Soyayya wata ji ce mai zurfi ta ƙauna da shauki, girmamawa, aminci, fata na Alheri, Fatan samun wani abu wadda mutum yake yi ga wani ko wani abu.
Soyayya na iya zama a tsakanin ma’aurata, abokai, iyaye da ‘ya’ya, ko kuma ga wani abu kamar sana’a ko ƙasa.
Ga wasu daga cikin nau’ikan soyayya:
Soyayyar Ma'aurata: Wannan ita ce soyayya tsakanin mutum da masoyinsa, wanda sun riga sun yi aure ta yanda kowane na son kowa kuma ana girmama juna da rufawa juna asiri, da amfanar juna, da yaye ma juna damuwa.
Soyayyar Iyaye da 'Ya'ya: Wannan ita ce soyayyar da ke tsakanin iyaye da 'ya'yansu, wadda ke da zurfi kuma mara yankewa. Ita wannan soyayya itace kusan makura wadda bata da wani sharadi.
Soyayyar Abokai: Wannan ita ce soyayyar da ke tsakanin abokai, wadda take bisa amana, goyon ...