa suka mayar dashi Asiwaju. Yace kuma dayan sunansa shine Bala inda Yarbawa nan ma suka mayar dashi Bola. Kalli Bidiyon anan https://www.youtube.com/watch?v=Olv-J_MF5gQ?si=tgPP_rA4LORA_o-w Gandune ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sadarwa.
Manyan Limaman Kiristoci sun yi ruwan Allah wadai ga gwamnatin Tinubu inda suka ce Ya magance matsalar Talauci data tsaro

Manyan Limaman Kiristoci sun yi ruwan Allah wadai ga gwamnatin Tinubu inda suka ce Ya magance matsalar Talauci data tsaro

Duk Labarai
Manyan malaman kiristoci sun yi ruwan Allah wadai ga gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka bukaci da ya kawo hanyar kawar da matsalar tsaro data talauci da matsin tattalin arziki. Sun bayyana hakanne a sakonnin bukukuwan Easter daban-daban da suka fitar. Misali babban fasto, Bishop Matthew Hassan Kukah ya misalta halin da Najeriya ke ciki da lokacin da aka gicciye Yesu inda yace Tinubu ya sauko da mutanen Najeriya daga gicciyewar shedan. Bishop Kuka yayi kira ga gwamnatin data dauki matakan gaggawa na kawo karshen matsalolin tsaro da yunwa da sauransu. Yace mafi yawancin 'yan Najeriya sun yanke tsammanin samun canji amma su a matsayinsu na kirista basu yanke tsammani ba. Yace duk da ba Tinubu bane ya saka 'yan Najeriya a cikin wannan hali ba amma yana Kiran ...
Fararoma yayi kiran a yi Sulhu a Gaza

Fararoma yayi kiran a yi Sulhu a Gaza

Duk Labarai
Babban Limamin Kirista, Fafaroma Francis ya nemi a yi sulhu a yakin da ake tsakanin kungiyar Hamas da Israela. Yayi wannan kirane a yayin da ake bukukuwan Easter. Yawan wanda aka kashe a Falasdin ya haura mutane dubu 50 ciki hadda mata da kananan yara. Fafaroma ya kuma bayyana a karin farko tun bayan da yayi doguwar rashin lafiya a bainar jama'a. Hakanan Mataimakin shugaban kasar Amurka, J.D Vance ya halarci fadar Fafaroman yayin da ake bukukuwan Easter.
Najeriya ta mayar da ƴan Mali 62 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba

Najeriya ta mayar da ƴan Mali 62 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba

Duk Labarai
Hukumar shige da fice ta Najeriya ta tabbatar da mayar da wasu ƴan Mali 62 da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba. Cikin wata sanarwar da babban kwanturolan hukumar mai lura da kan iyakar Illela - inda ta nan ne aka fitar da mutanen - Tony Akuneme ce mutanan sun haɗa da maza 51 da kuma mata 11, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar, NAN ya ruwaito. Mista Akuneme ya ce jami'an hukumar ne suka yi wa mutanen rakiya daga shalkwatar hukumar shige da fice ta ƙasa da ke Abuja zuwa kan iyakar Illela da ke jihar Sokoto, cikin motocin bas biyu. Ya ƙara da cewa bayan tanatance takardunsu, an miƙa su ga jami'an ƴansandan Nijar da ke Birnin Konni. A baya-bayan nan Najeriya mayar da ƴan ciranin da ke shiga ƙasar daga maƙwabtan ƙasashe ba tare da cikakkun takardun izini ba. A watanni...
Rashin Wutar Lantarki na Kwanki 10 a jihar Kano ya gurgunta harkokin tattalin arzikin jihar inda Cajin waya yanzu ana karbar Naira 200, jarkar ruwa ma ta koma Naira 200

Rashin Wutar Lantarki na Kwanki 10 a jihar Kano ya gurgunta harkokin tattalin arzikin jihar inda Cajin waya yanzu ana karbar Naira 200, jarkar ruwa ma ta koma Naira 200

Duk Labarai
Rashin tsayayyiyar wutar lantarki na tsawon lokaci na sama da kwanaki 10 ya jawo dakatar da kasuwanci a cikin ƙwaryar birnin Kano da kewaye. Wasu mazauna Kano da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Lahadi, sun koka game da rashin sanin tabbacin abin da za su yi bayan faɗuwar babban layin wutar lantarki wanda ya jefa al’umma cikin duhu da shafar kasuwanci da al’umma a gidajensu. Da yawa daga cikin ‘yan kasuwa sun koka game da illar rashin wuta ga kasuwancinsu. Wani mai gidan otel da unguwar Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Fage, Jude Michael, ya ce yana cikin tashin hankali. Michael ya ce ya rasa kwastamominsa sakamakon rashin wuta da yake amfani da ita wajen ajiye kayan abin sha. “Na shafe tsawon kwanaki ina aiki da Janareta kuma har ya fara taɓa k...
‘Yan Bìndìgà sun tare motar Bas cike da mutane suka sàcèsù akan hanyar Malunfashi zuwa Funtua

‘Yan Bìndìgà sun tare motar Bas cike da mutane suka sàcèsù akan hanyar Malunfashi zuwa Funtua

Duk Labarai
'Yan Bindiga a daren ranar Alhamis sun tare wata Motar Bas inda suka sace mutanen cikinta su duka. Motar dai na tafiyane akan Titin Malunfashi zuwa Funtua. Rahoton yace lamarin ya farune a daidai kauyen Burdugau kamar yanda me amfani da kafar X, Bakatsine ya bayyana. Saidai zuwa yanzu babu wata sanarwa daga hukumomi game da lamarin.
Fati Karishma Kenan, Wadda A Shekarun Baya Kaf Masana’antar Finafinan Hausa Ba Wacce Ta Kai Ta Iya Rawa

Fati Karishma Kenan, Wadda A Shekarun Baya Kaf Masana’antar Finafinan Hausa Ba Wacce Ta Kai Ta Iya Rawa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Fati Karishma Kenan, Wadda A Shekarun Baya Kaf Masana'antar Finafinan Hausa Ba Wacce Ta Kai Ta Iya Rawa Ko kun tuna ta?