Atiku Abubakar ƙyashi yake yi wa Shugaba Tinubu – Fadar Shugaban Ƙasa
Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na shugaban ƙasa, muƙamin da ɗantakarar jam'iyyar PDP na muƙamin a 2023, ta ce yake ta faman nema har sau shida amma bai yi nasara ba.
Fadar shugaban ta soki Atikun ne saboda shawarar da ya bayar ta sauye-sauyen tattalin arziƙi da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a wani saƙon Tweeter da ya sanya kwanan nan.
Wani saƙo da ya fito daga fadar shugaban ƙasar, wanda mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ya ce, tun bayan da Atiku ya sha kaye a zaɓen 2023 a hannun Tinubu, ya fi mayar da hankali kan zagon-ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam'iyyarsa....








