Da Duminsa: Masana Kimiyya sun ce wani mulmulen wuta daga Rana zai fado Duniya gobe kuma zai iya haddasa daukewar wutar lantarki da sabis din waya
Masana kimiyya sun ce an samu wani tarnaki da fashewa a jikin rana.
Sun ce nan da gobe, 16 ga watan Mayu ake sa ran burbushin fashewar zai iya fadowa Duniya.
Masanan sun ce kuma hakan zai iya haifar da daukewar wutar Lantarki da sabis dun waya.








