Ka Hakura da neman zama shugaban kasa, Allah be kaddaro maka zaka mulki Najeriya ba>>Wike ya gayawa Atiku
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesome Wike ya gayawa Alhaji Atiku Abubakar cewa ya daina neman takarar shugabancin Najeriya dan ba zai samu ba saboda Allah be kaddaro masa zai mulki Najeriya ba.
Wike ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Lere Olayinka inda ya kara da cewa, laifuka da cin amanar da yawa jam'iyyar PDP ne a baya ke tambayarsa.
Yace ya kamata Atiku ya gane cewa shi yanzu ya zama uba dan a lokacin da yayi takara a jami'iyyar SDP Wike bai wuce shekaru 25 ba.
Dan haka yace Atikun ya hakura dan a shekarar 2027, PDP ba zata sake bata tikitin takarar shugaban kasarta ta baiwa wanda ba zai ci zabe ba dama.