Saturday, November 15
Shadow
YANZU-YANZU: Babiana Ta Fitar Da Takardar Saki Ukkun Da Mìjinta Yayi Mata

YANZU-YANZU: Babiana Ta Fitar Da Takardar Saki Ukkun Da Mìjinta Yayi Mata

Auratayya, Nishadi
DAGA Shafin Dokin Karfe TV Jarumar Tik-Tok Hafsat Waziri, wadda aka fi sani da Babiana ta bayyana cewa mijinta ya sake ta saki uku dan haka, yanzu haka ba ta da aure kuma ta ga cewa bai kamata ta yi ta ɓoye-ɓoyen sakin da mijinta yayi mata ba gara ta fito ta shaidawa Duniya halin da take ciki. Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu takardar shaidar sakin wadda Babiana Waziri ta aiko mata inda a ciki aka bayyana cewa "Ni Muhammad Izzudden Eze na saki matata saki uku". An rubuta takardar ranar 11 ga watan 4 na shekarar 2024, kamar yadda kuke gani. Babiana ta kuma bayyana cewa "Na shiga bala'in rayuwa a dalilin aurensa da nayi, har asibitin mahaukata an kai ni a dalilin aure kuma har yanzu ban gama farfaɗowa ba". In ji ta. Daga nan ta ƙara da cewa "Mijina ba ya biya mun buƙatuna na rayuwa...
YANZU – YANZU: Matashin Malami mai da’awah, Mufti Yaks ya rasú

YANZU – YANZU: Matashin Malami mai da’awah, Mufti Yaks ya rasú

Ilimi
INNÁ LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UÑ YANZU - YANZU: Matashin Malami mai da’awah, Mufti Yaks ya rasú. Allah Ya yi wa matashin malamin nan Abdullateef Aliyu Maitaki, wanda aka fi sani da Mufti Yaks rásúwâ. Sheikh Isa Ali Pantami ne ya wallafa labarin rasúwar ta matashin malamin, wanda ya ke kwaikwayòn shararren malamin nan Mufti Menk, a shafinsa na Facèbook a yau Asabar da safe. Pantami, wanda ya baiyana kaɗuwar sa da rasúwar matashin malamin, wañda ya ke gabatar da wa’azuzzukañ sa da turanci ta kafafen sada zumunta, ya ce za a yi jana’izar sa da ƙarfe 10 na safe a layin Justice Maiyaki, Dutsén Kura Gwari, Minna, Jihar Neja. Marigayi Mufty Yaks sananne ne wajén da’awah (kira zuwa ga Musúlunci) a ciki da wajén Nájeriya. Mu na fatan Allah Ya karbi dukkanin aiyukansa na alk...
An bayyana sunayen sojojin da Kungiyar IPOB ta kashe

An bayyana sunayen sojojin da Kungiyar IPOB ta kashe

Tsaro
Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana sunayen sojoji 5 da ake zargin 'yan Kungiyar IPOB sun kashe. An kashe sojojinne a ranar Laraba a Obikabia dake jihar Abia. sunayen sojojin sune: • Sergeant Charles Ugochukwu (94NA/38/1467)• Sergeant Bala Abraham (03NA/53/1028)• Corporal Gideon Egwe(10NA/65/7085)• Corporal Ikpeama Ikechukwu (13NA/70/5483)• Corporal Augustine Emmanuel (13NA/70/6663) Hukumar sojojin Najeriya dai ta sha Alwashin daukar mataki me tsauri dan rama kisan sojojin nata.
‘Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu’

‘Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu’

Tsaro
Asusun bayar da bashin karatu na Najeriya (NELFUND) ya ce sama da ɗalibai miliyan 9.5 ne suka kai ziyara ofishinta dangane da bashin karatu da za a bai wa dalibai tun bayan buɗe shafin da za a cike takardar neman bashin karatun a ranar Juma’ar da ta gabata. Sama da ɗalibai 6,000 ne suka cike takardan neman bashin. Yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a taron da aka shirya wa ɗaliban da suka cike takardan neman bashin a ranar Alhamis, shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce sama da kashi 90 cikin 100 na manyan makarantun gwamnatin tarayya sun mika bayanan dalibansu da cibiyoyi kusan biyar da suka rage. Ya kuma bayyana cewa nan da makwanni uku za a bude shafin neman bashin ga daliban da ke manyan makarantu na gwamnati domin su samu su iya cike takardun neman bashin karat...
Gwamnatin Abia ta sa ladan N25m ga wanda ya fallasa mutanen da suka kashe sojoji

Gwamnatin Abia ta sa ladan N25m ga wanda ya fallasa mutanen da suka kashe sojoji

Tsaro
Gwamnatin jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya ta saka ladan naira miliyan 25 ga duk mutumin da ya bayar da bayanan da za su taimaka a kama mutanen da suka kashe sojoji a jihar. Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Okey Kanu ya fitar, gwamnatin jihar ta aike da sakon ta'aziyya ga babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja kan faruwar lamarin. A ranar Alhamis ne wasu 'yan bindiga suka afka wa sojoji a wani shingen bincike a mahadar Obikabia da ke yankin tsaunin Ogbor, tare da kona motar aikinsu. Rahotonni sun ce wasu sojojin sun samu tsallake rijiya da baya a harin. “Domin samun saukin kama maharan, gwamnati ta yi alkawarin bayar da ladan naira miliyan 25 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama su,'' in ji s...
Amurka za ta tallafa don sake gina makarantu da asibitoci a Gaza – Biden

Amurka za ta tallafa don sake gina makarantu da asibitoci a Gaza – Biden

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ana bukatar hanyar sasanci domin kawo karshen yakin yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da daidaita lamurra a kan iyakar arewacin Lebanon. Mista Biden ya ce akwai bukatar shugabannin Falasdinawa da na Isra'ila su hada kai domin sake gina Gaza, ta yadda ba za a bar Hamas ta sake mallakar makamai ba. ''Amurka za ta tallafa wajen sake gina makarantu da asibitocin Gaza'', in ji Biden. Ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen sake daidaita lamurran dangataka da Saudiyya da magance barazanar Iran a yankin. Mista Biden ya kuma gabatar da kudurin da zai bai wa Isra'ila damar zama mai karfi a yankin.
An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema  wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

An kulle kasuwanni da makarantu yayin da sojoji ke nema wanda suka kashe sojoji 5 a garin Aba

Tsaro
Garin Aba ya rikice inda sojoji suka mamayeshi bayan kisan abokan aikinsu 5. Wasu da ake kira da 'yan Bindigar da ba'a san ko su wanene ba amma ana kyautata zaton 'yan IPOB ne kawai da suke fakewa da wannan sunan suka yi kisan. Sun yi kisanne ranar Laraba bayan sun tursasa kowa ya je gida ya zauna dan tunawa da mutanen da suka mutu a yakin Biafra. Lamarin yasa hukumar sojojin Najeriya ta sha Alwashin sai ta rama wannan kisa da kakkausar murya. Rahoton jaridar Vanguard yace sojojin sun shiga kasuwanni suka tursasa mutane suka kulle shaguna da kuma a jiya, Juma'a yawanci yara basu je makaranta ba a garin. Hakanan an ga jirage masu saukar Angulu suna shawagi a sararin samaniyar wajan.
Bidiyo da Hotuna: Kalli Yanda Ali Jita da Rahama Sadau suke shakatawa a Landan

Bidiyo da Hotuna: Kalli Yanda Ali Jita da Rahama Sadau suke shakatawa a Landan

Ali Jita, Kannywood, Rahama Sadau
Taurarin Fina-finan Hausa, Rahama Sadau da Ali Jita kenan a wadannan hotunan da bidiyo suke shakatawa a kasar waje. An ga Jita da Rahama dai suna nishadi tare a cikin mota da kan titi. Ali Jita ne ya saka bidiyon a shafinsa na sada zumunta. https://www.tiktok.com/@realalijita/video/7375206383370652933?_t=8mpctjMHVyA&_r=1 Da yawan mata da maza na masana'antar Kannywood sukan je kasashen waje dan shakatawa.
Kasashen Larabawa sun sha Alwashin ba zasu bar Falas-dinawa su sake mallakar makamai ba bayan yakin su da Israela

Kasashen Larabawa sun sha Alwashin ba zasu bar Falas-dinawa su sake mallakar makamai ba bayan yakin su da Israela

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Larabawa sun dauko alwashin ba zasu sake barin Falas-dinawa au mallaki makamai ba bayan an gama yaki tsakaninsu da Israela. Hakan na zuwa ne yayin da ake tsammanin za'a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Israela da Kungiyar Hamas. Saidai abin tambaya anan shine, anya kasashen Larabawan zasu iya aikata hana Falas-dinawa mallakar makamai? Dalili kuwa shine a yanzu gashi ana ta kashesu babu kasar Larabawan data shigar musu ko ta tsaya musu, an zura ido ana kallo Israela na musu kisan kare dangi, ta yaya zasu yadda a hanasu mallakar makamai bayan sun san duk randa Israela ta sake far musu da yaki babu me tare musu? Wannan dai abune me kamar wuya.