Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed yayin da yaje ta’aziyyar malamin
Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed
…Malami ne mara tsoro da ya sadaukar da rayuwarsa wajen karantar da mušùĺùnçìn, wanda jihar Bauchi za ta yi kewarsa
…ya ku mallakawa Almajiransa filin game village
Daga Rariya
A yammacin yau Abasar ne Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheik Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ga iyalansa da mabiyansa, wanda ya rasu a daren Juma'ar da ta gabata.
Gwamna Bala wanda ya jagoranci tawagar mukarraban gwamnati, ya kai ziyarar ta'aziyyar ne a madadin kansa, iyalansa, gwamnati da kuma daukacin al'ummar jihar Bauchi.
Gwamnan ya bayyana marigayi Shehin Malamin a matsayin malamin mara tsoro wanda ya sadaukar da kansa waj...








