Saturday, April 11
Shadow
DOLE MU YI JINJINA A GARE SU: Sun Biya Dukkan Bashin Da Ake Bin Marigayi Sheik Idris Da Kudin Aljihunsu

DOLE MU YI JINJINA A GARE SU: Sun Biya Dukkan Bashin Da Ake Bin Marigayi Sheik Idris Da Kudin Aljihunsu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Daga Datti Assalafiy Lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya zare ran babban Malamin Tauhidi na Afirka Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi, wadannan manyan Malamai wato Sheikh Dr Ibrahim Disina da Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum suna samun labari suka taho gidan Malam. Sannan sukace a tattaro musu list na mutanen da suke bin Malam bashi zasu biya daga aljihunsu, basa bukatar a biya bashin da kudin Malam. Wallahi wadannan Malamai basu bari an yiwa Malam Sallar jana'iza ba sai da...
Bankin Duniya ya baiwa Najeriya kyautar Dala Miliyan $10.5

Bankin Duniya ya baiwa Najeriya kyautar Dala Miliyan $10.5

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Bankin Duniya ya baiwa Najeriya kyautar Dala Miliyan $10.5. Bankin ya bayar da kyautar ne dan amfani da gudin wajan inganta ayyukan babban bankin Najeriya, CBN dan ya karfafa bangaren fasahar zamani. A baya dai an bayyana wadannan kudade a matsayin bashi ga Najeriya. Saidai binciken jaridar Punchng ya tabbatar da cewa kudin kyautane kamar yanda wata majiya daga bankin Duniyar ta gayawa jaridar.
Hukumar ‘Yansandan Najeriya sun yi magana kan Zàngà-Zàngàr da ake shirin yi gobe ta Adawa da wasu tsare-tsaren gwamnatin Tinubu

Hukumar ‘Yansandan Najeriya sun yi magana kan Zàngà-Zàngàr da ake shirin yi gobe ta Adawa da wasu tsare-tsaren gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Hukumar 'yansanda a jihar Legas sun fitar da sanarwa game da zanga-zangar da ake shirin yi gobe a fadin Najeriya. Hukumar 'yansandan ta gargadi masu zanga-zangar kada wajan gudanar da zanga-zangar su rika hayewa 'yansanda suna cin zarafinsu. Kungiyar TIB da wasu kungiyoyin ne suka shirya wannan zanga-zangar inda suka ce suna so ne a soke dokar saka ido a kafafen sada zumunta da yanar gizo da kuma janye dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara. Saidai a sanarwar da hukumar 'yansandan jihar Legas din ta fitar ta bakin kakakinta wadda DCP Tijani O. Fatai ya sakawa hannu, yace sun lura da cewa, ana amfani da wahalar da ake ciki wajan jawo mutane su fito zanga-zangar. Ya bayyana cewa, zasu saka mutanensu a gurare daban-daban na fadin j...
Tsohuwar Ministar Jin Kai, Betta Edu da aka sauke saboda zargin karkatar da kudin Talakawa ta samu kyautar girmamawa a jami’ar Calabar

Tsohuwar Ministar Jin Kai, Betta Edu da aka sauke saboda zargin karkatar da kudin Talakawa ta samu kyautar girmamawa a jami’ar Calabar

Duk Labarai
Tsohuwar minister Jin kai, Betta Edu wadda aka sauke saboda zargin karkatar da kudaden talakawa ta bayyana a wajan bikin cika shekaru 50 da kafuwar jami'ar Calabar dake jihar Cross-River. Wani abin mamaki shine har kyautar karramawa aka baiwa ministar. Da yawa sun yi mamakin ganin Ministar a bainar jama'a tana ta sha'aninta. Kyautar da aka bata itace ta tallafawa al'umma da ta yi. Daga cikin zarge-zargen kudaden da akawa ministar a baya sun hada da na Naira Miliyan N585 da kuma na Dala $640,000. A baya dai tsohuwar ministar ta kuma shiryawa Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero shan ruwa a gidanta.
Yansanda Sun Cafke Jami’insu Da Ya yi Barazanar Ramuwar Gayya Kan Kìsàn Mafarauta a Edo

Yansanda Sun Cafke Jami’insu Da Ya yi Barazanar Ramuwar Gayya Kan Kìsàn Mafarauta a Edo

Duk Labarai
‘ Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta cafke Hadaina Dan-taki, wanda ya yi barazanar kai hari ga ‘yan kudu a Arewa, domin daukar fansa kan mafarauta 16 da aka kashe a Uromi, jihar Edo. Hakan ya biyo bayan cece-kucen da jama’a suka yi akan jami'an bayan wallafa sakon barazanar a shafinsa na Facebook. Idan zamu iya tunawa dai dan sandan ya yi barazanar kai harin ramuwar gayya ga 'yan kudancin Najeriya da ke zaune a arewacin Najeriya. Kalaman Dan-Taki na zuwa ne a matsayin martani ga kashe ‘yan Arewa 16 da aka yi a garin Uromi dake Jihar Edo. A wani zazzafan tsokaci da ya yi a Facebook ranar Talata, Dan-Taki ya rantse da Allah sai ya rama kisan da aka yiwa al'ummar Arewa, yana mai shan alwashin cewa ‘yan Arewa za su dauki kwakkwaran mataki kan ‘yan Kudu a nan gaba kaɗan. ...
Al’ummar Kano Sun Zargi ‘Yansanda Da Yunƙurin Sanya Dokar Ta-baci Kan Gayyatar Sarki Sunusi

Al’ummar Kano Sun Zargi ‘Yansanda Da Yunƙurin Sanya Dokar Ta-baci Kan Gayyatar Sarki Sunusi

Duk Labarai
Al'umma Jihar Kano sun yi ikirarin cewa gayyatar da babban Sifetan 'yansanda ya yi wa Sarki Sanusi wani bangare na shirin kafa dokar ta-baci a Jihar. Hakan na zuwa ne biyo bayan rahotannin da ke cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a hukumance, zuwa ofishin ta dake Abuja domin bincike kan wani yamutsu da aka samu a lokacin bukukuwan Sallah. Wasu ‘yan jihar da suka yi magana kan kama Usman Sagiru dan shekara 20 a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025 da ke Sharifai Quarters dangane da zargin kisan wani dan banga a tawagar Sarki Sanusi Lamido Sanusi na biyu bayan Sallar Idi, sun bayyana cewa ba za su iya alakanta lamarin da gayyatar Sarki ba. Takardar gayyata mai kwanan wata 4 ga Afrilu, 2025, kuma mai dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ib...
Kalli Yanda Zanga-zangar “Takalmin Annabi ya fi kowa” ta barke a Katsina

Kalli Yanda Zanga-zangar “Takalmin Annabi ya fi kowa” ta barke a Katsina

Duk Labarai
Daga Auwal Isa Musa Kamar yadda wakilin Jaridar Taskar Labarai taskar labarai ya aiko mana, cincirindon jama'a ne suka yi farin-dango wajen fitowa tare da bazama a kan manyan Titunan birnin Katsina da hantsin yau Asabar, domin gudanar da zanga-zanga maintaken "Takalmin Annabi ya fi kowa" Bangarorin al'ummar musulmi a jihar ta katsina, an shaida shigarsu wannan zanga-zanga wadda yanzu haka take gudana a tsanake, a yain da mahalartanta ke rera wakokin yabo ga fiyayyen halitta, musamman Takalminsa (S) da suka fito zanga-zangar nuna daraja da fifikonsa. Zanga-zangar ta taso ne taso ne daga filin Polo/kofar 'yandaka, inda ta ta nufo cikin gari.
Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed yayin da yaje ta’aziyyar malamin

Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed yayin da yaje ta’aziyyar malamin

Duk Labarai
Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed …Malami ne mara tsoro da ya sadaukar da rayuwarsa wajen karantar da mušùĺùnçìn, wanda jihar Bauchi za ta yi kewarsa …ya ku mallakawa Almajiransa filin game village Daga Rariya A yammacin yau Abasar ne Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheik Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ga iyalansa da mabiyansa, wanda ya rasu a daren Juma'ar da ta gabata. Gwamna Bala wanda ya jagoranci tawagar mukarraban gwamnati, ya kai ziyarar ta'aziyyar ne a madadin kansa, iyalansa, gwamnati da kuma daukacin al'ummar jihar Bauchi. Gwamnan ya bayyana marigayi Shehin Malamin a matsayin malamin mara tsoro wanda ya sadaukar da kansa waj...
Bashin da ake bin Najeriya ya karu sosai

Bashin da ake bin Najeriya ya karu sosai

Duk Labarai
Bashin da ake bin Nijeriya ya haura zuwa tiriliyan N144.67 a 2024 - Rahoton DMO Ofishin kula da basussuka na Nijeriya ya ce bashin da ake bin Najeriya ya karu da naira tiriliyan N47.32tn, wanda ya nuna karuwar kashi 48.58 cikin 100 daga Disamba 2023 zuwa Disamba 2024. Sabon rahoton da aka fitar a wannan Juma’a, ya nuna cewa an samu karuwar cin bashi daga kasashen waje da kuma cikin gida, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
An min Wahayi cewa nan gaba a saman wata da kuke gani a sama zamu je mu yi zaman taro>>Inji Pastor Enoch Adeboye

An min Wahayi cewa nan gaba a saman wata da kuke gani a sama zamu je mu yi zaman taro>>Inji Pastor Enoch Adeboye

Duk Labarai
Babban Malamin kirista, Pastor Enoch Adeboye ya bayyana cewa, an masa wahayi cewa, nan gaba a saman wata za'a je a gudanar da taron cocinsa. Faston ya bayyanawa mabiyansa hakane yayin da yake musu wa'azi. Saidai yace lamarin Allah akwai ban mamaki amma ba lalai bane sai mutane sun yarda ba. Lamarin dai ya baiwa mutane da yawa, ciki hadda kiristoci mamaki.