Friday, April 3
Shadow
Mahaifiyarmu ce tasa muka fito muka yi Bidiyon akan babanmu

Mahaifiyarmu ce tasa muka fito muka yi Bidiyon akan babanmu

Duk Labarai
'Yan matannan da suka fito suka bayyana cewa ba zasuwa mahaifinsu addu'a ba bayan rasuwarsa sun ce mahaifiyarsu ce ta sakasu. Sun bayyana cewa, kuma duk masu zaginsu, suna fatan Allah ya baiwa 'ya'yansu mazaje irin mahaifinsu. https://www.tiktok.com/@fatima.yakubu54/video/7591800870786829589?_t=ZS-92pBiVULCjZ&_r=1 Yan matan dai sun dauki hankula bayan da suka bayyana suna murna da rasuwar mahaifinsu inda suka ce ya yaddasu bai musu komai ba, mahaifiyarsu ce ke wahala dasu har suka girma. Marikiyarsu wadda 'yar uwa ce a wajan Mahaifiyarsu ta bayyana cewa, sun yi hakanne dan ya zama wa'azi ga sauran maza masu irin wannan hali.
Wata Sabuwa: Ana rade-radin akwai yiyuwar tsohon Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar zai koma jam’iyyar ADC

Wata Sabuwa: Ana rade-radin akwai yiyuwar tsohon Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar zai koma jam’iyyar ADC

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, akwai yiyuwar Tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan tsaro, Abubakar Badaru ,ai bar jam'iyyar APC zuwa ADC. Rahoton yace hakan na zuwane yayin da baraka ke ci gaba da bayyana a tsakanin tsohon Ministan da magajinsa gwamna me ci na yanzu, watau Namadi. https://twitter.com/i/status/2008108500493197502
Da Duminsa: An samu Baraka a jam’iyyar APC, ji maganganu marasa dadi da Wike yake gayawa shugaban kasa

Da Duminsa: An samu Baraka a jam’iyyar APC, ji maganganu marasa dadi da Wike yake gayawa shugaban kasa

Duk Labarai
Wani Bidiyon Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana inda aka jishi yana wata barazana. An ji Wike na barazanar ne a wajan wani taron siyasa a jiharsa. Ya bayyana cewa mutum kada ya zo ya kawo musu abinda ba shi kenan ba a jihar Rivers. Wike bai fadi da wanda yake ba inda yace mutum ya tambayi abinda ya faru da wadanda suka yi yunkurin yiwa jihar Rivers kutse a baya. saidai wasu sun ce da sakataren Jam'iyyar APC yake inda wasu kuma ke cewa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake. https://twitter.com/i/status/2008170575286419869
Da Duminsa: Manchester United ta kori Ruben Amorim a matsayin kocinta

Da Duminsa: Manchester United ta kori Ruben Amorim a matsayin kocinta

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar Manchester United ta kori Ruben Amorim a matsayin kocinta. Hakan na zuwane bayan da ya kwashe watanni 14 yana matsayin kocin Kungiyar. Dangantaka ta yi tsami tsakanin dan kasar Portugal din me shekaru 40 da kungiyar a 'yan kwanakinnan. Manchester United dai a yanzu tana matsayi na 6 akan teburin Premier league. Manchester United ta sanar da Darren Fletcher a matsayin kocin wucin gadi.
Kudaden Bashin da Shugaba Tinubu ke karbowa da ‘yan Najeriya yake baiwa su yi Jari da an samu saukin Rayuwa>>Inji Peter Obi

Kudaden Bashin da Shugaba Tinubu ke karbowa da ‘yan Najeriya yake baiwa su yi Jari da an samu saukin Rayuwa>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023 data gabata, Peter Obi ya bayyana cewa, kudaden da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke karbowa Bashi, da Tallafawa 'yan Najeriya yake yi da jari da ba haka ba. Yace ana ta cewa babu kudi amma kuma gwamnati na ta kara ciwo bashi. Ya ce wadanda aka baiwa su yi jari zasu samarwa wasu aikin yi ta hakane za'a samu saukin talaucin da ake fama dashi a kasarnan. https://twitter.com/i/status/2007903277632069826