Monday, April 20
Shadow
Yawanci masu sharhi akan dakatar da sanata Natasha Akpoti jahilaine, kamar wanda ba musulmi bane yace zai fassara Qur’ani>>Sanata Godswill Akpabio

Yawanci masu sharhi akan dakatar da sanata Natasha Akpoti jahilaine, kamar wanda ba musulmi bane yace zai fassara Qur’ani>>Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya gargadi 'yan Najeriya da su daina tsoma baki akan abinda basu da ilimi akansa. Ya jawo hankalin 'yan Najeriya da cewa, su fahimci dokokin majalisar kamin su tsoma baki akan harkokinta. Ya bayyana hakane a yayin da wasu kungiya daga yankinsa na Niger Delta suka kai masa ziyara. Hakan na zuwane a yayin da ake ta bayyana ra'ayoyi mabanbanta game da dambarwarsa da Sanata Natasha Akpoti. Ya bayyana cewa masu sharhi akan al'amuran majalisar ba tare da sanin dokokinsu ba kamar me maganin gargajiyane dake son fassara Baibul ko wanda ba Musulmi ba yayi kokarin fassara Qur'ani. Akpabio yace kujerar da yake kai rabon yankinsu na Niger Delta da samunta tun shekaru 46 da suka gabata yace kuma ba dan shi bane yake kan kujerar, yana ...
Jihar Kebbi ta gano karin ma’adanan karkashin kasa a jihar

Jihar Kebbi ta gano karin ma’adanan karkashin kasa a jihar

Duk Labarai
Jihar Kebbi ta gabo karin ma'adanai na karkashin kasa a jihar. Kwamishinan yada labarai na jihar, Yakubu Ahmed-BK ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Yace an gano karin ma'adanan ne a Jega, Dandi, Gwandu, Suru, Birnin Kebbi, Argungu da sauransu. Wannan na zuwane a yayin da jihar Kebbi ke da ma'adanai kamar su gwal da sauransu. Ya bayyana gano wadannan karin ma'adanai da cewa, wata hanyace ta karin samun kudin shiga ga jihar.
Talauci da rashin tsaro ya karu a Najeriya>>Inji Kungiyar Kiristoci darikar Katolika

Talauci da rashin tsaro ya karu a Najeriya>>Inji Kungiyar Kiristoci darikar Katolika

Duk Labarai
Kungiyar Limaman Kiristoci na darikar Katolika sun bayyana cewa matsalar talauci, rashin aikin yi tsakanin matasa da matsalar tsaro na karuwa a Najeriya. Kungiyar ta bayyana hakane a zaman ta a Abuja ranar Labadi inda ta nemi shugaba Tinubu da ya dauki matakin gyara. Zaman wanda ya samu halartar shugabannin Kungiyar Most Rev. Lucius Ugorji, Archbishop na cocin Owerri da shugaban CBCN, Archbishop Daniel Okoh, da kuma shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Christian Association of Nigeria (CAN); da Most Rev. Ignatius Kaigama, Catholic Archbishop of Abuja ya yi na'am da matakan Gwamnati na gyara amma yace matakan sun yi kadan.
Kasar Amurka ta hana shugaban Kwamitin da’a na Majalisar dattijai da ya dakatar da sanata Natasha Akpoti shiga kasarta saboda cin hanci da rashawa

Kasar Amurka ta hana shugaban Kwamitin da’a na Majalisar dattijai da ya dakatar da sanata Natasha Akpoti shiga kasarta saboda cin hanci da rashawa

Duk Labarai
Shugaban kwamitin da'a na majalisar dattijai Sanata Neda Imasuen wanda shine ya bayar da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti tsawon watanni 6, shi kuma kasar Amurka ta hanashi shiga kasarta saboda zargin rashawa da cin hanci. Yana da kamfanin aikin Lauya, kuma wata mata ta kawo masa aikin ya wakilceta a kotu, saidai maimakon ya wakilceta, bayan da ta biyashi kudin aiki, sai ya tsere da kudin ba tare da ya je ya wakilceta a kotun ba. Hakanan rahoton yace an nemi a bincikeshi amma yaki. Matar me suna Daphne Shyfield a shekarar 2009 ta baiwa Sanata Neda makudan kudade ya wakilceta a kotu amma ya tsere da kudinta kuma yaki wakiltarta a Kotu.
Ku kiyayi kanku da tunanin fita kasar waje ci rani, da yawa da suka je suna cikin nadama>>Gwamnati ta gargadi Matasa

Ku kiyayi kanku da tunanin fita kasar waje ci rani, da yawa da suka je suna cikin nadama>>Gwamnati ta gargadi Matasa

Duk Labarai
Shugabar hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen Ketare, Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewa da yawan 'yan Najeriya da suka je kasar waje ci rani suna cikin halin nadama da dana sani. Ta bayyana hakane ta kafar X inda tace da yawan 'yan Najeriya dake zaune a kasashen na ketare na damun ta da maganar cewa suna cikin nadama da dana sanin fitar da suka yi. Ta mayar da martanine akan ikirarin wani lauya dan Najeriya dake zaune a kasar Ingila inda yake cewa lamarin cirani a kasar ta Ingila ya canja inda da yawa suke cikin nadama da damuwa da danasani. Yace kamin mutum ya sayar da kadararsa ya tafi kasar Ingila ci rani yayi tunani kada kawai dan ya ga wani yayi shima yace zai yi. Yace idan mutum na da aikinsa me kyau, ya rike abinsa kada yace sai ya je ingila. Tace inda ake tafiya c...
Ashe shima Godswill Akpabio ya taba sukar Bukola Saraki bayan da ya canja mai kujerar zama kamar yanda a yanzu fadanshi da Sanata Natasha Akpoti ya samo Asali ne daga canja mata kujera

Ashe shima Godswill Akpabio ya taba sukar Bukola Saraki bayan da ya canja mai kujerar zama kamar yanda a yanzu fadanshi da Sanata Natasha Akpoti ya samo Asali ne daga canja mata kujera

Duk Labarai
Rahotanni na tuna baya sun nuna cewa a lokacin tsohon kakakin majalisar Dattijai, Bukola Saraki, sun samu tirka-tirka da kakakin majalisa na yanzu, Sanata Godswill Akpabio kan maganar canja masa kujera. A wancan lokacin, Sanata Godswill Akpabio ya nemi yayi magana da lasifikar dake kujerar sanata Ali Ndume amma Sanata Bukola Saraki ya hanashi inda yace ya koma kan wata kujera da ya canja masa wadda lasifikarta na aiki. Saidai hakan ya jawo cece-kuce a majalisar inda a wancan lokacin aka zargi Bukola Saraki da aikata rashin Adalci. A wannan karin ma, abinda ya jawo cece-kuce tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti shine canja mata kujerar zama da kuma canja mata kwamiti.
Ka daina batawa Mahaifin mu suna>>’Ya’yan Abacha suka gargadi IBB

Ka daina batawa Mahaifin mu suna>>’Ya’yan Abacha suka gargadi IBB

Duk Labarai
'ya'yan Marigayi Janar Sani Abacha sun gargadi tsohon shugaban kasar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB cewa ya daina batawa mahaifinsu suna. Sanarwar wadda daya daga cikin 'ya'yan Sani Abachan, Muhammad Abacha ya fitar tace IBB ya zargi cewa Abacha da cewa shine yayi sanadiyyar soke zaben zaben Abiola. Saidai sanarwar tace wannan ikirari na IBB ba gaskiya bane, duk da yake cewa, Abacha babba ne a gwamnatin IBB din amma IBB din shine shugaban kasa. A karshe dai sun gargadi IBB din da ya daina batawa babbansu suna.
Na yi aiki da mata kyawawa masu yawa babu wadda ta taba cewa na nemeta sai Sanata Natasha Akpoti, dadin abin ba ni kadai ta taba kalawa sharri ba>>Sanata Godswill Akpabio

Na yi aiki da mata kyawawa masu yawa babu wadda ta taba cewa na nemeta sai Sanata Natasha Akpoti, dadin abin ba ni kadai ta taba kalawa sharri ba>>Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, Akwai mata da yawa kyawawa da yayi aiki dasu amma babu wadda ta taba zarginsa da neman yin lalata da ita sai Sanata Natasha Akpoti. Ya bayyana hakane a wajan taron ranar mata ta Duniya. Sanata Akpabio yace zargin da Sanata Natasha Akpoti ta yi masa ya girgiza Majalisar inda yace abin ya basu mamaki. Yace amma dadin abin bashi kadai ne ta taba yiwa irin wannan sharri ba da kuma ta kasa kawo shaida. Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ma ya zargi Sanata Natasha Akpoti da cewa shima ta taba kala masa sharrin yin lalata da ita amma daga baya aka gano karyane.
Karya ake mana, bamu ce muna goyon bayan Peter Obi da El-Rufai su yi takarar shugaban kasa a shekarar 2027 ba>>Inji Gwamnonin PDP

Karya ake mana, bamu ce muna goyon bayan Peter Obi da El-Rufai su yi takarar shugaban kasa a shekarar 2027 ba>>Inji Gwamnonin PDP

Duk Labarai
Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun musanta jita-jitar da ke cewa wasu daga cikinsu Guda biyar na Goyon bayan tikitin El-Rufai/Obi a zaɓen 2027. Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na ƙungiyar, Dakta Emmanuel Agbo, ya fitar a madadinsa a yau Asabar. Ya ce, “Wajibi ne a gare mu a matsayin ƙungiyar Gwamnonin PDP, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, mu fito mu karyata, kuma mu yi Allah-wadai da wadannan jita-jita marasa tushe da wasu ‘yan siyasa masu son zuciya ke yayatawa. Su ne dai ba za su iya jure irin kokarin da muke yi don nuna gazawarsu a shugabanci ba, wanda ya jefa ‘yan Najeriya cikin fatara da tsananin wahala.” “A saboda haka, ƙungiyar gwamnonin PDP ba ta d...
Tinubu da mukarrabansa sun kashe Naira Biliyan 1.9 wajan tafiye-Tafiye zuwa kasar Faransa

Tinubu da mukarrabansa sun kashe Naira Biliyan 1.9 wajan tafiye-Tafiye zuwa kasar Faransa

Duk Labarai
Manyan ma'aikatun Gwamnati da suka hada da fadar shugaban kasa sun kashe Naira Biliyan 1.9 wajan tafiye-Tafiye da horas wa a kasar Faransa. Hakan ya farune a tsakanin Watan May 2023 zuwa September na 2024. Wasu kungiyoyi masu zaman kansu da ke saka idanu kan yanda ake kashe kudin Gwamnati GovSpend ne suka gudanar da wannan bincike. Kudin dai an kashesu ne akan kudin jirgi, dana Otal, dana abinci dana horaswa da sauransu. Rahoton yace yawancin kudin an kashesu ne a wajan ayyukan horaswa.