An ga gawar wata mata me ciki kwance tsirara akan titi wanda lamarin ya tayarwa da mutane hankali.
An ga gawarne a titin Amaraku-Umudim dake karamar hukumar Isiala-Mbano ta jihar Imo.
Saidai ba'a kai ga tantance menene sanadiyyar mutuwar matar ba.
A karshe dai, kasashen Tarayyar Turai karkashin EU sun juyawa kasar Israela baya.
Kasashen sun fito sun nemi a kakabawa kasar Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa.
Hakan ya biyo bayan nacewa da kasar ta yi cewa sai ta shiga Rafah inda dubban fararen hula na Falasdinawa ke gudun Hijira.
Kasar kuma ta kai wani mummunan hari a sansanin 'yan gudun hijirar wanda ya kone mutane akalla 50 kurmus ciki hadda yara kanana.
Lamarin ya jawowa kasar Israela Allah wadai wanda daga baya Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu ya fito yace kuskurene kuma suna bincike akai.
A jiya, Talata dai an samu hukunce-hukuncen kotu biyu masu karo da juna wanda daya na babbar kotun tarayya ce dake Kano data ce a sauke Sarki Muhammad Sanusi II saga sarautar Kano.
Mai shari'a, S. Amobeda ne ya bayyana hakan a hukuncin daya fitar inda yace a mayar da Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kano.
Saidai itama babbar kotun Kano karkashin mai shari', Amina Aliyu tace Sarki Muhammad Sanusi II ne sarkin Kano inda kuma tace Sarki Aminu Ado Bayero ya daina bayyana kansa a matsayin sarkin Kano.
Saidai duk da wannan hukunci, Sarki Aminu ya ci gaba da zama a karamar fadar dake Nasarawa inda yace ci gaba da ayyana kansa a matsayin sarkin Kano.
Rahotanni sunce har yanzu akwai jami'an tsaro da aka girke a gidan Nasarawa wanda kuma suna hana ma mutane bin hanyar sai wanda ya zama...
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Sadiya Kabala ta bayyana cewa, Sarki Aminu Ado Bayero e zabinta.
Ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumunta i da tace bata hana kowa ya bayyana zabinsa ba.
Sadiya ta saka hoton sarkin tana waka akai.
Rikicin sarautar Kano wadda ya taso bayan da majalisar jihar ta sauke Sarki Aminu Ado Bayero ta mayar da tsohon Sarki Muhammad Sanusi II akan karagar sarautar ya raba kawunan mutane da yawa a ciki da wajen jihar ta kano.
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana dawo da tsarin tallafawa mutane wanda ta tsayar a watannin da suka gabata.
Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a matsayin shiri na cika shekara daya da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi.
Tsarin dai wanda ya hada da ciyar da dalibai, da Npower, da baiwa mutane gajiyayyu kudin tallafi da tallafawa 'yan kasuwa da sauransu a yanzu ya dawo zai ci gaba da aiki.
Ministan yace dama a baya an tsayar da tsare-tsarenne dan bincike da kuma kawar da matsalolin dake cikin tsarin kuma yanzu an kammala.
A dambarwar da aka yi ta dakatar da tsarin, ta hada da dakatar da ministan jin kai Beta Edu wadda aka yi zargin ta aikata ba daidai ba.
Saidai a yayin da yake maganar, Mi...
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar wanda kuma shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata na shekarar 2023 ya soki gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bayan da ta cika shekara guda da kafuwa.
Atiku yace tsare-tsaren gwamnatin Tinubu ta jefa mafi yawan al'umma cikin halin wahala inda kuma ta talauta masu kudi.
Atiku yace Najeriya bata aiki a karkashin Tinubu inda yace Tinubun ya kasa kawo canji da ci gaban da ya mutane alkawari.
Yace matakan da Tinubu ya dauka sun ma kara jefa mutanene cikin halin kaka nikayi.
Yace matsayin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki a yanzu yafi muni idan aka kwatanta da shekara daya data gabata.
Yace gwamnatin Tinubun ta karawa mutane wahala ne akan wahalar da ake ciki wadda gwamnatin tsohon s...
Wannan aikin na ciyar da kada abinci ana ganin kamar yafi kowane wahala a Duniya.
Ko nawa za'a baka ka iya yinshi?
https://www.youtube.com/watch?v=_5M-d07qjZk
Farashin dala ya dan fadi kasa a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu na shekarar 2023.
An kulle kasuwar dalar akan ana sayen dala a farashin Naira 1,339.33.
Idan aka kwatanta da farashi Naira 1,482.81 da aka sayi dalar a ranar Juma'a, ana iya cewa an samu ci gaba.
Shugaban jam'iyyar ADC, Dr Ralphs Okey Nwosu ya bayyana cewa, sai an shekara 6 ana wahala kamin a kawo karshen wahalar da cire tallafin man fetur ya jefa mutane.
Ya bayyana hakane hirar da Daily Trust ta yi dashi.
Cire tallafin man fetur ya jefa mutane da yawa a cikin matsin rayuwa inda mutane suka rika fama da abinda zasu ci wanda a baya ba haka bane.
Saidai Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, wannan mataki ne data dauka dan amfanar al'umma baki daya wanda kuma na dolene.
Wasu alamu sun nuna cewa ga dukkan mai yiyuwa kwaikwakayar sa hannun babban alkalin kotun tarayya dake Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya da yace a cire sarki Muhammad Sanusi II daga kan kujerar sarautar Kano.
A wani bincike da Kafar Daily Nigerian ta yi, ta gano cewa sa hannun da aka gani a takardar data dakatar da sarkin ta banbanta da sauran sahannun da alkalin ya saba yi.
Kuma a baya, Alkalin yakan saka hannu a duka takardun hukunci ne amma a na hukuncin da ya sauke sarkin, a takardar karshe ce kawai aka saka hannun.
Hakanan kuma Akwai wanda ake tuhuma a takardar kotun su 8 amma cikinsu babu wanda baiwa kwafin takardar sai kwamishinan 'yansandan jihar kadai.
Wannan yasa ake zargin cewa takardar ta boge ce.