Wednesday, October 7
Shadow
Jihar Kano ta zo ta daya a Najeriya wajan yawan daliban da suka ci 5 credit a jarabawar NECO

Jihar Kano ta zo ta daya a Najeriya wajan yawan daliban da suka ci 5 credit a jarabawar NECO

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Jihar Lagos ta zo ta daya a Najeriya wajan yawan daliban da suka samu 5 credit a jarabawar NECO ciki hadda Turanci da Lissafi. Dalibai 74,413 ne suka samu 5 credit a jarabawar NECO daga jihar Kano wanda hakan yasa Kano ta zo ta daya a Najeriya wajan yawan daliban da suka ci jarabawar. Jihar dake biye mata itace jihar Lagos dake da dalibai 72,496 sannan sai jihar Oyo dake da yawan dalibai 55,543 da suka ci jarabawar. Ko da a shekarar data gabata ma, Jihar Kano din dai itace ta zo ta daya wajan yawan daliban da suka ci jarabawar NECO. Gwamnan jihar Kano ta bakin me magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa, yana taya daliban, Malamsu da iyayensu murnar wannan nasara.
Mazan larabawa sun hanani Sakaat>>Inji Hafsat Baby

Mazan larabawa sun hanani Sakaat>>Inji Hafsat Baby

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Hafsat Baby ta bayyana cewa, Mazan Larabawa sun hanata Sakat. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo data wallafa inda aka ga wani Balarabe na lekowa cikin Bidiyon. https://www.tiktok.com/@hafsatbaby092/video/7690285168883404052?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7690285168883404052&source=h5_m&timestamp=1790592017&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7685096581537105684&share_link_id=6ab0fead-1853-4716-9491-a60260da236e&share_app_id=1233&ugbiz_name=MAIN&ug_btm=b5836%2Cb2878&a...
Wata Sabuwa: Wasu Rahotanni na bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin sayen kamfanin Sadarwa na MTN

Wata Sabuwa: Wasu Rahotanni na bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin sayen kamfanin Sadarwa na MTN

Duk Labarai
Wani Rahoto daga Sahara Reporters na cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin zama wanda ke da mafi yawan hannun jari a kamfanin sadarwa na MTN. Rahotan yace Shugaban zai sayi hannun jarinne ta hannun kamfanin Mafab Communications da IHS Towers. Sannan kuma shugaban Kamfanin MTN, Karl Olutokun Toriola ne zai saukaka kasuwancin. Sahara Reporters dai sun ce wata majiya ce daga bangaren harkar sadarwa ta sanar dasu hakan. Saidai ba'a bayyana hannun jarin na nawa shugaba Tinubu zai siya ba.
Sheikh Lawal Triumph na ta shan raddi bayan da yace duk inda Alamtara Kaifa tazo, Ila ce ke biyo baya a Qur’ani

Sheikh Lawal Triumph na ta shan raddi bayan da yace duk inda Alamtara Kaifa tazo, Ila ce ke biyo baya a Qur’ani

Duk Labarai
Sheikh Lawal Triumph yayi wani karatu inda yake cewa duk inda alamtara tazo a Qur'ani, Ila ce ke biyo bayanta. Saidai da yawa, Musamman 'yan Darika sun ta yi masa raddi masu zafi akan cewa ba gaskiya bane. https://www.tiktok.com/@shaaweuei5p/video/7690333213985639701?_r=1&_t=ZN-9A6gZwRRUby https://www.tiktok.com/@shaaweuei5p/video/7690337191280561429?_r=1&_t=ZN-9A6hL6tUTjz https://www.tiktok.com/@auntyshanmix80/video/7690316015699365141?_r=1&_t=ZN-9A6haYKRsRC
Sabon Rikici ya kunno kai a jam’iyyar NDC

Sabon Rikici ya kunno kai a jam’iyyar NDC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Sabon Rikici ya kunno kai a jam'iyyar NDC bayan da jam'iyyar tace zata fara yin rijistar membobinta kamin zabe. Me magana da yawun jam'iyyar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace za'a yi rijistarne kyauta. Saidai bangarori biyu na jam'iyyar Watau Ok Movement da Kwankwasiyya duk sunce basu yadda ba. Sun ce ba za'a sakasu cikin wadanda zasu yi rijista a jam'iyyar ta NDC ba. Shugaban Tafiyar Kwankwasiyya, Habibu Muhammad yace ko da a baya su kunyane basa yin rijistar jam'iyyar dan haka a yanzu ma ba zasu yi ba. Yace burin dai shine 'yan takararsu su yi nasara dan haka abinda zasu saka a gaba kenan. Shima shugaban Tafiyar Ok Movement, John Ughulu ya bayyana cewa ba zasu yi rijista da jam'iyyar NDC ba dan doka ta basu damar yin ku...
Gwamnatin Tarayya ta mikawa bankin Duniya kokon barar ciwo bashin dala Biliyan $1.5

Gwamnatin Tarayya ta mikawa bankin Duniya kokon barar ciwo bashin dala Biliyan $1.5

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta mikawa Bankin Duniya bukatar ciwo sabon Bashin dala Biliyan $1.5. Hakan na zuwane yayin da bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira Tiriliyan N166.79tn. A bukatar da gwamnatin ta mikawa Bankin Duniya, Najeriya tace tana neman bashinne dan bayar da tallafi ga talakawa marasa karfi da kuma Taimakawa Fannin Noma. Bashin dai Gwamnatin ta bukaci dala Miliyan $500 ne har sau 3.
Tawagar Me baiwa shugaban kasa Shawara kan harkar siyasa, Ibrahim Masari ta yi Hadari

Tawagar Me baiwa shugaban kasa Shawara kan harkar siyasa, Ibrahim Masari ta yi Hadari

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Tawagar me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar siyasa, Ibrahim Masari ta yi hadari. Hadarin ya farune a karamar Hukumar Kafur ta jihar yayin da ya je yin wata gaisuwa. Rahoton yace mutane 2 sun rigamu gidan gaskiya. Hadimin Ibrahim Masarin me amfani da sunan Wazirin Kabir Ibrahim Masari ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook kamar haka: "Innalillahi wa'innailaihir raju'u😭😭 Acikin tawagar da suka raka Alh Ibrahim Masari Ta'aziyya Dantitture Yanzu nan ansamu Hatsarin mota wasu sun rasu mutum 2 munkawo wata asibiti Allah ya jiqansu da rahama, su Kuma masu rauni Allah ya basu lapia." Da fatan Allah ya jikansu.
Matar aure, Rukayya Muhammed da Suka je ita da kwartonta otal asiri ya tonu ta yi bayani

Matar aure, Rukayya Muhammed da Suka je ita da kwartonta otal asiri ya tonu ta yi bayani

Duk Labarai
Wannan matar sunanta Rikayya Muhammad kuma matar aure ce wadda suka je Otal ita da wani Saurayinta dan sheke aya. Bayan sun kammala sai rai yayi Halinsa, Saurayin ya rigamu gidan gaskiya. Ko da ta lura da haka sai ta dauke wayarsa ta tsere. Saidai Dubunta ya cika an kamota. Tace ta ajiye lambar wayarsa da sunan safiya a wayarta. https://twitter.com/abis_fulani/status/2104326436849164631