Wednesday, March 11
Shadow
Yanzu-Yanzu:Kasar Faransa ta hana kasar Yahudawan Israela zuwa bikin nuna makamai saboda kisan Falas-dinawa

Yanzu-Yanzu:Kasar Faransa ta hana kasar Yahudawan Israela zuwa bikin nuna makamai saboda kisan Falas-dinawa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
A karin farko, Kasar Faransa ta zama kasar Turai ta farko data kakabawa kasar Israela takunkumi kan kisan kiyashin da takewa falasdinawa. Faransar ta hana kasar Israela hakartar bikin nuna makamai da za'a yi ranar 17 zuwa 21 ga watan Yuli. Bikin dai shine bikin nuna ko kuma bajakolin makamai mafi girma a Duniya wanda aka sakawa sunan Eurosatory 2024. Wannan mataki na zuwane bayan da kasar Israela ta ki bin umarnin kotun Duniya na daina kashe Falasdinawa. Hakanan kasashen Duniya da yawa na ta Allah wadai da kasar kan kisan da takewa Falas-dinawan. Sannan kuma wannan mataki zai iya zama gargadi ga kasar ta Israela ta canja salo ko kuma akwai yiyuwar wasu sauran kasashen Turawa suma su saka mata takunkumo.
Kalli hoton Maryam Yahya da Masoyanta ke sam barka suna cewa ta ciko ta yi Bulbul

Kalli hoton Maryam Yahya da Masoyanta ke sam barka suna cewa ta ciko ta yi Bulbul

Kannywood, Maryam Yahya
Tauraruwar Fina-finan, Maryam Yahya kenan a wannan kayataccen hoton nata da masoyanta da dama suka yaba. Maryam ta saka hoton a shafinta na Instagram inda aka ganta zaune a wani gidan sayar da abinci. Saidai masoyanta da yawa hakalinsu ya kai ne kan kibar da Maryam ta yi. Da yawa dai sun yaba da Masha Allah, inda wani yace: "Kin cika kin yi kyau, Masha Allah" "Shi kuwa wani cewa yayi, anya a wannan harkar babu kari?" "Wani kuma cewa yayi, Kai Maryam Gaskiya kin ciko"
Ba lallai sai kana da Karatun Bo-ko bane sannan zaka yi nasara a rayuwa>>Inji Shugaban kasar Ingila

Ba lallai sai kana da Karatun Bo-ko bane sannan zaka yi nasara a rayuwa>>Inji Shugaban kasar Ingila

Siyasa
Britain's Prime Minister and Conservative Party leader Rishi Sunak reacts after bowling a ball during a Conservative general election campaign event at the Market Bosworth Bowls Club in Market Bosworth, central England, on May 28, 2024. (Photo by Alastair Grant / POOL / AFP) Firai kinistan Ingila, Rishi Sunak ya bayyana cewa, ba lallai sai mutum na da karatun boko bane zai yi nasara a rayuwa. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta. Screenshot Saidai lamarin ya jawo cece-kuce sosai inda wasu suka goyi bayansa, wasu kuma suka ce hakan ba daidai bane.
Gwamnatin tarayya ta samo bashin Dala Miliyan dari biyar($500 million) dan gyaran wutar Lantarki

Gwamnatin tarayya ta samo bashin Dala Miliyan dari biyar($500 million) dan gyaran wutar Lantarki

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan dari biyar, $500 million dan karfafawa kamfanonin rarraba wutar lantarki na kasa. Hukumar BPE tace an ciwo bashinne dan magance matsalolin da suka mamaye kamfanonin rarraba wutar lantarki na kasarnan. Wakiliyar hukumar BPE, Amina Othman ce ta bayyana haka inda tace za'a yi amfani da kudadenne wajan sayo mitocin wuta da sauransu.
Hoto: Dansanda ya kash-she wannan matashin saboda yaki bashi cin hancin Naira 200

Hoto: Dansanda ya kash-she wannan matashin saboda yaki bashi cin hancin Naira 200

Tsaro
Ana zargin 'yansanda sun kashe wannan mutumin me shekaru 40 a titin Azikoro Road dake Yenagoa ta jihar Bayelsa saboda yaki bada cin hancin Naira dari biyu(200). Rahoto ya bayyana cewa, mutumin me suna Benalayefa Asiayei yana kan hanyarsa ta komawa gidane daga wajan aiki da misalin karfe 8 na yamma yayin da aka kasheshi. Bayan da 'yansandan suka kasheshi, sun tsere daga wajan amma wani daga cikin shaidun abinda ya faru sun dauki hotunansu. Kakakin 'yansandan jihar, Musa Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin kuma yace sun tantance wanda ake zargi. Iyalan mamakin sun ce suna neman adalci.
Kalli bidiyo:Ana Allah wadai da yanda “Dan Ganduje” ya gaisa da shugaban kasa Tinubu, wasu na cewa bashi da tarbiyya

Kalli bidiyo:Ana Allah wadai da yanda “Dan Ganduje” ya gaisa da shugaban kasa Tinubu, wasu na cewa bashi da tarbiyya

Kano
Wani tsohon bidiyon haduwar Shugaban kasa, Bola Ahmad da shugaban jam'iyyar APC, Dr. Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana a shafukan sada sumunta. A bidiyon, an ga wani matashi wanda aka bayyana da cewa, dan tsohon gwamnan Kanon ne, Ganduje wanda ya gaisa da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Saidai yanayin gaisawar tasu ta jawo cece kuce saboda bai durkusa ba hannu kawai ya bashi suka gaisa. https://www.tiktok.com/@weddings_and_cruise/video/7367361316601728262?_t=8mo5NJgw9kE&_r=1 A al'adar yarbawa dai har kwanciya ana yi wajan gaishe da manya.