Hadin tsawon gashi
Hadin tsawon gashi
Akwai hanyoyi da dama da mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo.
Abu ne mai sauki.
Mata da dama suna son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau don haka, ya kamata mu kula da gashinmu sosai. Wannan hadin da zan rubuto muku na dada wa gashi maiko , wato yana hana gashi karyewa da sanya shi tsayi da laushi.
Ina son a san cewa wannan hadin akan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, ba ya kamata ana hada wannan salon gyaran gashi da wani daban in ba haka ba, sai a ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Abubuwan da za a bukata
Man AmlaZumaRuwan dumiHadi
A zuba cokalin amla biyu a roba.Sannan sai a zuba rabin cokalin ...


