Hajji 2025: Za a Fara Jigilar Alhazan Kano Ranar 13 Ga Mayu
Hajji 2025: Za a Fara Jigilar Alhazan Kano Ranar 13 Ga Mayu
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana cewa za a fara jigilar alhazan jihar zuwa ƙasa mai tsarki a ranar 13 ga Mayu, 2025.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Sulaiman A. Dederi, Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukumar ya fitar.
Shugaban hukumar, Alhaji Lamin Rabi'u Danbappa, ne ya sanar da hakan yayin wata ziyara da ya kai cibiyoyin bita na kananan hukumomin Ungogo da Bichi, a wani bangare na shirin Hajjin shekarar 2025.
Ya bayyana cewa, bisa ga jadawalin da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta fitar, za a fara jigilar alhazan Kano ta jirgin Max Air. Alhaji Lamin ya ce tuni hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba don tabbatar da nasarar jigilar alhazan cikin tsari da kwanc...








