ALLAHU AKBAR: Ƙabarin Marigayi Shêikh Dahiru Usman Bauchi Kenan, Wanda Ya Rasu A Ranar 27 Ga Watan Nuwamba, Shekarar Nan Ta 2025.
Allah ya gafarta masa.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Najeriya zata fara kera sassan jirgin sama.
Shugaban ta bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar kan jiragen sama na kasa da kasa a Najeriya.
Sakataren Gwamnati, George Akume ne da ya wakilci shugaban kasar a wajan taron ya bayyana haka.
Ya bayyana cewa kudin shigar Najeriya daga bangaren harkokin jiragen sama zasu kai Dala biliyan $2.56 nan da shekarar 2029.
Wannan Bidiyon wani Barawo ne da ya sace motar Tirela guda zai gudu.
Saidai wani Hazikin soja ya harbi tayar motar inda hakan yayi sanadiyyar faduwar motar.
Daga baya dai an kama barawon.
https://twitter.com/SaharaReporters/status/1995953732409061423?t=Lftm3pyrAExMQK365Qb8LQ&s=19
Wannan wata matar aure ce da aka yi garkuwa da ita a Abuja.
Tun ranar Lahadi data shiga motar once chance a Lugbe ba'a kara jin duriyarta ba sai dai suka kira suka ce a tura musu Dubu 50
Bayan an tura musu sai suka ce suna neman Miliyan 50, mijin yace bai da kudin.
Ya je wajan 'yansanda amma sai yawo ake msa da hankali babu alamar zasu taimaka masa su ceto matar tasa.
https://twitter.com/OzorNdiOzor/status/1995818456147496977?t=UVdq0SIrgGtF8WABwxM7SA&s=19
Bidiyon wani fada daya kaure tsakanin wasu sojoji da wani dansanda a Jos babban Birnin jihar Filato ya dauki hankula a kafafen sada zumunta
An ga yanda sojojin suka kwace Bindigar dansandan.
Sannan wasu rahotanni sun ce sun kuma lakada masa na jaki.
https://twitter.com/General_Somto/status/1995745568430195194?t=aI2Krr87XuBEHQiurxIgDA&s=19
https://twitter.com/General_Somto/status/1995920361846604155?t=MH9hRN7bF7-VytrMP0ySsQ&s=19
Tauraruwar Kannywood, Hadiza Gabon ta sabunta dakin daukar shirye-shiryen hirar da take da mutane inda ta saka hotunan manyan jarumai amma babu hoton Adam A. Zango.
Lamarin ya dauki hankula inda aka ga mutane nata mayarwa Hadiza Gabon da raddi kala-kala inda da yawa ke nuna mata rashin dacewar hakan.
https://www.tiktok.com/@prince_abdool/video/7578566841547640072?_t=ZS-91taL7CYyvp&_r=1
https://www.tiktok.com/@hadizaaliyugabon/video/7578602441503952150?_t=ZS-91tZCAa9pGj&_r=1
https://www.tiktok.com/@umarpitykhalid0/video/7579216257484868871?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7579216257484868871&source=h5_m×tamp=1764709276&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wL...
Rahotanni sun bayyana cewa, Gfresh zai mayar da matarsa ko ma ya mayar da ita.
Hakan na zuwane bayan da aka ga matar tasa a Tiktok Live din Gfresh din kuma har ma ya dorata a babban allo.
An jima tana wa masu musu bakin ciki habaici ita da mijin nata.
Wasu dai da suka shigar mata fadan da ta yi da Gfresh an gansu suna fadin ta koma da wuri ya kamata ta jawa Gfresh din aji.
https://www.tiktok.com/@mrs.gfresh/video/7579053809305980180?_t=ZS-91tVrYF4hjV&_r=1
Wannan wata me ciki ce data shiga wani shago da niyyar sayayya amma sai ta saci famfas din yara zata tsere.
Allah ya taimaki me shagon ya ganta shine ya tareta.
A Bidiyon da aka mata, an ganta a durkushe da famfas din data sata akanta.
https://twitter.com/Elorm_Hood/status/1995538828749140475?t=CaNaai1JkjAJ--dhI1sz6A&s=19
Wadannan wasu motoci ne da aka gani a daji babu kowa a cikinsu.
Rahotanni sun ce tsageran daji sun yi garkuwa da mutanen cikin motocin.
Lamarin dai ya farune akan titin Aba zuwa Owerri dake yankin Inyamurai.
https://twitter.com/IkukuomaC/status/1995844510740611583?t=ScTai0g847Gyd5n4DC7fJg&s=19