Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka hàrbè wani dan Daba me suna Halifa Baba a Kano wanda duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun sa a ciki
Rahotanni daga unguwar Gwammaja da ke nan Kano sun bayyana yadda a ka harbi wani rikakken dan daba, Halifa Baba, yayin arangama tsakanin jami'an tsaro da bata-gari a yankin.
A na zargin cewa duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun Halifa Baba a ciki.
Majiyarmu tace bisa dukkan alamu Halifa Baba rai ya yi halinsa.
https://www.tiktok.com/@garkuwanyancrypto/video/7496266492581907717?_t=ZM-8vlrVEM7buw&_r=1
Shaidu sun ce jami'an 'yan sandan Dala Division ne su ka dauke Halifa Baba domin ci gaba da bincike.
Daga NasaraRadio








