Friday, July 17
Shadow

Wata Sabuwa: Za’a kara kudin kiran waya da na aika sakon waya a Najeriya>>NCC

Hukumar kula da harkar Sadarwa ta kasa, NCC ta bayyana fara duba farashin kiran waya dana aikawa da sako a Najeriya.

Hakan zai sa a kara kudin kiran dana sako kamar yanda Rahotanni suka nunar.

Wani me ruwa da tsaki a harkar sadarwar, Wole Adenekan ya tabbatar da hakan inda yace karin ya zama dole saboda an samu sauye-sauyen tattalin arziki da na kimiyya da fasaha.

Yace maimakon a rika biyan kudi kadan amma ba’a samun sabis me kyau, gara a rika biyan ainahin kudin kiran dana aika sako sabis din ya inganta.

Hakan na zuwane a yayin da ‘yan Najeriya da dama ke kokawa da matsalar tsaro.

Karanta Wannan  Na yiwa Atiku Makarkashiya a zaben shekarar 2023 duk na ni dan PDP ne hakanan idan ya sake tsayawa takara a shekarar 2027 zan sake yi masa makarkashiya>>Inji Ayodele Fayose

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *