Monday, April 20
Shadow
Kalli Bidiyo yanda aka wulakanta wani barawon Kunin Aya inda aka sashi yace shi barawo ne ya saci kunun aya

Kalli Bidiyo yanda aka wulakanta wani barawon Kunin Aya inda aka sashi yace shi barawo ne ya saci kunun aya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan wani mutum ne da aka kama a wani Shago a Abuja ya saci kunin Aya. Bayan kamashi an sashi ya rike takardar da ta ce ni barawo ne na saci kunun aya. https://www.youtube.com/watch?v=EFI6pOhuVsc Daga baya dai an barshi ya tafi ba'a masa komai ba. Mutanene suka roki me shagon ya kyaleshi.
Bai kamata ka turo matarka ta rika fada da Natasha ba, kai ya kamata ka tsaya a yi da kai>>Betty Akeredolu

Bai kamata ka turo matarka ta rika fada da Natasha ba, kai ya kamata ka tsaya a yi da kai>>Betty Akeredolu

Duk Labarai
Matar marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Betty Akeredolu ta bayyana cewa bai kamata kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya saka matarsa a cikin fadan da suke da Sanata Natasha Akpoti ba. Tace kamata yayi ace ya tsaya an yi fadan dashi ba ya koma gefe ya turo matarsa ba. Betty ta bayyana hakanne a kafar X. Tace kuma Sanata Natasha Akpoti ta birgeta data fito ta nuna rashin jin dadinta kan canja mata kujera ba tare da saninta ba. Tace dan an yiwa wasu sun yi shiru hakan ba yana nufin itama ta yi shiru bane. tace irin su Sanata Natasha Akpoti ne ya kamata ace mata suna sakawa a gaba dan su jagorancesu musamman a majalisa.
Alawus din da kuke dauka me yawa da yanda kukafi kowa kudi na baiwa ‘yan Najeriya haushi sosai>>Batist Church ta gayawa Tinubu

Alawus din da kuke dauka me yawa da yanda kukafi kowa kudi na baiwa ‘yan Najeriya haushi sosai>>Batist Church ta gayawa Tinubu

Duk Labarai
Kungiyar Baptist church dake Abuja sun caccaki gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka bukace shi yayi wani abu game da yunwa da matsin rayuwa dake damun 'yan Najeriya. Cocin ta bayyana hakane a yayin taron cikarta shekaru 10 da kafuwa a Abuja inda manyan baki a wajan suka soki irin rayuwar kece raini da 'yan siyasa ke yi yayin da su kuma talakawa aka barsu cikin halin kaka nikayi. Daya daga cikin wadanda suka yi magana a wajan taron zhine Reverend Dr. Israel Akanji inda yayi kira ga gwamnati data kawo tallafi a bangaren Ilimi, da lafiya da noma. Yace 'yan Najeriya da yawa na daf da fadawa matsalar yunwa da zata iya kaisu ga halaka. Yace suna yabawa da kokarin da gwamnati take yi amma akwai bukatar a kara kaimi. Yace Alawus masu yawa da 'yan siyasa ke dauka da kum...
Barayi sun sace mashina 3 yayin da ake sallar Taraweeh a Abuja

Barayi sun sace mashina 3 yayin da ake sallar Taraweeh a Abuja

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Barayi sun sace mashina 3 a wani masallaci dake Tipper garage dake Kuje, babban Birnin tarayya, Abuja. Lamarin ya farune ranar Asabar a yayin da ake sallar Taraweeh a wani masallaci dake cikin Gidan mai. Wani shaida me suna Ibrahim Jamilu ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa, bayan sun kammala sallah, mutane 3 sun bayyana cewa, an sace musu mashina. Yace sun sanar da kungiyar masu mashina da kungiyar 'yan Kato da Gora wanda aka bazama neman mashinan. Saidai 'yansandan dake yankin sunce ba'a sanar dasu ba.
Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta dakatar da Kabir Sani-Giant saboda kai maciji cikin gidan gwamnatin jihar ya tsorata mutane

Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta dakatar da Kabir Sani-Giant saboda kai maciji cikin gidan gwamnatin jihar ya tsorata mutane

Duk Labarai
Jam'iyyar APC a jihar Kebbi ta dakatar da Kabir Sani-Giant saboda kai maciji cikin gidan Gwamnatin jihar ya tsorata mutane. Sakataren Jam'iyyar na jihar, Alhaji Sa’idu Muhammad-Kimba ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Lahadi. Yace ranar February 8, 2025 Kabir ya shiga da maciji cikin gidan gwamnatin jihar inda ya tsorata mutane, yace hakan ya sabawa kundin tsarin Jam'iyyar. Yace dakatarwar da akawa kabir zata ci gaba da zama har zuwa lokacin da za'a kammala buncike akansa.
Za’a rage farashin kiran waya dana data daga kaso 50 zuwa kaso 35

Za’a rage farashin kiran waya dana data daga kaso 50 zuwa kaso 35

Duk Labarai
Rahotannin da kafar hutudole ta samu na cewa, za'a rage farashin kudin kiran waya dana data daga kaso 50 da aka kara zuwa kaso 35. Hakan ya bayyanane a cikin jawabin da shugaban kungiyar NLC ya fitar inda suke barazanar shiga yajin aiki idan ba'a yi wannan ragi ba. Hutudole ya faimci cewa, an yi zama tsakanin Gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro inda aka cimma matsaya gane da karin kudin kiran waya dana data, maimakon kaso 50 cikin 100 da aka yi, yanzu zai koma kaso 35 cikin 100. Kungiyar NLC tace idan ba'a tabbatar da wannan kari ba, zata tafi yajin aiki.
Ba zamu yadda da karin kudin wutar lantarki ba>>NLC

Ba zamu yadda da karin kudin wutar lantarki ba>>NLC

Duk Labarai
Kungiyar kwadago ta NLC ta yi gargadin cewa idan aka ce za'a kara kudin wutar lantarki ba zasu amince da hakan ba, zasu tafi yajin aiki. Kungiyar tace ba zata amince da duk wata dabara ta kokarin kara kudin wutar lantarkin ba. Tace idan aka yi hakan zata jagoranci gagarumar zanga-zanga. Kungiyar ta NLC tace tana sane da shirin da ake yi na mayar da kowa da kowa kan tsarin Band A na wuta da sunan wai inganta samar da wutar, kungiyar tace ba zata amince da hakan ba dan yunkuri ne na kara kudin wutar lantarkin.
Ana ci gaba da kiraye-kirayen cewa Jihohin Arewa da suka bada hutun Ramadan a makarantu basu kyauta ba, inda Kungiyar Kiristocin CAN tace ko Saudi Arabia da UAE basu bayar da hutu a makarantu ba saboda Ramadan

Ana ci gaba da kiraye-kirayen cewa Jihohin Arewa da suka bada hutun Ramadan a makarantu basu kyauta ba, inda Kungiyar Kiristocin CAN tace ko Saudi Arabia da UAE basu bayar da hutu a makarantu ba saboda Ramadan

Duk Labarai
Masu sharhi a kafafen yada labarai da kafafen sada zumunta musamman daga kudancin Najeriya kuma mafi yawanci Kiristoci na ci gaba da yin Allah wadai da hutun da wasu jihohin Arewa suka bayar a makarantu saboda zuwan watan ramadana. Ko da a jiya, saida kungiyar Kiristocin CAN ta fitar da sanarwar cewa, bata goyon bayan bayar da wannan hutu i da tace babban abin takaici ma shine ba'a tuntubeta ba kamin bayar da wannan hutu. Jihohin da suka bayar da irin wannan hutu sun hada da Katsina, Kano, Kebbi da Bauchi. A maganar da Kungiyar kiristoci ta CAN tayi tace akwai kasashen da suka fi 'yan Najeriya yawan musulmai amma duk da haka basu bayar da hutun Azumin watan Ramadana a makarantun su ba maimakon hakan sun rage yawan awannin da ake zuwa makarantunne. Da safiyar yau, Litinin ma Kaf...