Ina da kwararan shaidu cewa mijin ki mijin ki ɗan neman mata ne – Sanata Natasha ga matar Akpabio
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bukaci Ekaette Akpabio, matar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da ta send tsoma baki a batun zargin da ta ke yi wa mijin na ta na neman mata.
A wata hira da aka yi da ita a tashar Arise a ranar Juma’a, Sanata Natasha mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, ta bayyana cewa Akpabio ya yi mata tayin lalata a ofishinsa da kuma gidansa da ke Akwa Ibom.
Hakan ne ya sanya matar Shugaban Majalisar Dattawan, Ekaette, ta mayar da martani inda ta ce mijinta mutum ne mai kamun kai, kuma ta ce ikirarin sanatar “karya ne.”
Ekaette ta kuma shigar da kara a kotu kan take hakki ta da ɓata suna da Akpoti-Uduaghan ke yi.
A cikin wata wasika mai kwanan wata 1 ga Maris, da aka aikawa matar Shugaban Majalisar, sanatar, ta hannun lauyanta, Vict...








