Saturday, April 11
Shadow
Majalisar Kula Da sarautun Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II

Majalisar Kula Da sarautun Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II

Duk Labarai
Majalisar Kula Da Cibiyoyin Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II Ƙungiyar ta yi nuni da cewa tuni rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan lamarin, wanda hakan ya sa gayyatar ‘yan sandan bai zama dole ba. Ƙungiyar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun ko-odinetan ta na ƙasa Alhaji Yahaya Nda Musa, ta bayyana mamakin gayyatar da ‘yan sandan suka yi mai dauke da kwanan watan Afrilu 4, 2025, mai ɗauke da sa hannun kwamishinan ‘yan sanda Olajide Rufus Ibitoye, a madadin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da sashen leken asiri na rundunar. “Muna da ra’ayin cewa wannan gayyata da babbar hukumar ‘yan sanda ta yi wa Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu cin mutunci ne ga cibiyarmu ta gargajiya, ...
Ana zargin Jami’an tsaro na shirin farmakar muhallan Mabiya Shi’a

Ana zargin Jami’an tsaro na shirin farmakar muhallan Mabiya Shi’a

Duk Labarai
A wani rahoto da jaridar Sahara Reporters ta ruwaito ya nuna cewar, ana zargin gamayyar jami'an tsaron Nijeriya suna shirin kai mummunan hari wasu gurare guda biyar cikin muhallan yan Harkar Musulunci kamar yanda majiyar ta bayyana. Majiyar ta kuma shaida ma jaridar Sahara Reporters yadda Gamayyar jami'an tsaron suke ta tattaunawa da sauran jami'an a karkashin kasa, suna faɗa musu su kwana cikin shiri domin gudanar da aikin da zasu yi a cikin daren Litinin da misalin karfe 2 na daren nan. A makon data gabata ne dai aka yi jana'izar wasu cikin mutanen da sojoji suka kashe masu gudanar da jerin gwano kan lamarin Palasɗinu. Sama da mutane dari uku ne ake tsare dasu a gidajen yarin Kuje dake Abuja da kuma Suleja, wasu kuma suna hannun yan sanda kamar yanda Lauyoyin Harkar Musuluncin s...
Labari Mai Daɗin Ji; Shugaba Tinubu ya amince da samar da sabbin ƙananan asibitoci dubu 8,800 ko’ina a faɗin Nijeriya

Labari Mai Daɗin Ji; Shugaba Tinubu ya amince da samar da sabbin ƙananan asibitoci dubu 8,800 ko’ina a faɗin Nijeriya

Duk Labarai
Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar sa sabbin asibitocin sha-ka-tafi guda dubu 8,800 a fadin kasar nan da kuma inganta manyan asibitoci da ake da su don magance cutukan damuwa da cutuka masu yaɗuwa. Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yau Asabar a lokacin da ya kaddamar da cibiyar kula da cutar damuwa ta Sulaiman Adebola Adegunwa a garin Sagamu na jihar Ogun. Mataimakin shugaban kasar, a wajen taron, ya yi kira da a kara samar da asibitoci masu zaman kan su a wani ɓangare na sauye-sauyen da gwamnatin ke yi a fannin kiwon lafiya da ci gaban kiwon lafiya a fadin Najeriya. Ya jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na magance matsalolin da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya ta hanyar dabarun hadin gwiwa da zuba jari, yana mai cewa bude asibitoci masu z...
Kamfanonin sufurin maniyyatan Najeriya sun janye daga aikin hajjin bana

Kamfanonin sufurin maniyyatan Najeriya sun janye daga aikin hajjin bana

Duk Labarai
A Najeriya, wasu kamfanonin sufurin hajji da umarah na Najeriya sun bayyana janyewarsu daga hada-hadar aikin hajjin bana, saboda yadda suka ce hukumar alhazan Najeriyar tana gudanar da wasu ayyuka da kamfanonin ya kamata su riƙa aiwatarwa. Malam Haruna Isma'il shugaban ɗaya daga cikin kamfanonin uku, ya ce sun kwashe tsawon shekara uku suna neman a yi gyara, amma ba a yi komai ba. Malam Haruna Isma'il shugaban kamfanin harkar sufurin hajji da umarah na Annur Air Services ya karan-tsaye da wuce gona da iri da acewarsa suke cutar da alhazai da masu harkar jigilar ne suka sa suka yanke shawarar janyewa daga aikin. Mun dai nemi jin ta bakin jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar alhazai ta Najeriya, wadda ta yi alƙawarin aiko mana da nasu martanin kan wannan batu, amma har ya zuwa yanzu b...
An kashe ƴan China biyu a jihar Abia

An kashe ƴan China biyu a jihar Abia

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan jihar Abia da ke kudu maso kudancin Najeriya ta tabbatar da kashe wasu ƴan ƙasar China guda biyu da wani ɗansanda mai ba su kariya. Rundunar ta ce ƴansanda sun ɗauki ne bayan rundunar ta samu kiran kar-ta-kwana cewa wasu gungun mahara sun kai wa ƴan Chinan da ƴansanda da ke rakiya hari a hanyarsu ta zuwa kamfaninsu da ke titin Agukwu-Amaya a garin Ndundu a ƙaramar hukumar Isuikwuato na jihar. A wata sanarwa da tashar Channels ta ruwaito daga kakakin rundunar ƴansandan jihar, Maureen Chinaka yana cewa an kashe Mista Quan wanda shi ne manajan kamfanin da Mista Cai abokin aikinsa da Insfekta Audu Saidu. Rundunar ta ƙara da cewa jami'anta sun samu nasarar ceto wasu ƴan China huɗu da ƴansanda guda biyu. A sanarwar, kwamishinan yansandan jihar, Danladi Is...
Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga uku a Taraba

Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga uku a Taraba

Duk Labarai
Sojojin Najeriya masu aiki na musamman na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun sanar da kashe ƴanbindiga uku, sannan suka lalata mazauninsu tare da ƙwace makamai a ƙaramar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba. Sojojin sun samu nasarar ce a ranar 5 ga Afrilu, kamar yadda kakakin sashen Olubodunde Oni ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta ƙara da cewa da sojojin suka isa yankin Chibi, sai ƴanbindigar suka fara tserewa, "inda sojojin suka bi sahunsu suka yi musayar wuta, inda dakarunmu suka kashe ƴanbindigar guda uku, sannan suka tarwatsa mazauninsu, tare da ƙwato makamai." Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin na Najeriya sun yi sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle a kwanakin baya, inda suka tarwatsa mazaunan ƴanbindiga da dama.
Akwai rashin hankali a kashe-kashen jihar Filato – Gwamnonin arewa

Akwai rashin hankali a kashe-kashen jihar Filato – Gwamnonin arewa

Duk Labarai
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi Allah wadai da kashe-kashen da wasu mahara suka yi a garuruwan Ruwi da Manguna da Daffo da Josho da Hunti da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato, inda ta bayyana kisan da na rashin hankali. Shugaban ƙungiyar, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka, inda ya ce harin - wanda ya ci rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu ciki har da mata da ƙananan yara - yana bazarana ga zaman lafiya da ci gaban yankin arewacin ƙasar. A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya ce, "rayuwar ɗan'adam na da daraja da ta wuce a wulaƙanci," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Gwamna Inuwa ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang bisa matakan da ya ɗa...
Duk wanda ke samun Naira Dubu daya da dari biyar(1,500) A Najeriya a kullun ba karamin me sa’a bane>>Gwamnatin Tinubu

Duk wanda ke samun Naira Dubu daya da dari biyar(1,500) A Najeriya a kullun ba karamin me sa’a bane>>Gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Dala 10 ba za ta siya maka abinci a Amurka ba, amma $1 za ta baka abinci a Najeriya – Tope Fasua, in ji hadimin Tinubu Dr. Tope Fasua, Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, ya bayyana rikice-rikicen da ke tattare da auna talauci, yayin da yake kare darajar Naira a cikin gida, inda ya kwatanta tsadar rayuwa a Najeriya da ta Amurka. Yayin da yake magana a cikin shirin MicOnPodcast tare da Seun Okinbaloye, Fasua ya bayyana cewa mutane da dama a Najeriya ba su fahimci ma’anar talauci mai fuskoki da dama ba, wanda ake yawan amfani da shi a cikin kididdigar talauci ta duniya. “Wasu mutane ba su fahimci ma’anar talauci mai fuskoki da dama ba,” in ji shi. “Suna ganin kamar yana da muni fiye da talauci na rashin abinci. Abin da ake nufi da talau...
TIRKASHI KALLI BIDIYO: Yan Kaduna Sun Yiwa Bilal Villah Ruwan Duwatsu, Lokacin da yaje gabatar da wasan sallah

TIRKASHI KALLI BIDIYO: Yan Kaduna Sun Yiwa Bilal Villah Ruwan Duwatsu, Lokacin da yaje gabatar da wasan sallah

Duk Labarai
Matashin Mawaki Bilal Villa Ya Sha Ruwan Duwatsu A Kaduna A Yayin Wasan Sallah, Inda Aka Farfasa Masa Mota, Yayin Da Shi Ma Takwaransa, Ngulde Ya Hadu Da Fushin Katsinawa Inda Suka Rotse Masa Kai Da Dutśe A Yayin Wasan Sallah A yayin da ba a san dalilin da ya sa aka fatatti Bilal Villa a Kaduna ba, amma wata majiya ta gano cewa shi Ngulde ya tabo Katsinawa ne, inda a wata ziyarar da ya kai Katisna, yana sauka sai ya bankawa sigari wuta, wanda hakan yana nufin al'adar su ce shan sigari. Kalli Bidiyon anan Kalli Bidiyo anan Kalli Bidiyo anan