{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Babban Malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa a kyale mutane su dandana wahalar Rayuwa watakila hakan zai sa su shiga taitayinsu ta yanda zasu rika kalubalantar azzaluman shuwagabanni.
Ya bayyana hakanne da yammacin yau, Juma'a, 7 ga watan Yuni yayin da yake karatun littafin Muktasar a masallacin Sultan Bello dake Kaduna.
Malam ya kara da cewa, mutane suna da wakilai a majalisar tarayya idan akwai abinda basa so zasu iya gayawa wadannan wakilai cewa shugaban kasa ya canja idan ba haka ba ...
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar Gwamnatin tarayya zata ranto Naira Tiriliyan 6.6 dan cike gibin kasafin kudi.
Gwamnatin zata ciwo bashinne a wannan shekarar ta 2024 kuma zata yi hakan ne dan samar da kudin da zata biya tallafin man fetur wanda zai lakume Naira Tiriliyan 5.4.
Kafar yada labarai ta Reuters ce ta ruwaito wannan labari.
Saidai Gwamnatin tarayya ta ci gaba da nanata cewa ita fa har yanzu bata biyan tallafin man fetur.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, a yayin da ya cika shekara daya da fara mulkin Najeriya, ya cika alkawuran da ya daukarwa yan kasar.
Tinubu ya bayyana haka ta bakin ministan yada labarai, Muhammad Idris.
Ministab yace tun bayan hawansa mulki, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cika alkawuran tada komadar tattalin arziki.
Yace ya cire tallafin dala dana nera da sauransu.
Ga bayanin sa kamar haka:
“Since taking office a year ago, President Tinubu has done what he promised on the economy: he has removed the fuel subsidy, floated the Naira, and instituted a raft of other reforms including changes to the tax code and waivers for foreign investors in critical industries including mining, energy, and infrastructure.”
Matashi Mai Suna Umar Faruk Muhammad Zai Angwace Da Mata Biyu A Rana Guda, Zai Auri Safinat Shuaibu Da Sadiyya Salihu.
Za'ayi Daura Auren A Ranar 22 Ga June 2024 Idan Allah Yakaimu.
Wane Fata Zakuyi Mashi?
~Karaduwa Post
A karo na 3 an tsinci jaririya da aka yadda a East London.
An tsinceta ne a Newham cikin tsanin sanyi ranar 18 ga watan Janairu na shekarar 2024.
Saidai binciken kwayoyin halitta na DNA sun nunar cewa, ita wannan jaririya tana da 'yan uwa har guda 2 wanda suma aka yaddasu a shwkarun 2017 da 2019.
Zuwa yanzu dai ana bincike ba'a gano iyayen wadannan yara ba.
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA ta kama wasu mahajjata a otal din Emerald Hotel dake Ladipo a jihar Legas suna hadiye hodar Iblis da zasu tafi da ita kasa me tsarki.
An kamasu ne ranar Laraba, 5 ga watan Yuni kamin tashin jirgin su zuwa kasa me tsarkin.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace wadanda aka kamadin, Usman Kamorudeen na da shekaru 31, sai kuma Olasunkanmi Owolabi me shekaru 46, akwai kuma Fatai Yekini me shekaru 38, sai Ayinla Kemi.me shekaru 34.
Yace an kwace dauri 200 na hodar Iblis din daga hannun wadanda ake zargi.
Mutane aun nutse a ruwa yayin da suka shiga jirgin ruwa dan tserewa harin 'yan Bindiga a garin Gurmana dake karamar hukumar Shirori jihar Naija.
Yawanci idan maharan suka kai hari, mutane kan tsere zuwa wani tsibiri har sai kura ta lafa kamin su koma gidajensu.
Mutanen daai sun tserene ranar Laraba.
Saidai ranar Alhamis, yayin da suke dawowa daga kan tsibirin da suka samu mafaka, mutane 4 sun mutu, bayan da jirgin ruwan da suke ciki yayi hadari.
Hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta bayyana cewa an samu hadarin jirgin kasan dalilin satar karafan dake rike titin jirgin.
Hakan ya haddasa aka dakatar da jigilar jirgin ranar Alhamis na dan wani lokaci dan cire jirgin da ya samu matsalar.
Saidai me magana da yawun hukumar, Yakub Mahmood ya bayyana cewa duk wanda ya riga ya sayi tikitin jirgin, zai iya amfani dashi har nan da zuwa sati biyu masu zuwa.
Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hajji
… don Allah a yada (sharing) domin amfanar wadanda ba su samu damar zuwa aikin Hajji ba.An karbo Hadisi daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce: ranar daya ga watan zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya gafarta wa Annabi Adam (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) Zai gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da Shi..(2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) Ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan rana yana da lada kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada ..(3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) Ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai karbi adduo’in sa..(4...