Wannan wani dan shekaru 50 ne da aka kama bisa zargin baiwa 'yan Bindiga bayanan sirri a jihar Katsina.
Ya amsa laifinsa.
https://twitter.com/ZagazOlaMakama/status/1922753828597764387?t=S7oXlZgDtTseqTaAGozfEw&s=19
Allah ya kyauta.
Dan gidan Gwamnan jihar Anambra, Ya dauki hankula bayan da aka ganshi da baturiya budurwarsa suna shakatawa a kasar Waje.
Bidiyon ya dauki hankula inda akai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi daban-daban.
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1922988630781390911?t=b7NoSvFKsAxNgW8JJHEdGQ&s=19
Badai a bayyana a wace kasa ce yake ba.
Dan majalisar Wakilai daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa ya nemi a baiwa 'yan Najeriya dama su rike makamai dan baiwa Kansu Kariya.
Ya bayyana hakane a farfajiyar majalisar Wakilai inda yace idan jami'an tsaro sun kasa, kamata yayi a baiwa 'yan Najeriya damar kare kansu.
https://twitter.com/General_Somto/status/1922760426145620359?t=W744pEzgJuQRYfcSdcw8pg&s=19
A baya dai Tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung da Lauya dan fafutuka, Deji Adeyanju, da Janar T.Y Danjuma duk sun nemi a baiwa 'yan Najeriya damar daukar Makamai dan kare kansu
Hankula sun tashi a jihohin Ogun da Legas saboda farfagandar yaduwar shinkafa me guba dake kisa.
'Yan uwa da dangi sun rika aikawa jina sakonni musamman ta WhatsApp inda ake gargadinsu da cin shinkafa, ana yada cewa, wata mata ce 'yar kasuwa aka kwacewa Shinkafar aka shigo da ita Najeriya inda ita kuma ta yi tsafi kan duk wanda ya ci ya mutu.
Rahoton yace masu yada wannan labari sunce har wasu sojoji da jami'an Kwastam sun rasu sanadiyyar wannan shinakafa, kamar yanda Punchng ta ruwaito.
Hakanan rahoton yayi ikirarin cewa, Mutane 70 sun mutu sanadiyyar shinkafar.
Iyaye har makaranta sun rika bin 'ya'yansu suna gargadin masu abinci kada su sayarwa da 'ya'yansu Abinci.
Saidai Tunu hukumomin Kwastam na jihohin Ogun da Legas suka musanta wannan zargi.
Sun ce babu wata shinka...
Majalisar tarayya za ta yi bincike kan matsalolin da aka samu a JAMB ta bana
Majalisar Wakilai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan kuskuren fasaha da ya shafi sakamakon Jarrabawar UTME na shekarar 2025.
Majalisar ta amince da wannan kuduri ne a zaman ta na ranar Alhamis, bayan ta amince da kudurin gaggawa mai muhimmancin jama’a da dan majalisa daga jihar Osun, Adewale Adebayo, ya gabatar.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC reshen Kaduna ta samu nasara bayan da kotu ta yanke hukunci ga wani a mai amfani da shafukan Tiktok da Instagram, Muhammad Kabir.
An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban Mai Shari’a R.M. Aikawa na Babban Kotun Tarayya dake zamanta a Kaduna, bisa laifin wulakanta kudin Naira.
Shugaban sashen hulda da jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa an kama Kabir ne a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 a Tudun Wada, jihar Kaduna, bayan ya wallafa wani bidiyo a shafukansa na Tiktok da Instagram (@youngcee0066), yana watsar da takardun kudi na Naira a ƙasa, yana taka su da kafa, tare da furta wasu kalmomi cikin harshen Hausa yana kalubalantar EFCC da ta zo ta kama shi a inda aka san yana zaune.
An kama shi bisa karya dokar Babban Bankin Najer...
Majalisar wakilai na son a maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya
Wani ƙudiri da ke neman maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.
Ƙudurin, wanda shugaban majalisar, Tajuddeen Abbas ya ɗauki nauyi, ya tsallake karatu na biyu bayan an yi wata zazzafar muhawara a zauren majalisar a yau Alhamis.
Gwamnatin Najeria ta bayyana cewa za ta ƙaddamar da tauraron ɗan'adam guda huɗu da za su taimaka wajen lura da yanayin ƙasa da kuma yaƙi da matsalolin tsaro da ake fama da su.
Wadannan taurarin dan'adam ɗin za a yi amfani da su wajen nazarin dazuka da kai kawon jama’a da kuma wadda za ta ɗauko hotunan tekuna da tsaunuka da kuma gano sauran ma’adinai.
Ministan sadarwa da fasahar zamani na ƙasar Uche Nnaji ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron majalisar zartaswa ta ƙasa da ya shafi kirkira da fasahohin zamani karo na ashirin da biyu, wanda ya gudana a babban birnin ƙasar Abuja.
Gwamnatin dai ta ce za ta ƙaddamar da waɗannan taurarin ɗan'adam ne domin gudanar da muhimman ayyukan da suka shafi saka ido a kan yankuna da wuraren da ke fama da matsalar tsaro da kuma ɗaukar muhimman ho...
An ga wadannan hotunan a sararin samaniyar kasar Greece.
Da farko idan mutum ya kalla, zai yi tsammanin AI ne, amma kafofin yada labarai da yawa irin su Beauty of Planet Earth dake wallafa labarai da hotunan ababen kayatarwa a Duniya sun tabbatar da faruwar lamarin.
Saidai masana kimiyya sunce wannan ba wani abin tashin Hankalo bane, tana iya yiyuwar tauraron dan Adam ne rana ta haskashi shine hasken ya hasko cikin Duniya.
lamarin ya farune ranar 14 ga watan Mayu.
Bidiyon matan Larabawa babu Hijabi babu dankwali akansu ya jawo cece-kuce sosai a yayin da aka gansu suna tarbar shugaban kasar Amurka, Donald Trump a kasar UAE.
Matan dai dake da dogayen Gashi sun rika wasa da gashin a gaban Shugaba Trump.
https://twitter.com/MargoMartin47/status/1922995639455044017?t=PJ0FlItXLf_841VVjSttDg&s=19
Lamarin ya bayar da mamaki kasancewar kasar Musulunci ce ya je kuma kasar Larabawa.