Saturday, December 6
Shadow
Majalisar Dattijai Ta amince da kirkiro karin Jiha daya a Yankin Inyamurai dan suzo daidai da sauran Yankunan Najeriya

Majalisar Dattijai Ta amince da kirkiro karin Jiha daya a Yankin Inyamurai dan suzo daidai da sauran Yankunan Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa Kwamitin majalisar Dattijai dake aiki kan gyaran kundin tsarin Mulki ya amince da samar da savuwar Jiha a yankin Inyamurai. Idan aka kirkiro wannan jiha, yankin na Inyamurai zai zamo daidai da sauran yankunan kasarnan watau suma zasu zamana suna da jihohi 6 kenan. A halin yanzu dai yankin na Inyamurai sune kadai yankin dake da Jihohi 5 kadai watau Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo
Karya ake mana bama kera makamin kare dangi>>Inji Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria

Karya ake mana bama kera makamin kare dangi>>Inji Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria

Duk Labarai
Rahotanni daga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria jihar Kaduna sun musanta labaran dake cewa jami'ar na kera makamin kare dangi. Daraktan hulda da jama'a na jami'ar, Awwal Umar ne ya bayyana haka inda yace babu kanshin gaskiya a Bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta. Bidiyo dai ya rika yawo a kafafen sada zumunta inda aka rika cewa, Jami'ar ta ABU na kera makamin kare dangi bisa hadin kan kasar Pakistan. Saidai jami'ar ta fito ta musanta wannan ikirari.
Wata Sabuwa: Ana zargin Tonon Sililin da Janar Christopher Musa yawa wasu sojoji da hannu a matsalar tsaro, da kuma kalaman da yayi na cewa Talauci da Yunwa da rashin aikin yi na kara rura wutar matsalar ne suka sa aka saukeshi daga mukaminsa

A jiya ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanar da sauke Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Shugaban sojojin Najeriya. Saidai rade-radin na yawo cewa, Saukeshin na da alaka da siyasa. Domin a baya ya bayyana cewa akwai wasu sojoji dakewa kokarin Gwamnati na kawo karshen matsalar tsaron zagon kasa. Hakanan ya roki gwamnati ta kawo karshen matsalar Yunwa, Talauci da rashin aikin yi wanda yace suna taimakawa rura wutar matsalar tsaro a Najeriya. https://twitter.com/Edrees4P/status/1981856038585610540?t=LQsIPBwiNJxNfXZmcFOkSQ&s=19
Kuma Dai: Bayan sauke shuwagabannin tsaro da shugaba Tinubu yayi jiya, za kuma a tursasawa Wasu manyan Janarorin soja 60 ajiye aiki

Kuma Dai: Bayan sauke shuwagabannin tsaro da shugaba Tinubu yayi jiya, za kuma a tursasawa Wasu manyan Janarorin soja 60 ajiye aiki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa akwai karin sojoji da zasu bar aiki a Najeriya bayan da shugaba Tinubu ya sauke shuwagabannin tsaron a jiya. Rahoton wanda Daily Trust ta kawo yace manyan sojoji dake sama da sabbin sojojin da aka baiwa mukaman shugabancin gidan sojan dole su ajiye aiki. Rahoton yace dama haka tsarin aikin gidan sojan yake dan a ci gaba da samun da'a da yiwa na gaba biyayya. Hakan na zuwane sati daya bayan da rahotanni suka ce an yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.
Kalli Bidiyon: Yanda Saurayi dan Kaduna ya kai Budurwarsa ‘yar Kano suka ci tsire suka kuma yi sayayya amma ya tsere ya barta

Kalli Bidiyon: Yanda Saurayi dan Kaduna ya kai Budurwarsa ‘yar Kano suka ci tsire suka kuma yi sayayya amma ya tsere ya barta

Duk Labarai
Wannan wata 'yar Kano ce da saurayinta ya kaita wajan sayayya suka ci tsire kuma suka sayi kaya amma da aka zo biyan kudi sai ya tsere. Daga baya dai sai wayarta aka kwace a shagon. Ta bayyana cewa Samarin Kaduna akwai yaudara. https://www.tiktok.com/@mix_muhammad/video/7564905876197264660?_t=ZS-90qH1uLi8DB&_r=1
Kalli Bidiyo: Naira Miliyan 2 Soja Boy yake baiwa ‘yan mata suna rawa dashi a wakokinsa na Badhala

Kalli Bidiyo: Naira Miliyan 2 Soja Boy yake baiwa ‘yan mata suna rawa dashi a wakokinsa na Badhala

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Naira Miliyan 2 Soja Boy ke baiwa wasu daga cikin 'yan matan da yake rawar badala dasu a cikin bidiyonsa. 'Yar Fim Mashahuriyace ta bayyana haka a wani Bidiyo data saki inda tace ya baiwa Eshat Aminu amma tace tafi karfin hakan. Ana dai ganin Soja Boy yana rawa da mata kala-kala inda a wasu lokutan yake kama hannunsu ko kuma ya rika rungumarsu. https://www.tiktok.com/@officialsojaboyy/video/7564851359137172756?_t=ZS-90qGa2OqrVB&_r=1
Kalli Bidiyon:Yanda dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya gaisa da diyar tsohon shugaban kasa, Zahra Buhari, sannan ya Sumbhachi kanwarta

Kalli Bidiyon:Yanda dan Shugaban kasa, Seyi Tinubu ya gaisa da diyar tsohon shugaban kasa, Zahra Buhari, sannan ya Sumbhachi kanwarta

Duk Labarai
Bidiyon dan shugaban kasa, Seyi Tinubu yana gaiwa da diyar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sannan ya sumbaci daya ya jawo cece-kuce sosai. A Bidiyon, an ga Yusuf Buhari a zaune inda Seyi ya Mikawa Zahara Buhari hannu suka gaisa sannan ya zagaya ya sumbaci 'yar uwarta. Lamarin dai ya jawo zazzafar Muhawara inda wasu ke cewa masu kudi ba ruwansu da haramun wajan gaisawa da mata. https://www.tiktok.com/@abkblogg/video/7564937419531799815?_t=ZS-90qCo7nGDZZ&_r=1
Lokacin da zan sauka daga Mulki, An so in dauko Nasiru El-Rufai a matsayin magajina, amma nace ban yadda ba sai ya Kara hankali tukuna>>Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

Lokacin da zan sauka daga Mulki, An so in dauko Nasiru El-Rufai a matsayin magajina, amma nace ban yadda ba sai ya Kara hankali tukuna>>Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, a lokacin da ya so sauka daga Mulki, an bashi shawarar ya dauko Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin magajinsa. Yace amma a wancan lokacin yaki yadda da wannan shawarar. Yace dalili kuwa shine yace Sai El-Rufai ya kara hankali. Yace da wanda ya bashi shawarar ya ga irin ayyukan El-Rufai yake yi shine ya sake zuwa ya sameshi yace lallai ya yadda da maganarsa. El-Rufai dai yayi ministan Abuja a zamanin mulkin Tsohon shugaban kasar.