Sunday, December 21
Shadow

Gwajin ciki da sugar

Gwajin Ciki
Gwajin ciki da Sugar ana yinshine ta hanyoyi kamar haka: Ana samun kofi ko kwano ko kuma mazubi a yi fitsari a ciki. Bayan nan sai a zuba sukari a ciki. Yanda ake gane idan ciki ya shiga: Idan mace na da ciki, bayan ta hada fitsarin ta da sukari, zata ga ya yi kulalai. Yanda ake gane babu ciki: Idan mace ta bata dauki ciki ba, bayan ta hada sukarin da fisarin zata ga suka yin bayi kula lai ba. Menene ingancin gwajin ciki da sugar? Gwajin ciki da sugar hanyace ta gargajiya wadda ake amfani da ita wajan gano mace na da ciki ko bata dashi. Saidai babu wani binciken masana lafiya daya tabbatar da cewa wannan hanya na aiki wajan gane mace na da ciki ko bata dashi.
Nasan cewa matakan dana dauka a mulkina sun saka mutane wahala>>Shugaba Tinubu

Nasan cewa matakan dana dauka a mulkina sun saka mutane wahala>>Shugaba Tinubu

labaran tinubu ayau, Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yasan matakan da gwanatinsa ta dauka na tayar da komadar tattalin arziki sun kawo wahala. Ya bayyana hakane a jawabin da yayi da safiyar yau na ranar Dimokradiyya. Inda yace yana sane da wahalar da 'yan kasa suke sha. Ya bayyana cewa amma daukar matakan dolene dan dora Najeriya a turba me kyau wadda zata daina dogaro akan man fetur kadai dan samun kudin shiga. Ya bayyana cewa wannan abu ne da ya kamata a yi shi da dadewa amma shuwagabannin da suka gabata ba su yi ba.

Gwajin ciki na sati daya

Gwajin Ciki
Bayan yin jima'i ba tare da kariya ba ta kwaroron roba, watau Kondom, mace zata iya daukar ciki. Kuma zaki so yin gwaji da ganin kin dauki cikin ko baki dauka ba? Saidai masana sun bayyana cewa, sati daya yayi kadan ki gane cewa kin dauki ciki ko baki dauka ba. Mafi abinda ya dace a yi shine a dakata har sai bayan kwanaki 10 zuwa sati 2 da yin jima'i kamin a fara yin gwajin ciki. Wasu kuma sun bayar da shawarar a jira sai bayan daukewar jinin al'ada. Ana iya yin gwajin ciki ranar farko da aka yi batan wata. Jira zuwa lokaci me tsawo watau sati 3 zuwa 4 bayan an yi jima'i ba tare da kariyar kwaroron roba ba, watau kondon kamin a yi gwajin ciki, ya fi bayar da sakamako me kyau.

Tauraruwar Fina-Finan kasar Amurka, Angelina Jolie ta yi Allah wadai da shuwagabannin kasashen Duniya saboda kyalewa da suka yi anawa Falas-dinawa kisan kiyashi

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Tauraruwar Fina-finan kasar Amurka, Angelina Jolie ta yi Allah wadai da kisan da akewa Falasdinawa. Sannan kuma tace Tana zargin shuwagabannin kasashen Duniya da suka saka Ido suna ganin yanda akewa Falasdinawa kisan kiyashi. Jolie dai dama ta kasance me son tallafawa mutane inda a baya ta yi aiki da majalisar dinkin Duniya wajan bada ayyukan agaji.
Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da sulhu da kasar Israela

Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da sulhu da kasar Israela

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da tayin yin Sulhu da kasar Israela. Shugaban Hezbollah din, Hassan Nasrallah ne ya bayyana haka. Fada na ci gaba da kazancewa tsakanin kasar Israela da Hezbollah. Ko da a jiya sai da Hezbollah tawa kasar Israela ruwan bamabamai masu yawa. Kungiyar dai ta Hezbollah ta bayyana cewa tana goyon bayan samun 'yancin Falasdinawa.
Tinubu ya ce a kamo maharan da suka kashe mutum 50 a Katsina

Tinubu ya ce a kamo maharan da suka kashe mutum 50 a Katsina

Siyasa
Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kamo maharan da suka kai hari a ƙananan hukumomin Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da tabbatar da an hukunta su. Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman Ajuri Ngelale ya fitar a ranar 11 ga watan Yuni, 2024 yana mai kakkausar suka kan yawaitar hare-hare a ƙasar. A yayin da ya bayyana sabbin hare-haren a matsayin munanan hare-hare, shugaban ya jaddada cewa za a ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaron ‘yan kasa da kuma taarwatsa ‘yan ta’adda gaba daya da sauran masu tayar da zaune tsaye da kuma baƙin ciki a kowane ɓangare na ƙasar. Shugaban ya jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, da gwamnati da kuma al’ummar jihar Katsina, tare da addu’...
Ba mu ƙara kuɗin da muke kashewa a tallafin man fetur ba – NNPCL

Ba mu ƙara kuɗin da muke kashewa a tallafin man fetur ba – NNPCL

Kasuwanci
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya musanta rahotannin da ke cewa ya kara kudin tallafin man fetur da sama da naira tiriliyan uku a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai magana da yawun kamfanin na NNPCL, Olufemi Soneye, ya jaddada cewa an tabbatar da ikirarin tallafin da kamfanin ya bayar, tare da mika dukkan bayanan da suka dace ga hukumomin da suka dace. Ya kuma bayyana cewa kamfanin na NNPCL bai san wani shiri na tantance asusun ajiyarsa ba, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai na farko suka nuna. "NNPCL ta lura da wani rahoto a wani sashe na kafafen yada labarai da ke zargin cewa ta kara kudin tallafin da naira triliyan 3.3," in ji Soneye. “NNPCL tana gudanar da kasuwancinta ne cikin gaskiya bisa kya...
2024Sojojin Najeriya sun musanta zarge-zargen da Amnesty International ta yi musu

2024Sojojin Najeriya sun musanta zarge-zargen da Amnesty International ta yi musu

Tsaro
Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton da Amnesty International ta fitar na zargin jami’anta da tsare tare da cin zarafin mata da yara da dama da suka tsere daga hannun ‘yan Boko Haram a yankin arewa maso gabas. Mai magana da yawun rundunar Edward Buba ta bakin mataimakinsa kan yaɗa labarai, Group Kaftin Ibrahim Ali Bukar, ya shaida wa BBC cewa "ba za su damu da irin waɗannan kalamai na son kai da aka yi da niyyar rage kwarin gwiwar sojojin fafutuka don tabbatar da tsaro ba" Ya kara da cewa sojojin za su yi haɗin gwiwa mai inganci da Amnesty International idan akwai bukatar yin hakan kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kawar da ta'addanci da tabbatar da tsaro. Wannan martanin ya zo ne kwana guda bayan da Amnesty International ta zargi gwamnati da gazawa wajen bai wa ...
Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Katsina, Siyasa, Tsaro
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara wa al’ummar yankin. Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu. “Wannan babban rashi ne, kuma tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu,” in ji shi Atiku ya soki matakan da gwamnati...
‘Jami’an tsaro shida na cikin mutanen da aka kashe a harin Katsina’

‘Jami’an tsaro shida na cikin mutanen da aka kashe a harin Katsina’

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce akwai dakarunta huɗu da kuma dakarun tsaro biyu na gwamnatin jihar cikin mutanen da 'yanbindiga suka kashe a harin da suka kai ranar Lahadi. Kakakin 'yansadan a Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an tsaurara tsaro a yankin ƙaramar hukumar Kankara, inda suke aiki da sauran hukumomin tsaro don kare sake aukuwar harin. "A ranar 8 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 3:00 na rana maharan suka far wa garuruwan Gidan Tofa da Dan Nakwabo, inda suka harbe mutum 20 tare da raunata wasu biyu, sannan suka yi wa motarmu mai silke kwanton ɓauna kuma suka kashe jami'an 'yansanda huɗu da kuma biyu cikin dakarun tsaron gwamnatin Katsina (KSCWC)," in ji sanarwar. Tun da farko rahotonni sun ce aƙalla mutum 25 aka kashe a ...