Sunday, July 26
Shadow
Kalli Bidiyon yanda shugaban jarabawar JAMB ya fashe da kuka saboda kuskuren hukumar yasa dalibai da yawa sun fadi jarabawar

Kalli Bidiyon yanda shugaban jarabawar JAMB ya fashe da kuka saboda kuskuren hukumar yasa dalibai da yawa sun fadi jarabawar

Duk Labarai
An gano cewa, Kuskuren hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami'a ta JAMB yasa dalibai da yawa sun fadi jarabawar. Akalla Dalibai Miliyan 1.5 ne suka ci kasa da makin da ake bukata a jarabawar ta bana wadda ake ganin sun yi yawa. A yayin taron manema labarai dan bayyana dalilin da yasa aka samu wannan tangarda, shugaban hukumar ta JAMB, Professor Ishaq Oloyede ya fashe da kuka. https://twitter.com/ARISEtv/status/1922676757787766804?t=LRtY04XWaym5mjx3aoC7Ug&s=19 Ya dai bayar da hakuri sannan kuma ya sha Alwashin sakewa dalibai da yawa jarabawar. Yankin da aka samu wannan matsaloli na jihar Legas ne da kudu maso kudu.
Kalli Bidiyo: Dangote na daya daga cikin wadanda suka gaisa da shugaban Amurka, Donald Trump a kasar Qatar

Kalli Bidiyo: Dangote na daya daga cikin wadanda suka gaisa da shugaban Amurka, Donald Trump a kasar Qatar

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote na daya daga cikin wadanda suka gaisa da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yin ziyarar da ya kai kasar Qatar. Shugaba Trump ya kao ziyara kasar Qatar bayan kammala ziyara a kasar Amurka. https://twitter.com/thecableng/status/1922724222867996726?t=ELlWm2kvK9sQIMxkMnfH5g&s=19 Kasar Qatar dai ta baiwa shugaba Trump kyautar jirgin sama Kirar Boeing.
DATTIJUWA TA SAUKE KUR’ANI: Allah Ya Sa A Amfana Da Abinda Aka Karanta Baaba!

DATTIJUWA TA SAUKE KUR’ANI: Allah Ya Sa A Amfana Da Abinda Aka Karanta Baaba!

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} DATTIJUWA TA SAUKE KUR'ANI: Allah Ya Sa A Amfana Da Abinda Aka Karanta Baaba!
Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci

Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci

Duk Labarai
Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci. Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage ranar yanke hukunci kan shahararriyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, har zuwa ranar 20 ga watan Mayu, bayan da masu gabatar da kara su ka nemi izini don gyara tuhumar da a ke yi mata. Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa hukumar EFCC ce ta gurfanar da Murja da tuhuma daya tak kan zargin cin zarafin Naira. An ga Murja a wani faifen bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta tana watsar da kudi har Naira 400,000 tare da rawa a lokacin wani biki da aka gudanar a otal din Tahir Guest Palace a watan Disamba na shekarar 2024. Tuni dai wanda ake tuhumar ta amsa laifin da ake zarginta da shi. A zaman kotun na ranar Talata da aka tsara domin yanke hukunci, lauyan EFCC...
Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na’ura

Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na’ura

Duk Labarai
Ɗalibai 379,997 za su sake zana UTME ta bana bayan da JAMB ta tabbatar da an samu tangarɗar na'ura. Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta amince da kuskuren na'ura da ya kawo cikas ga sahihancin sakamakon jarabawar da aka yi ta bana a cibiyoyi 157 a fadin kasar nan. Shugaban hukumar ta JAMB, Ishaq Oloyede, yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Laraba, ya ce sakamakon ɗalibai 379,997 abin ya shafa. Ya ce hukumar ta gano matsalolin a cibiyar a Legas da Owerri, wanda hakan ya sa aka kasa dora amsoshin ɗaliban da abin ya shafa a kwanaki ukun farko na jarabawar. Oloyede ya ce ba gano matsalar da daya daga cikin kamfanonin da ke bada na'urar yin jarrabawar ya haifar ba kafin a fitar da sakamakon. Ya ce cibiyoyi 65 a Legas ɗalibai...
Mun shaida tsare-tsaren shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu na aiki yanda ya kamata, sun kawowa Najeriya ci gaba>>Inji Kasar Ingila

Mun shaida tsare-tsaren shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu na aiki yanda ya kamata, sun kawowa Najeriya ci gaba>>Inji Kasar Ingila

Duk Labarai
Gwamnatin Birtaniya ta ce matakan da shugaban Najeriya bola Ahmed Tinubu ke ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar kwalliya na biyan kuɗin sabulu. Birtaniyan ta ce matakan da aka ɗauka musamman wajen farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, da na kuɗin shiga na daga cikin dalilan da suka aka samu ƙaruwar damar zuba jari a ƙasar. Jakadan Birtaniya a Najeriya Dr. Richard Montgomery ne ya sanar da hakan a yayin wani taro na aiwatar da shirin bunƙasa tattalin arzikin Najeirya da Birtaniya, ta fuskar kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu, da ya gudana a Abuja babban birnin na Najeriya. Gwamnatin Birtaniyar ta ce la’akari da rahoton da Bankin Duniya a baya-bayan nan kan harkokin zuba jari a Najeriya ya nuna cewar darajar kuɗin ƙasar naira na farfaɗowa. Haka kuma rahoton ya ce ana sam...
Ba za mu bari PDP ta nutse da mu ba – Sanatocin Kebbi

Ba za mu bari PDP ta nutse da mu ba – Sanatocin Kebbi

Duk Labarai
Sanatocin Najeriya uku da suka fito daga jihar Kebbi, waɗanda suka sauya sheƙa daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki sun ce sun fita daga jam'iyyar ce sanadiyyar rikice-rikice na cikin gida. A jiya Talata ne shugabancin majalisar dattajai ya tabbatar da sauya shekar sanatocin wato Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta tsakiya da Yahaya Abdullahi mai wakilartar Kebbi arewa da kuma Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta kudu. Sanatocin sun ce sun fice daga jam'iyyar ne saboda rikice rikicen cikin gida da suka yi wa jam'iyyar PDP katutu. Daya daga cikinsu, Sanata Yahaya Abdullahi ya shaida wa BBC cewa a bayyane take tun bayan zaɓen 2023, jam'iyyar PDP ta shiga ruɗani da rikici kala-kala, kuma har kawo yanzu babu alamun jam'iyyar tana ɗaukar matakin gyara matsalolin n...
Jimullar Sojoji 100 da farar hula 200 ne masu ikirarin Jìhàdì suka kàshè a cikin sati 5 da suka gabata

Jimullar Sojoji 100 da farar hula 200 ne masu ikirarin Jìhàdì suka kàshè a cikin sati 5 da suka gabata

Duk Labarai
Wata kungiya me saka ido kan ayyukan masu ikirarin Jìhàdì me suna Nextier SPD ta bayyana cewa sojojin Najeriya 100 ne da farar hula 200 aka kashe a hare-haren masu ikirarin Jìhàdì cikin makonni 5 da suka gabata. Kungiyar a sabon rahoton data wallafa tace akwai bukatar a sake duba ga tsarin yakar ta'addanci a Najeriya da ake dashi a yanzu. Rahoton kungiyar yace an kai hare-hare 252 na ta'addanci a cikin watanni 6 da suka gabata sannan kungiyoyin B0K0 Hàràm da ÌŚWÀP sun kwace kananan hukumomi 3 a jihar Borno. Kungiyar ta yi gargadin cewa ana samun karin sanyin gwiwa a tsakanin sojoji hakanan alaka tsakanin jama'ar gari da sojoji na kara yin tsami, sannan kuma hakan na nufin lamarin na iya kara kazancewa nan gaba. Kungiyar tace rashin samun ilimi da rashin aikin yi tsakanin matas...