Saturday, April 25
Shadow
Hotuna: Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta girbe shukar data yi a gonarta dake fadar shugaban kasa

Hotuna: Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta girbe shukar data yi a gonarta dake fadar shugaban kasa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta nuna yabanyar data girbe daga gonarta dake fadar shugaban kasa.
An samu banbancin ra’ayi: Yayin da Kwankwaso yace masu zàngà-zàngà su bari sai lokacin zabe su canja wanda basu so, Abba Gida-Gida yace yana goyon bayan zàngà-zàngàr kuma ma zai iya shiga a yi dashi

{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamnatin jihar Kano, a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da goyon bayan masu zanga-zangar kan tsadar rayuwa. Gwamnan da kansa ne ya bayyana hakan a wajan wani taro na masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Laraba a Kano. Gwamnan yace muddin za'a yi zàngà-zàngàr cikin tsari ba tashin hankali zai karbi masu zanga-zangar a fadar gwamnati. Yace idam suna so ma zai shiga shima a yi dashi. Gwamnan yace kundin tsarin Mulkin Najeriya ya bayar da damar yin zanga-zangar. Saidai wannan ra'ayi nasa ya sh...
Dan kunar bakin wake da ya tayar da Bàm ya kàshe mutane 19 a jihar Borno

Dan kunar bakin wake da ya tayar da Bàm ya kàshe mutane 19 a jihar Borno

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Borno na cewa, akalla mitane 19 ne suka mutu,wasu da dama suka jikkata bayan harin bam da dan kunar bakin wake yakai akan kauyen Kawuri dake karamar hukumar Konduga ta jihar. Hakan na zuwane kasa da kwana daya bayan da bam ya tashi da wata mota ya kashe wani akawu dake aiki da karamar hukumar Damboa. Hakanan a baya ma bamabamai na kunar bakin wake sun tashi a karamar hukumar Gwoza inda mutane akalla 30 suka mutu wasu 100 suka jikkata. Jami'an tsaro sun fitar da sanarwar kiyaye kowane irin taron mutane a yanayin da ake ciki.
Da Duminsa: Babbar Kotu a Abuja ta Haramta Zàngà-zàngà

Da Duminsa: Babbar Kotu a Abuja ta Haramta Zàngà-zàngà

Duk Labarai
Wata babbar kotu dake babban birnin tarayya, Abuja ta haramta yin zanga-zanga. Kotun tace ba'a amince wani dan zanga-zanga ya hau kan titin babban birnin tarayya Abuja ba da sunan zai yi Zàngà-zàngà. Ministan Abuja, Nyesome Wike ne ya gabatar da wannan korafi a gaban kotun. A baya dai masu zanga-zangar sun nemi a basu filin Eagle Square dan amfani dashi wajan gudanar da gangaminsu amma hukumomi suka kiya. A yanzu masu zanga-zangar sun bayyana cewa ko an yadda ko ba'a yarda ba zasu yi amfani da filin.
Ana harbi ko aka kàshe mutum daya zamu ajiye duk wasu bukatu zamu koma neman sai Tinubu ya sauka daga mulki>>Inji Masu Zàngà-zàngà

Ana harbi ko aka kàshe mutum daya zamu ajiye duk wasu bukatu zamu koma neman sai Tinubu ya sauka daga mulki>>Inji Masu Zàngà-zàngà

Tsaro
Matasa masu shirin fita Zàngà-zàngàr tsadar rayuwa sun gargadi hukumomi kan cewa kada a sake a harbi ko a kashe ko da mutum daya a cikinsu. Sunce muddin aka yi hakan, to lallai zasu ajiye duk wasu bukatunsu su koma neman sai Bola Ahmad Tinubu ya sauka daga mulki. Daya daga cikin wakilan kungiyar, Damilare Adenola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Ya kara da cewa ba zasu bari jinin 'yan uwansu ya zuba a banza ba.
Sheikh Alkashnawy Ya Kammala Karatun Digirinsa Na Biyu Da Sakamako Mafi Daraja A Jami’ar Annadha Dake Ƙasar Niger

Sheikh Alkashnawy Ya Kammala Karatun Digirinsa Na Biyu Da Sakamako Mafi Daraja A Jami’ar Annadha Dake Ƙasar Niger

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya daga jihar Katsina Sheikh. Mal. Ismail Zakariya Alkashnawy, ya kammala karatun sa na digirin digirgir (PhD) a ɓangaren Larabci a jami'ar Annahdha International University da ke Niamey a ƙasar Niger. Haziƙin Malamin Dr. Alkashnawy, ya nuna hazaƙa sosai, yayin da ya kammala karatun da mataki mafi daraja (First Class).
Hukumar ‘yansanda tace duk wani dansanda dake hutu ya koma bakin aiki saboda zàngà-zàngàr gobe kuma kada dansandan daya sha giya dan kada yayi tambele a wajan Zàngà-zàngàr

Hukumar ‘yansanda tace duk wani dansanda dake hutu ya koma bakin aiki saboda zàngà-zàngàr gobe kuma kada dansandan daya sha giya dan kada yayi tambele a wajan Zàngà-zàngàr

Tsaro
Hukumar 'yansandan Najeriya ta bayyana cewa, duk wani dansanda dake hutu ya koma bakin aiki. Wannan mataki na zuwane yayin da ake kusa da fara Zàngà-zàngàr kukan tsadar rayuwa a Najeriya. Hakanan sanarwar ta bayyana cewa, kada a sake a samu wani dansanda da shan giya dan kada yayi tambele a wajan zanga-zangar. Hakanan an bukaci duka 'yansanda dasu saka kayan aiki cikakku a goben kuma an dakatar da kowane irin hutu.