Monday, April 20
Shadow
Doyin Okupe ya hango mutuwarsa tun kamin ta zo, yana sane da cewa ya kusa mutuwa dan ya gaya mana>>Inji Daya daga cikin yaransa

Doyin Okupe ya hango mutuwarsa tun kamin ta zo, yana sane da cewa ya kusa mutuwa dan ya gaya mana>>Inji Daya daga cikin yaransa

Duk Labarai
Daya daga cikn yaran tsohon hadimin shugaban kasa da ya mutu, watau Doyin Okupe ya bayyana cewa, Yasan zai mutu an ya hango mutuwar tasa. Mutumin me suna Jack ya bayyana Doyin Okupe a matsayin uba kuma haziki sannan jajirtaccen mutum. Yace dukan alamu sun nuna cewa ya hango mutuwarsa dan kuwa a shekarar data gabata ya tara na kusa dashi ya shirya musu liyafar cin abincin dare inda yace itace ta karshe.
Labari Me Dadi: Najeriya ta samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan 13.78 daga sayar da Danyen man

Labari Me Dadi: Najeriya ta samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan 13.78 daga sayar da Danyen man

Duk Labarai
Hukumar kididdiga ta kasa, NBS tace Najeriya ta samu kudin ahiga da suka kai Naira Tiriliyan 13.78 daga sayar da danyen man fetur a watanni 3 na karshen shekarar 2024 data gabata. A sanarwar da suka fitar sun ce Najeriya ta kuma samu kudin shiga daga harkokin da ba na man fetur ba da suka kai Naira Tiriliyan 2.8 da kuma Naira Tiriliyan 6.2. !Hakanan hukumar tace har yanzu dai abinda Najeriya ta fi fitarwa dan sayarwa da samun kudin shiga daga kasashen Duniya danyen man fetur ne wanda ke wakiltar kaso 68.87 cikin 100 na kudin shigar gwamnatin.
Duk da an rage farashin Man Fetur, mu ba zamu iya rage farashin daukar mutane ba>>Kungiyar Masu motocin haya

Duk da an rage farashin Man Fetur, mu ba zamu iya rage farashin daukar mutane ba>>Kungiyar Masu motocin haya

Duk Labarai
Kungiyar masu sana'ar tuka motocin haya, (NURTW) ta bayyana cewa, rage farashin Man fetur ba zai sa su rage farashin da suke daukar fasinja ba. Sakataren Kungiyar na jihar Kano, Yushu’a Haruna ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da jaridar Leadership. Ya bayyana cewa, duk da yake an rage farashin man fetur amma ba shi kadai ne suke kashe kudi wajan amfani da mitar ba, yace farashin taya ya karu hakanan farashin motar kanta ba sauka yayi ba. Dan haka yace ba zasu rafe farashin daukar mutane ba. Hakanan Takwaransa na kungiyar NARTO, Ado Inuwa Yakasai shima ya tabbatar da wannan magana inda yace tabbas an rage farashin man fetur amma na sauran kayan mota bai ragu ba. Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur din daga 860 zuwa 825.
Kalli: Sanata Shehu Sani ya sha raddi a wajan Kiristoci inda suka rika tambayarshi kana Azumi kuwa bayan da yayi comment a kasan wani bidiyon da ake nuna tsìràìcì mata Tsìràra suna rawa

Kalli: Sanata Shehu Sani ya sha raddi a wajan Kiristoci inda suka rika tambayarshi kana Azumi kuwa bayan da yayi comment a kasan wani bidiyon da ake nuna tsìràìcì mata Tsìràra suna rawa

Duk Labarai
Sanata shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai a shekarar 2015 zuwa 2019 ya sha raddi a kafar X. An wallafa wani Bidiyo ne inda aka nuna mata tsirara daga su sai dan kamfai a wani shagon Aski da aka ce a Najeriya yake auna rawa. Da yake bayyana ra'ayinsa akan bidiyon, sanata Shehu Sani yace ka zo Najeriya zaka ga abubuwan ban mamaki. Saidai da yawa sun yi mamakin ganin comment dinsa a kasan Bidiyon ganin cewa bidiyon na dauke da tsiraici. Da yawa sun rika tambayar anya Sanata Shehu Sani na Azumin kuwa? Kalli Bidiyon anan:
Wani bawan Allah ya rasu ana tsaka da Sallar Asuba

Wani bawan Allah ya rasu ana tsaka da Sallar Asuba

Duk Labarai
Wani bawan Allah me suna Salihu Byezhe ya rasu ana tsaka da sallar Asuba tare dashi. Lamarin ya farune a kauyen Gudaba dake Kuje a babban birnin tarayya Abuja. Wani mazaunin garin me suna Musa Dantani yace Salihu ya rasu ne a yayin da yake Sallar Asuba a masallacin garin. Yace Salihu ya gama yin Sahur ya tafi masallaci, ana tsaka da sallah ya yanke jiki ya fadi, an garzaya dashi Asibitin Kuje inda acan Likita ya tabbatar da ya rasu. An alakanta rasuwar tashi da hawan jini. An yi jana'izarsa da misalin karfe 10:12 am kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.
Kalli Yanda wani dansanda me bayar da hannu a Titi yake aiki akin bayar da hannin akan Tiktok Live

Kalli Yanda wani dansanda me bayar da hannu a Titi yake aiki akin bayar da hannin akan Tiktok Live

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Wani dansanda dake aikin bayar da hannu a kan titin Akure jihar Ondo ya dauki hankula sosai bayan da aka ga yana aikin amma yana daukar kansa akan Tiktok Live. https://www.youtube.com/watch?v=bXwPneb-YVU?si=NhW7QByz6kFKGsmM Bayan ya bayar da hannu akan jishi yana cewa Taptap alamar masu kallo su aika masa da kyauta.
Kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya, TCN yace ya samar da wuta me karfin da ba’a taba samun kamarta ba a Tarihin Najeriya

Kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya, TCN yace ya samar da wuta me karfin da ba’a taba samun kamarta ba a Tarihin Najeriya

Duk Labarai
Kamfanin samar da wutar Lantarki na kasa, TCN ya bayyana cewa, ya samar da wutar lantarki me karfin 5,801 megawatts wanda a Tarihin Najeriya ba'a taba samun wutar lantarki me karfin hakan ba. Saidai 'yan Najeriya dake amfani da wutar sun musanta wannan ikirari inda suka ce basu gani a kasa ba dan kuwa yankuna da yawa na kasar na kwana cikin duhu. A ranar Alhamis ne dai shugaban hukumar a fadar shugaban kasa dake Abuja ya tabbatar da hakan. Yace sun samu wannan nasara ne a ranar 4 ga watan Maris. Yace kuma rassan kamfanin wutar na jihohi sun tura wutar gaba daya zuwa ga 'yan Najeriya.
EFCC na binciken tsohuwar ministar mata da ta so hana aurar da mata marayu musulmai a jihar Naija da zargin karkatar da naira miliyan 138.4

EFCC na binciken tsohuwar ministar mata da ta so hana aurar da mata marayu musulmai a jihar Naija da zargin karkatar da naira miliyan 138.4

Duk Labarai
Jami'an hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci da Rashawa a Najeriya sun gayyaci tsohuwar ministar matan ƙasar, Uju Kennedy-Ohanenye domin amsa tambayoyi. Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ce hukumar na zargin Ms Kennedy da karkatar da naira miliyan 138.4 cikin kuɗin da aka ware wa ma'aikatar a kasafin kuɗin 2023, da ɓarnatar da kuɗi da kuma saɓa ƙa'ida wajen wasu abubuwa. Hukumar na zargin tsohuwar ministar da karkatar da kuɗin domin amfanin kanta, ciki har da kuɗaɗen da aka ware domin shirin tallafa wa mata na P-BAT. Tsohuwar ministan ta isa harabar hukumar da safiyar ranar Alhamis, domin amsa tambayoyi, kuma bayanai na cewa har yanzu ana ci gaba da yi mata tambayoyin, kamar yadda kafofin ya da labaran ƙasar suka ruwaito. Uju Kennedy-Ohanenye na ɗaya daga cikin ministoci biyar d...
Majalisar wakilan Najeriya na son a ƙwace ikon yi wa jam’iyyu rajista daga wurin INEC

Majalisar wakilan Najeriya na son a ƙwace ikon yi wa jam’iyyu rajista daga wurin INEC

Duk Labarai
Majalisar Wakilan Najeriya ta gabatar da wani ƙudirin da zai ƙwace wa hukumar zaɓen ƙasar ikonta na yi wa jam'iyyun siyasar ƙasar rajista da kula da ƙa'idojin jam'iyyun. ƙudurin - wanda kakakin majalisar wakilan ƙasar Hon.Tajudeen Abbas tare da haɗin gwiwar Hon Marcus onobun daga jihar Edo suka gabatar - ya buƙaci a samar da wata hukuma mai zaman kanta da za ta kula da batun yi wa jam'iyyu rajista da kula da ƙa'idojinsu da ɗaukar nauyin jam'iyyun. Tuni dai ƙudirin ya wuce karatu na biyu a zauren majalisar. Haka kuma ƙudirin ya buƙaci da kafa kotu ta musamman don sauraron ƙorafe-ƙorafen jam'iyyu domin magance rigingimu tsakanin mambobin jam'iyyu. Yayin da yake gabatar da ƙudirin, Hon. Onobun ya ce matakin ya zama wajibi, la'akari da yadda ake yawan samun rigingimun tsakanin jam'...