Wednesday, July 29
Shadow
Babu Alamar Abubuwa zasu yi sauki a gwamnatin Tinubu>>Inji Archbishop Nwaobia

Babu Alamar Abubuwa zasu yi sauki a gwamnatin Tinubu>>Inji Archbishop Nwaobia

labaran tinubu ayau, Siyasa
Wani babban malamin Kiristanci Archbishop Nwaobia ya bayyana cewa babu alamar lamura zasu gyaru a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. A hirar da wakilin jaridar sunnewsonline suka yi dashi, ya bayyana cewa faduwar darajar Naira akan Dalar Amurka matsala ce babba wadda ta jefa 'yan Najeriya da yawa cikin halin wahala. Yace kuma gwamnatin Tinubu ta kasa samo hanyar warware wannan matsala. Ya kara da cewa, Sam Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bata da alkibla dan ta kasa dasa tushen ci gaban Najeriya.
Kalli Hotuna: Gidan Mataimakin Shugaban kasar Najeriya ya fi na mataimakin shugaban kasar Amurka kyau

Kalli Hotuna: Gidan Mataimakin Shugaban kasar Najeriya ya fi na mataimakin shugaban kasar Amurka kyau

Duk Labarai
Gidan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima Wani abin mamaki da ya dauki hankulan 'yan Najeriya shine ganin yanda gidan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim ya fi na mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris kyau. Gidan na Mataimakin shugaban kasar Najeriya an ginashi ne akan Naira Biliyan 21 duk da cewa akwai wani gidan mataimakin shugaban kasar, a yanzu mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima gidaje biyu gareshi. A yayin da ita kuma mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris gida daya gareta. Gidan mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris. Bayan kashe Naira Biliyan 21 wajan gina sabon gidan na mataimakin shugaban kasar Najeriya da gwamnatin Tinubu ta yi ta kuma kashe Naira Biliyan 2.5 wajan gyara tsohon gidan mataimakin s...
Kalli Hotuna, Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa an kashshe mata sojoji 8 a Gazza

Kalli Hotuna, Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa an kashshe mata sojoji 8 a Gazza

Duk Labarai, Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kasar Yahudawan Israela ta bayyana cewa, an kashe mata sojoji 8 a Gazza a ci gaba da yakin da take yi da Israela. Kasat ta bayyana sunayensu kamar haka: Sergeant Ez Yeshaya Grover 20Sergeant Or Blomowitz 20Stanislav Kostarev 21Itay Amar 19Eliyahu Moshe 21Eylon Wiss 49Eytan Koplovich 28Wassim Mahmud 23
Bayan da Hadiza Gabon tasa aka kamashi, Rahama Sadau ta sa an sako Zaharaddeen Sani daga wajan ‘yansanda

Bayan da Hadiza Gabon tasa aka kamashi, Rahama Sadau ta sa an sako Zaharaddeen Sani daga wajan ‘yansanda

Duk Labarai, Hadiza Gabon, Kannywood, Rahama Sadau, Zaharaddeen Sani
Rahotanni sun bayyana cewa, Rahama Sadau ta sa an saki Zaharaddeen Sani daga wajan 'yansanda bayan da Hadiza Gabon tun a farko tasa aka kamashi. Yanzu haka dai rahotanni sun ce Zaharaddeen Sani na gida. Tun farko dai Hadiza Gabon ce tace matan da basu shiga fin ba kada su shiga, inda Zaharaddeen ya mata martani me zafi. Da alama, Hadiza Bata ji dadin martanin Abokin sana'arta ba inda tasa aka kamashi.
DA ƊUMI-ƊUMI: Jarùmar Kannywood Hadiza Gabon Tasa An Kama Jarumi Zahraddeen Sani

DA ƊUMI-ƊUMI: Jarùmar Kannywood Hadiza Gabon Tasa An Kama Jarumi Zahraddeen Sani

Hadiza Gabon, Kannywood, Zaharaddeen Sani
DA ƊUMI-ƊUMI: Jarùmar Kannywood Hadiza Gabon Tasa An Kama Jarumi Zahraddeen Sani. Hadiza Aliyu Gabon ta sa an kama jarumi Zaharaddeen sani a jihar Kaduna, rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka suna can Police Station a na kan tattaunawa. Kamun dai ya biyo bayan kalaman da yayi a wani martani ga Hadiza Gabon inda ya ce, daga kan su Hadiza aka fara zagin ƴan masana’antar kannywood saboda shigar da sukeyi da mu’amalarsu da wasu dake wajen masana’antar ta kannywood. Me zaku ce?

Alamomin ciwon zuciya ga mata

Ciwon Zuciya
Ciwon zuciya na daya daga cikin abubuwan dake kashe mata da maza. Alamomin ciwon zuciya kusa dayane ga duka mata da maza. Ga alamomin ciwon zuciya ga mata kamar haka: Ciwon wuya, haba, kafada, baya, da saman ciki. Sarkewar Numfashi. Jin ciwo a daya ko duka hannuwa. Yawan ciwo da safe da amai. Zufa. Jin kanki ba nauyi da Juwa. Jin Kasala sosai. Zafin Zuciya. Abubuwan da ka iya sa ciwon zuciya ya tsananta a jiki mata: Ciwon Suga: Duk macen dake fama da ciwon sugar na cikin hadarin iya kamuwa da ciwon zuciya. Damuwa da Kunci: Matsalar damuwa da kunci ta fi baiwa mata alamun kamuwa da cizon zuciya fiye da maza. Shan Taba ko Wiwi:Mace me shan taba ko wiwi tafi maza zama cikin hadarin kamuwa da ciwon zuciya fiye da maza. Rashin Motsa jiki: Yawan zam...

Maganin bugawar zuciya da sauri

Ciwon Zuciya, Duk Labarai
Bugawar zuciya da sauri na iya faruwa a kowane lokaci kuma abune wanda ke zuwa ya wuce, akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan Maganin bugawar zuciya da sauri. Ga abubuwan dake kawo bugawar zuciya da sauri kamar haka: Motsa jiki. Kishirwa me tsanani. Rashin Lafiya. Shiga halin takura. Me ciki na iya fuskantar hakan. Shaye-shayen miyagun kwayoyi. Shan taba Wasu daga cikin maganin bugawar zuciya da sauri sune: Tashin Hankali:Tayar da hankali na sa bugawar zuciya da sauri, dan haka neman maganin kwanciyar hankali da samun nustuwa zai taimaka magance wannan matsalar. Hanya ta gaba wajan magance matsalar bugawar zuciya da sauri itace a kwanta a kan gadon baya ko kuma ace rigingine sai a rika yin kamar ana tari, a dan rike numfashi sai a sakeshi. Ana k...