Dan Kwallon Najeriya, Wilfred Ndidi ya dauki Hankula bayan da aka ganshi yana baiwa wata yarinya kariya daga ruwan sama.
An dauki hotonne kamin fara wasa.
Baturen Ingila, Dr. Mark Thompson wanda yanzu ya canja suna zuwa Abdullahi ya karbi Musulunci shi da matarsa.
Yace ya karanta Qur'ani ya fahimci cewa Littafi ne wanda mutum bai isa ya rubutashi ba dan haka shi da matarsa suka karbi Musulunci.
Yace ya ziyarci Makkah yayi ibada amma kuma da ya koma kasarsa, sai ya kasa samun nutsuwa.
Yace dan hakane ya sake komawa dan yayi Ibada.
A wasan da Najeriya ta buga da Mozambique a daren jiya, An ga Victor Osimhen nawa Ademola Lukman tsawa a filin wasan.
Lukman dai be biye masa ba wanda hakan yasa wasu suka rika sukar Osimhen game da lamarin.
https://twitter.com/i/status/2008282216510447942
Bayan wasan an tambayi Ademola Lukman kan cewa menene ya faru tsakaninsa da Victor Osimhen, saidai ya kayar da baki yace ba komai wasane.
https://twitter.com/i/status/2008312453608689986
Wannan amsa ds ya bayar ta dauki hankulan mutane sosai inda akai ta yaba masa.
Dr. Hussain Kano ya bayyana cewa, duk wani Ahlussunah kamata yayi ace yayi farin ciki da kama Sheikh Khalifa Sani Zaria.
Ya bayyana cewa dalili shi dan bidi'a ne.
Yace idan Abu ya samu dan Bidi'a farin ciki ake amma idan ya samu Musulmi me sabo, shi kuma jaje ake mada.
https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7592008808231210252?_t=ZS-92pW4UzN2e1&_r=1
Baffa Hotoro ya bayyana Sheikh Khalifa Sani Zaria da jami'an tsaro suka kama da cewa matsafi ne boka.
Ya bayyana hakane a martanin da yake kan zargin cewa an baiwa Malam Sheikh Khalifa Sani Zaria kudi yayi addu'a.
Ya bayyana cewa dama Allah ba zai karbi irin wannan Addu'a ba dan kuwa dan kudi aka yi ta.
https://www.tiktok.com/@zaidou1taza/video/7592001048626220344?_t=ZS-92pUvfB3gRN&_r=1
Wannan wani Ango da Amarya ne da suka dauki hankula sosai saboda salon Murnar Bikinsu da suka yi.
Bidiyonsu ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda aka rika muhawara akai.
https://www.tiktok.com/@habeebullah_image/video/7591700979289132309?_t=ZS-92pSxb6ktft&_r=1
Wannan matashin Kirista ya bayyana cewa, a kokarin neman gaskiya da yake ne ya hadu da Musulunci kuma ya musulunta.
https://twitter.com/i/status/2008060497745043698
Rahotanni sun bayyana cewa, Rikicin Jam'iyyar APC ya kara ci gaba da kazancewa inda ake cacar baki tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da sakataren jam'iyyar APC din, Ajibola Basiru.
Ajibola Basiru ya bayyana cewa, kamata yayi Wike ya sauka daga mukamin nasa saboda munanan kalaman da yayi akan jam'iyyar APC.
Wike a wajan taron da yayi a jihar Rivers yace duk wanda ke son yi musu katsalandan a siyasar jiharsu ta Rivers, zai kwashi kashinsa a hannu.
iHakan na zuwane dai yayin da rikici tsakanin Gwamnan Rivers, Simi Fubara da Wike din ke kara kazanta.
Wike ya dage cewa, Fubara ba zai tsaya takara ba a karo na biyu.
'Yan matannan da suka fito suka bayyana cewa ba zasuwa mahaifinsu addu'a ba bayan rasuwarsa sun ce mahaifiyarsu ce ta sakasu.
Sun bayyana cewa, kuma duk masu zaginsu, suna fatan Allah ya baiwa 'ya'yansu mazaje irin mahaifinsu.
https://www.tiktok.com/@fatima.yakubu54/video/7591800870786829589?_t=ZS-92pBiVULCjZ&_r=1
Yan matan dai sun dauki hankula bayan da suka bayyana suna murna da rasuwar mahaifinsu inda suka ce ya yaddasu bai musu komai ba, mahaifiyarsu ce ke wahala dasu har suka girma.
Marikiyarsu wadda 'yar uwa ce a wajan Mahaifiyarsu ta bayyana cewa, sun yi hakanne dan ya zama wa'azi ga sauran maza masu irin wannan hali.
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, akwai yiyuwar Tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan tsaro, Abubakar Badaru ,ai bar jam'iyyar APC zuwa ADC.
Rahoton yace hakan na zuwane yayin da baraka ke ci gaba da bayyana a tsakanin tsohon Ministan da magajinsa gwamna me ci na yanzu, watau Namadi.
https://twitter.com/i/status/2008108500493197502