An gano Maniyyata na sayarwa da Takari Uniform dinsu a kudi me tsada a kasar Saudiyya
Hukumar alhazan Najeriya, NAHCON ta gargadi maniyyatan kasar kan sayar wa wadanda ke zaune a Saudiyya domin neman kudi da aka fi sani da 'takari' tufafin da hukumar ta dinka musu domin gudanar da ayyukan hajjin.
Daraktan Da'awah na hukumar ta NAHCON reshen jihar Kebbi, Sheikh Aminu Hassan ne ya bayyana haka lokacin da yake yi wa maniyyatan jhar jawabi bayan isarsu kasa mai tsarki.
Akwai zarge-zargen cewa takarin na sayen tufafin wasu maniyyatan musamman mata da kudi masu yawan gaske, tare da yin bad da bami domin shiga cikinsu da fakewa da aikin hajjin wajen aikata abubuwan da ba su dace ba.
Sheikh Aminu Hassan ya ce sayar da tufafin babban laifi ne da zai iya janyo wa duk wanda ya aikata hukunci mai tsanani, don haka ne ya gargadi maniyyatan su kauce wa wannan mummunar dabi'a.
...








