Ƴànbìndìgà sun kàshè mutane biyu tare da sàcè mutum ɗaya a Kano
Wasu da ake zargin ƴan fashin jeji ne sun kai hari garin Faruruwa da ke Karamar Hukumar Shanono a Jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da ba a bayyana adadinsu ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne a kasuwar garin da misalin karfe 7 na dare a jiya Alhamis, inda suka fara harbe-harbe kan me uwa da wabi.
Wani shaida, Ibrahim Faruruwa, ya ce maharan sun yi yunkurin sace wani hamshakin dan kasuwa, Alhaji Haruna Halilu, sai dai ba ya shagon nasa a lokacin harin.
Ya ce: “Da basu samu Alhaji Haruna ba, kawai sai suka sace dansa, Mas’ud.”
Ya kara da cewa maharan sun kashe mutane biyu — wato Alhaji Rabiu Faruruwa da Sahabi Dankwaro a yayin harbe-harben da su ka riƙa yi.
Wani mazaunin garin, Abubakar Hamza Adam, ya ce dan uwansa karami, ...








