Gwamna Bago ya janye matakin da ya ɗauka akan samari masu tara gashin dada a Neja
Gwamna Bago ya janye matakin da ya ɗauka akan samari masu tara gashin dada a Neja.
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya janye umarninsa na baya da ya bayar ga jami’an tsaro da su kama masu gashin dada da maza masu Kitso a Minna, babban birnin jihar.
Bago, yayin da yake magana a wani taron tsaro tare da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati ranar Talata, ya umarci jami’an tsaro da su yanke gashin dada na mutanen da aka kama tare da cin tarar kudi.
Ya ce: “Duk wanda kuka gani da Gashin Dada, ku kama shi, ku yanke masa gashi, sannan ku ci shi tara.
“Babu wanda zai rika yawo da irin wannan gashi a cikin Minna. Na riga na ba da umarni ga jami’an tsaro,” in ji gwamnan.
Sai dai a ranar Laraba, gwamnan ya janye wannan umarni bayan ya fuskanci suka daga 'yan Najeriya da dama.
Yayin...








