Tuesday, March 10
Shadow
Kalli Hotuna: Yanda ‘yan B0k0 Hqrqm suka yanka mutane 7 a Bassa da Erena dake jihar Naija

Kalli Hotuna: Yanda ‘yan B0k0 Hqrqm suka yanka mutane 7 a Bassa da Erena dake jihar Naija

Jihar Naija, Tsaro
Rahotanni daga Bassa da Erena a jihar Naija na cewa mayakan kungiyar B0k0 Hqrqm sun kai mummunan hari a yankin. Majiyar Hutudole tace an kai harinne a garin Makuba Lantan Bakin Kogi Bassa inda aka kashe mutane 7 ta hanyar yi musu yankan rago. Harin ya farune a jiya, Alhamis kamar yanda majiyar tamu ta tabbatar. Masu fada a ji a yankin sun nemi mahukunta da su kaiwa mutanen yankin musamman wadanda suka rasa muhallansu dauki. Mun samu hoton kan daya daga cikin mutanen da aka yanke, Allah ya kyauta.
Kadan ma kuka gani: Gwamnatin Tinubu tace matakan tada komadar tattalin arziki da zata dauka nan gaba sun fi wanda aka gani a baya tsanani

Kadan ma kuka gani: Gwamnatin Tinubu tace matakan tada komadar tattalin arziki da zata dauka nan gaba sun fi wanda aka gani a baya tsanani

Siyasa
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, matakan tada komadar tattalin arziki da zata dauka nan gaba, sai sun fi na baya tsanani. Hakan na fitowane daga bakin Ministan yada labarai, Muhammad Idris. Ya kara da cewa daukar wadannan matakai ya zama dole dan canja fasalin Najeriya ta yanda zata ci gaba ta fannin tattalin arziki. Ya bayyana hakane a wani rahoto da aka wallafa a wata jaridar kasar Ingila. Minista Muhammad Idris ya kara da cewa, Shugaba Tinubu gwarzo ne dan kuwa ya dauki matakan da shuwagabannin da suka gabata, suka kasa daukar irinsu. Babban matakin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta dauka wanda ya damu al'ummar kasar shine cire tallafin man fetur wanda ya yi sanadiyyar jefa mutane cikin halin kaka nikayi. Hakanan gwamnatin Tinubun ta kuma cir...
Da Duminsa: Fadar Shugaban kasa ta musanta cewa, Ministan kudi ya gabatar da Naira Dubu Dari da biyar(105,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Da Duminsa: Fadar Shugaban kasa ta musanta cewa, Ministan kudi ya gabatar da Naira Dubu Dari da biyar(105,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
Rahotannin da muke samu na cewa, fadar shugaban kasa ta musanta wasu bayanai dake cewa ministan kudi ya gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Naira Dubu dari da biyar(105,000) a matsayin mafi karancin Albashi. Babban me baiwa shugaban kasa Shawara kan harkar yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta. Ga sakonsa kamar haka: "The Honorable Minister of Finance and coordinating minister of the economy, Wale Edun has not proposed N105,000 minimum wage. The contrary story being disseminated is false.”
Ji matakin da Kasar Iran tace zata dauka akan kasar Israela bayan da Israelan ta sake kai harin da ya kashe sojan Iran din

Ji matakin da Kasar Iran tace zata dauka akan kasar Israela bayan da Israelan ta sake kai harin da ya kashe sojan Iran din

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
A jiyane dai muka samu rahoton cewa, kasar Israela ta kai wani mummunan hari a garin Aleppo dake kasar Syria wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa ciki hadda me baiwa kasar Iran shawara akan harkar soji. A martanin kasar Iran kan harin, Kwamandan dakarun IRGC na kasar Salami ya bayyana cewa, Israela ta saurari harin ramuwar gayya. A baya dai, irin wannan harin ne Israela ta kai kan ginin ofishin jakadancin Iran wanda ya kashe wasu janarorin soja na Iran. Hakan yayi sanadiyyar harin ramuwar gayya akan Israela da Iran ta yi wanda ya baiwa Duniya mamaki kuma ya tayar da hankalin kasar Israela. A wannan karin dai ba'a san wane irin harin ramuwar gayyane Iran zata kai akan Israela ba.
Na bauta wa Kaduna da gaskiya kuma ina alfahari da hakan – El-Rufai

Na bauta wa Kaduna da gaskiya kuma ina alfahari da hakan – El-Rufai

Kaduna, Siyasa
Kwamitin da Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa kan nazari game da kuɗaɗen da aka kashe a gwamnatin da ta gabata a jihar ya miƙa sakamakon bincikensa a yau. Cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar har da na buƙatar hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i. Lokacin da ya gabatar da rahoton a ranar Laraba, shugaban kwamitin, Henry Zacharia ya ce an gano cewa akasarin kuɗin bashin da jihar ta karɓa a zamanin mulkin El-Rufa'i, ko dai ba a yi amfani da su kan abin da aka ciyo bashin domin su ba ko kuma ba a bi ƙa'ida wajen cin bashin ba. Da yake karɓar rahoton, shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman ya ce kuɗi naira biliyan 423 ne suka zurare a lokacin gwamnatin El-Rufa'i tare da jefa jihar cikin ƙangin bashi. Sai dai tsohon gwamnan ya ce binciken da...
A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

Siyasa
Ministan kudi, Wale Edun a yau ne ake sa ran zai gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sabon daftarin mafi karancin Albashi. Ko da ita kanta kungiyar kwadago, NLC ta dage zaman ta da gwamnatin tarayya sai yau din Alhamis da ake tsammanin sake ganin nawane gwamnatin tarayyar zata kara akan Naira dubu 60 da a baya NLC din ta ki amincewa da ita a matsayin mafi karancin Albashi. Saidai a rahotanni na baya, kungiyar TUC tace ba zata amince da Kari dan kadan ba akan Naira dubu 60 din. Sannan kuma tace ba ta dage akan sai an biyata Naira Dubu 400 ba, kawai dai abinda take nema shine a biya albashi da zai wadaci ma'aikaci.