Saturday, December 6
Shadow
‘Yan Damfarar Yanar Gizo(Yahoo Boys) mutanene masu Bhasiyra bai kamata ana Zhaginsu ba, kamata yayi a jawo su jiki>>Inji Peter Obi

‘Yan Damfarar Yanar Gizo(Yahoo Boys) mutanene masu Bhasiyra bai kamata ana Zhaginsu ba, kamata yayi a jawo su jiki>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 a Labour Party Peter Obi ya bayyana cewa, masu damfarar yanar gizo, Wanda aka fi sani da Yahoo Boys mutanene masu basira. Yace ida aka kula dasu aka canja musu tunani zasu amfani ci gaban kasa. Ya bayyana hakane a Onitsha Jihar Anambra ranar Asabar. Ya yi kiran da a daina karfafa cin hanci da Rashawa a Najeriya.
Subhanallahi: Kalli Bidiyon inda wani Dan Dariqa ya jawo cece-kuce sosai bayan da yayi Ikirari Sheikh Tijjani yafi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)

Subhanallahi: Kalli Bidiyon inda wani Dan Dariqa ya jawo cece-kuce sosai bayan da yayi Ikirari Sheikh Tijjani yafi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)

Duk Labarai
Wani dan Darika ya jawo Muhawara me zafi sosai bayan da yayi ikirarin cewa Sheikh Tijjani Yafi Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya bayyana cewa, su akan karantarwar da aka dorasu kenan amma idan ya gane gaskiya zai canja https://www.tiktok.com/@buharimandemgy/video/7565017487750876423?_t=ZS-90r74ueAimG&_r=1
Dalibai a jami’ar Maradi University dake kasar Nijar sun Rhushye Katangar da aka gina dan raba bangaren maza dana mata a jami’ar

Dalibai a jami’ar Maradi University dake kasar Nijar sun Rhushye Katangar da aka gina dan raba bangaren maza dana mata a jami’ar

Duk Labarai
Rahotanni sun ce dalibai a jami'ar Maradi University dake kasar Nijar sun rushe katangar da aka gina dan raba bangaren maza dana mata a jami'ar. Hukumomin makarantar sun so raba bangaren maza dana mata a jami'ar amma daliban suka ki amincewa da wannan yunkuri. Lamarin har sai da ya kai ga Sarkin Maradi ya je makarantar dan ganewa idansa abinda ke faruwa. https://twitter.com/UstazofArewa/status/1982054687810723882?t=HaSmj4meZc6sQtQzc4vzuA&s=19
Kalli Bidiyo: Rawar da Tauraruwar fina-finan Hausa, Hannatu Bashir ta yi ta jawo cece-kuce sosai inda wasu ke cewa ba girman ta bane

Kalli Bidiyo: Rawar da Tauraruwar fina-finan Hausa, Hannatu Bashir ta yi ta jawo cece-kuce sosai inda wasu ke cewa ba girman ta bane

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Hannatu Bashir ta jawo cece-kuce sosai bayan wani Bidiyon rawa data wallafa a shafinta na Tiktok inda wasu ke ta mata comment cewa ba girmanta bane. Da farko ta fara amsawa masu mata comment da zagi amma daga baya ta kyalesu. Kalli Bidiyon anan: https://www.tiktok.com/@hannatubashir3/video/7563720873077673234?_t=ZS-90r3NCdVfPc&_r=1
‘Yansanda sun kama Jarumar Fina-Finan Hausa, Khadija MaiNumfashi an tafi da ita Legas

‘Yansanda sun kama Jarumar Fina-Finan Hausa, Khadija MaiNumfashi an tafi da ita Legas

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Legas na cewa 'yansanda sun kama jarumar fina-finan Hausa, Khadija MaiNumfashi. Rahoton yace kamen da aka mata na da alaka da wani fada da suka yi da kawarta inda kalaman da ta yi akan wani Kabiru legas suka watsu a kafafen sada zumunta. Rahoton yace Kabiru Legas dinne ya kai korafi wajan 'yansanda wanda dalilin hakan yasa aka kama jarumar. Saidai wata kungiyar 'yan Fim ta nemi a sako Khadija MaiNumfashi saboda a cewarsu, an take hakkinta kuma marainiyace sannan ta shiga harkar fim ta hanyar data dace. https://www.tiktok.com/@fahadkabirmaitata/video/7565248236512873749?_t=ZS-90qzvNVmMoz&_r=1 https://www.tiktok.com/@aminujtown87/photo/7565156058180652309?_t=ZS-90r2yso25Ev&_r=1
Majalisar Dattijai Ta amince da kirkiro karin Jiha daya a Yankin Inyamurai dan suzo daidai da sauran Yankunan Najeriya

Majalisar Dattijai Ta amince da kirkiro karin Jiha daya a Yankin Inyamurai dan suzo daidai da sauran Yankunan Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa Kwamitin majalisar Dattijai dake aiki kan gyaran kundin tsarin Mulki ya amince da samar da savuwar Jiha a yankin Inyamurai. Idan aka kirkiro wannan jiha, yankin na Inyamurai zai zamo daidai da sauran yankunan kasarnan watau suma zasu zamana suna da jihohi 6 kenan. A halin yanzu dai yankin na Inyamurai sune kadai yankin dake da Jihohi 5 kadai watau Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo
Karya ake mana bama kera makamin kare dangi>>Inji Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria

Karya ake mana bama kera makamin kare dangi>>Inji Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria

Duk Labarai
Rahotanni daga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria jihar Kaduna sun musanta labaran dake cewa jami'ar na kera makamin kare dangi. Daraktan hulda da jama'a na jami'ar, Awwal Umar ne ya bayyana haka inda yace babu kanshin gaskiya a Bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta. Bidiyo dai ya rika yawo a kafafen sada zumunta inda aka rika cewa, Jami'ar ta ABU na kera makamin kare dangi bisa hadin kan kasar Pakistan. Saidai jami'ar ta fito ta musanta wannan ikirari.