Sunday, April 12
Shadow
A yanzu Kotu ta amince a yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye

A yanzu Kotu ta amince a yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Lokoja ta amince a shiryawa sanata Natasha Akpoti kiranye. Kotun tace mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti suna da 'yancin yi mata kiranye kamar yanda kundin tsarin mulki ya basu dama. Kotun tace mutanen mazabar zasu iya ci gaba da gudanar da zaben kiranyen da suke shiryawa Sanata Natasha Akpoti amma su bi doka da oda wajan yin hakan. Kotun ta bayyana hakane bayan da a ranar Alhamis tace a dakata da maganar yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye.
Dakatar da gwamnan Rivers ɓata sunan Najeriya ne a idon duniya — Jonathan

Dakatar da gwamnan Rivers ɓata sunan Najeriya ne a idon duniya — Jonathan

Duk Labarai
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya soki dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakiyarsa da ƴanmajalisar dokokin jihar, wanda shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi. Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na cire zaɓaɓɓun shugabanni. "Wannan matakin da aka ɗauki zai ɓata sunan Najeriya ne a idon duniya," in ji shi, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito. Jonathan ya ce duk da cewar akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su magance rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers na tsawon lokaci, a cewarsa dakatar da waɗanda mutane suka zaɓa a matsayin shugabanninsu bai dace ba. Ya ƙara da cewa ya san bai kamata a matsa...
Dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ba ta fara biyan kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ba – ALGON

Dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ba ta fara biyan kananan hukumomi kudadensu kai tsaye ba – ALGON

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya ba ta fara bayar da kudaden kasafi kai tsaye ga Kananan Hukumomi ba saboda ana ci gaba da bin wasu hanyoyin aiki, in ji Kungiyar Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON). Shugaban kwamitin amintattu na ALGON, Odunayo Alegbere, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja bayan wani taron kungiyar. Ya bayyana cewa an umarci kananan hukumomi da su bude asusu a Babban Bankin Najeriya (CBN) domin saukaka aiwatar da tsarin rabon kudade kai tsaye. Duk da cewa har yanzu ba a kammala tsarin ba, Alegbere ya jinjinawa Gwamnatin Tarayya kan ci gaban da aka samu, yana mai cewa hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi babbar nasara ce. Ya jaddada cewa gwamnati na aiki don aiwatar da wannan hukunci, wanda ya hada da ‘yancin gudanarwa da kuma ‘yancin siyasa...
Dalilan da ya sa mata ke rububin rigar mama ta gwanjo a Legas

Dalilan da ya sa mata ke rububin rigar mama ta gwanjo a Legas

Duk Labarai
Bukatar rigar mama ta ganjo a wajen matan Legas na Karuwa, inda hakan ya kasance abin dubawa a jihar, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito. Wasu mata da jaridar ta zanta da su sun nuna cewa zaɓinsu na rigar mama ya dogara ne kan dalilai kamar araha da kuma ƙarko. Da yawan matan Legas na sayen rigar mama ta gwanjo, wacce aka fi sani da "Okrika" saboda suna samuwa da yawa, ga araha, kuma su na da kyau. Vanguard ta gano cewa baya ga manyan kasuwanni kamar Tejuosho, Balogun, da Katangowa a Legas, ana iya samun rigar mama na Okrika a ƙananan kasuwanni, shaguna, da wuraren masu sayar da kaya a gefen hanya. Mrs Peace Okeke, wadda ake kira "Lady Bra" a tsakanin kwastomominta a Festac Town, yankin Amuwo Odofin, ta ce ta kwashe fiye da shekaru 18 ta na wannan sana'a. A cewarta, tun...
An yi gàrkùwà da soja da wasu sauran mutane a Abuja

An yi gàrkùwà da soja da wasu sauran mutane a Abuja

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa an yi garkuwa da wata sojar ruwa dake aiki a hedikwatar tsaro ta kasa tare da wasu mutane. Lamarin ya farune a Mpape dake Abuja ranar Juma'a inda aka shiga har gida aka tafi da wadanda aka yi garkuwar dasu. Wata majiya ta shaida cewa, wadanda aka yi garkuwa dasu din an kira iyalansu inda ake neman Naira Miliyan 100 a matsayin kudin Fansa. Jimullar mutane 3 ne aka yi garkuwar dasu, ciki hadda sojar me suna Lt. Cynthia Akor. Hukumomin soja dai basu ce uffan kan lamarin ba.
Makiyanane ke wannan karyar: Sanata Akpabio yace bai rabawa sanatoci dala Dubu 5 ba dan su goyi bayan dakatar da gwamnan Rivers ba

Makiyanane ke wannan karyar: Sanata Akpabio yace bai rabawa sanatoci dala Dubu 5 ba dan su goyi bayan dakatar da gwamnan Rivers ba

Duk Labarai
created by photogrid Sanata Godswill Akpabio a kokarin kare kansa daga zargin da ake masa na raba dala dubu 5 da dubu 10 ga wasu sanatoci dan su goyi bayan dakatar da gwamnan jihar Rivers yace makiyansa ne ke yada wannan maganar. An dai yi zargin cewa, Sanata Godswill Akpabio ya kira sanatocin zuwa shan ruwa a gidansa inda a canne ake zargin ya raba musu kudaden. Saidai a martani ta bakin kakakinsa, Hon. Eseme Eyiboh yace makiya ne ke yada wannan jita-jitar. Yace dama can al'adace ta Sanata Godswill Akpabio ya shiryawa sanatoci shan ruwa duk shekara, shekarar data gabata yayi a wannan shekarar ma yayi. Amma maganar raba daloli babu ta. An dai zargi cewa ministan Abuja, Nyesome Wike ne ya kaiwa Sanata Godswill Akpabio Dala Miliyan $3 dan ya rabawa sanatocin.
Kalli Bidiyon yanda ‘yan daba suka ķķàśhè matashi a yayin Sallar Tahajjud a Unguwar Rigasa jihar Kaduna

Kalli Bidiyon yanda ‘yan daba suka ķķàśhè matashi a yayin Sallar Tahajjud a Unguwar Rigasa jihar Kaduna

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} 'Yan daba sun kai hari a unguwar Rigasa dake jihar Kaduna ranar Juma'a, 21 ga watan Ramadana wanda yayi daidai da ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2025. Kakakin 'yansandan jihar,DSP Mansir Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wani mazaunin unguwar Rigasan ne ya kirasu ya sanar dasu cewa, 'yan daba daga Malalin Gabas, da Tudun Wada, Rafin Guza, da Unguwar Baduko sun shiga unguwar dan farwa masallata. Yace sun kai harinne Layin Bilya inda matashi dan sa kai da ab...
Kai Duniya: Duk da Azumin watan Ramadana, an kama wani me suna Ridwan Bello ya tono gawar wata mata daga kabari zai sayar

Kai Duniya: Duk da Azumin watan Ramadana, an kama wani me suna Ridwan Bello ya tono gawar wata mata daga kabari zai sayar

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan jihar Oyo sun sanar da kama wasu mutane da suka kware wajan tono gawar matattu bayan an binnesu a makabarta dan yin sihiri. A sanarwar data fitar ranar Talata, 18 ga watan Maris, Hukumar 'yansandan jihar tace ta kai samame gidan wani mutum me suna Ridwan Bello dan shekaru 35 bayan samun bayanan sirri akansa. Tace kuma ta yi sa'a ta iske gangar jikin wata mata babu kai babu kafafu da kasusuwan mutane. Mutumin wanda wasu lokutan ana kiransa da sunan Asalailu ya bayyana amsa laifinsa. Yace yana kaiwa wani matsafine sassan jikin yana saye. Ridwan ya kai 'yansandan har kabarin da ya tono gawar. Sannan ya kaisu gurin mutumin da yake sayarwa da sassan jikin wani me suna Fatai Adeleke dan kimanin shekaru 70. Shima ya amsa laifinsa. Hukumar tace an kaisu bang...